Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 31
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAR MAKAFI*
Page 98
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
https://chat.whatsapp.com/F93CYFGSIWA3ewhl8cCAYW
Barkanku da zuwa zauren A.A GARKUWA FOUNDATION inayi mana fatan alkhairi, fatan wannan haɗakar tamu na taimako zata kaimu ga Jannatul Firdausi, *Ga Ramadan ya ƙarato mai akwai da mai niya, taimakon sadaka ga ma buƙata ciyarwa ko shayarwa in Allah ya hore mana kamar yadda muka yi last year ga account da zamu fara tara kuɗin ga mai niya 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa*
jama'ata kune Æ™arfina, domin su jama'a Rahama ne, ba haushe yace hannu É—aya baya É—aga jinka, yan uwa ita sadaka bata yawa kuma bata kaÉ—an ko Naira 500, 1k 2k 3k 4k 5k har zuwa 10k 20k 50k 100k kai har 1million zuwa sama in Allah ya baka iko, kai koda Naira É—arice kike bayar zamuyi farin ciki da ita, kuma ajiyace maidaraja, wacce Allah ne zai bamu sakamakonta kada ki/ka raina abinda ke hannunki domin manzon Allah S.A.W yace muyi sadaka koda da tsagin dabino ne! kada kuma muyi tunanin sadaka zata raunata dukiyar mu ko ta hanamu ci gaba, kada kuma muga sadalar tayi yawa in kina da hali ko 1M kika bayar akwai ma buÆ™atan da in za'a raba musu zasu iya neman Æ™ari ma. Kuma Manzon Allah yace, ita sadaka tana kashe masifa kamar yadda ruwa ke kashe wuta, Allah Ubangijin talikai shi zai yi mana sakayyar al'khairi da zamu wanzar duk Æ™anÆ™antarshi, Allah ya bamu ikon haquri da zama da juna, Allah ya bamu ikon taimako, ya kuma sa mana a mizanin kyawawan ayyukanmu ya taimakemu fiye da yadda zamu ke taimakawa jama'a. mu haÉ—a hannu da hannu mu ciyar da mabuÆ™ata a Ramadan. Afwan In nayi miki/maka wani kuskure cikin rashin sani da ajizanci na d'an adam a gafarceniðŸ¤ðŸ™ðŸ»
A taimaka domin Allah
"To shike nan Mahmoud sai kuma ka haÆ™ura da Fariyda in dai bazaka amince da umarnin mahaifin kaba nasan shima bazai yarda da nakabaâ€. Hannunsa duka biyu yasa ya riÆ™e kansa tare da rumtse idanunsa yayi shiru tamkar wanda ruwa ya cinye ya nitsa cikin juya tunaninsa, ido Malam ya zuba masa ganin yadda jikinsa ke tsuma.
Kusan 7 minute suna a haka can ya É—ago kanshi cikin sanyi yace.
"Malam na yarda in dai za'a barni da Farriyyhana na amince Abba ya aura min duk wacce yaga damaâ€. Numfashi mai nauyi Baba Malam É—in ya sake haÉ—e da dafa kansa a hankali yace.
"Allah yayi maka al'barka kaje ka samu mahaifin naka ka bashi haÆ™uri in ya kawo maka mgnar Jidda kace ka yarda nasan zai barka kazo ka É—auki matarka, tashi kaje kaga har goma ta wuce dare ya fara nisa Allah yayi maka al'barkaâ€.
Cikin sanyi ya miÆ™e haÉ—i cewa. "Amin Ya Allahâ€. Daga nan ya wuce gida zuciyarsa cike da saÆ™e-saÆ™e.
Ita kuwa Fariydan a cikin gida kamar yadda ya zata ɗin fir taƙi shan maganin haka yasa Mamy fusata ta juya tana faɗin.
"Saddiqa barta kada Allah yasa tasha maganin ai jiki magayi, in danne Æ´aÆ´anta in basu magani itama in tsaya danneta takeso ko me take nufiâ€.
Ta ƙare maganar tana kallon Aunty Amarya data shigo parlour tana ce mata.
“Malam yace kizoâ€. Tana gyara goyon Zaid tace.
"Lfy dai kam ko?â€. Ta Æ™are maganar tana kallon time a wayarta.
"Lfy lau sai yanzu mafa ya dawo masallacinâ€.
Bayanta tabi suka tafi parlour.
Sit sukayi shiru suna jin bayanin da yake musu na yadda yayi da Mahmoud Saida yayi shiru Aunty Amarya tayi ƙasa da kai cikin takaici tace.
"Gskya malam baka kyautawa Fariyda ba ta ya zaka zama mai tirsasawa mijinta da yi mata kishiya, ai wannan ba so bane, tana zamanta da mijinta da Æ´an yaranta ta jumre duk wani murÉ—eÉ—É—en halinsa da zafinsa da miskilancinsa saida zamansu ya fara daÉ—i minjinta na masifar sonta ku wani Æ™aÆ™abo mata kishi ai wannan cutarwane in shi baban Mahmoud baiji zafin za'ayi mata kishiya ba ai kai ya kamata kaji zafin za'ayiwa yarka kishiyaâ€.
Dariya Mamy tayi haÉ—i da kallon Malam daya zuba wa Aunty Amarya ido.
"To me acikin Maman Raihana mu yanzu ba mu biyu bane, meya damemu me muka rasa na jin daÉ—in duniyaâ€. Da sauri tace.
"A'a mu da banfa su yaran yanzu da ban kai inama zaki haÉ—asu damu dan Allah abar Fariyda tayi farin ciki a rayuwarta anzo an rabata da minjinta wlh wannan ciwon da take tayi fa maÆ™on mijinta ne da soâ€. Murmushi Baba Malam yayi yace.
"MaÆ™o shayar da ita yake bare ace maÆ™o takeyi kamar wata yar yayeâ€. Cikin suÉ“utar baki tace.
"Ato yo shayar da ita yake mana mijin ta nefa shayarwa da tafi ta uwa daÉ—i ma kuwa a Dan Allah ku bar yarin taji daÉ—in mijintaâ€.
Ida Mamy ta rufe haÉ—i da cewa.
"Ya Salam wannan magana hakaâ€. Shima Malam murmushi kawai yayi ya É—aura da cewa.
"Aure dai sunnace kuma Mahmoud ma É—ane a gareni hakama Jidda dan ya aureta ba abinda zai ragu a son da Mahmoud yakewa Fariyda dan tabbas na gamsu yana sonta so mai Æ™arfiâ€.
Mamy tace.
“Itama É—in É—aya tana sonshi duk wannan ciwon nurkufurcine yake cinta ba komai ba, kadai ga abinda sukayi mana ai ranar yau kuma ya biyo ka masallaci gaba bamu san ina Mahmoud zai tsarekaba nifa tsoro nake ma kada rabo ya murÉ—emuâ€. Murmushi Malam yayi kana sukaci gaba da tattaunawa Aunty Amarya dai sai mita take har ranata abin ya mata ciwo harda hawayenta.
Shi kuwa Mahmoud koda ya isa gida ya samu tuni su Abba sun shiga.
Yana shiga kan gadonsa ya faÉ—a ko hula da takalminsa bai cireba, kiranta yayi bugu É—aya ana biyu ta amsa.
Saddaqa tayi saurin amsar wayar kafin tace wani abu taji yana faÉ—in.
“My Angel zamugudu mu bar Æ™asar nan, mu barwa Abba da Malam su Zaid su zame musu madadinmu ki amince min mugudu dan Allah. In ba hakaba bazasu barmu inji daÉ—in rayuwa da kebaâ€. Da sauri tace.
"Salamu alaikum Mahmoud Fariyda bata da lfy kuma taÆ™i shan maganiâ€. Cikin cushewar tunani yace.
"Our Aunty ina son matata su bani abata inyi jinyarta da kaina dama nasan bazata shaba in bani na bataba, Our Aunty bana son Æ™ara aure bana son yiwa My Angel kishiya Malam da Abba sun matsa wai sai na auri waccar mayyar yarinyar kafin zasu bani matata Please ki ce mata ta yarda mugudu mu tafi nesa dasu ba wanda zai san inda zamuje sai keâ€. Cikin jin zafin da taya yar uwarta tace. "In sha Mahmoud hakama bazai faruba Fariyda kaÉ—ai ta isheka rayuwar duniya gata kace mata tasha maganiâ€.
Ta ƙare maganar tana mannawa Fariydan wayar a kunne daga nan ta wuce bathroom alwala tayi ta fito.
Har yanzu suna waya sai kai kawai Fariyda ke gyaÉ—awa hawaye na bin fuskarta.
Darduma ta shimfiɗa ta fara yin nafilfili a cikin dukkan sujjadar ta sai ta roƙi Allah da yasa a ƙaddarar rayuwar Fariyda ba kishiya haka nan tausayi Fariyda yasata zubda wahaye ita dai tunda tayi aure bata cika farin cikiba koda Yah Amin ke raye kullum baƙin cikin Mahmud bayan shi ga rashin Yah Amin da mutuwa ta yanke mata ƙaunar masoyi akazo batun karbar yara tayi takaba cikin kuka da fargabar rasa yaranta, bata wanye da wannan ba ba zato ba tsammani aka aura mata Mahmood mutumin da duk duniya tasan basa son juna, ta rayu dashi da azaba da ƙuncin zuciya, targaɗe da bakar magana da ko in kula tasha ba adadi yanzu da yazo ya fara sonta suka fara jin daɗin juna anzo an nesantasu, yanzu kuma ace sharaɗin barinta ta tare dashi sai an ƙaƙaba mata kishiya wannan tunanin da ganin hawayen Fariyda yasata kuka.
Ita kuwa Fariydan a hankali ta É—auki maganin yana kallon ta ta video call daya kirata a hankali tace.
"Zan sha maganin Appiy ka gani yanzu zan sha ba sai ka zoba dare yayi ina tsoron wani abu ya samekaâ€. Kai ya gyaÉ—a mata haÉ—i da cewa.
"To in dai bakya son wani abu ya sameni kisha mganinki, kuma ki yarda zamu guduâ€. Kai ta gyaÉ—a mishi haÉ—i dasa maganin a bakinta da sauri ta riÆ™e wuyanta.
Aunty Saddiqa data iso wurin ya kalla haɗi da yin mgna da sauri ganin Fariyda ta fara yunƙuri.
"Our Aunty kisa mata ruwa kisa hannunki ki rufe mata bakin a hankali kar taji ciwoâ€.
Da sauri Aunty Saddiqa tayi yadda taga yayi mata ranar da yazo.
Amman ina sai kakari dan maganin ya tsaya a maƙoshinta dan shima ɗin ranar Saida ya tattauna ya bata.
Gaba ɗaya jikinta tsuma yake tana kakari da yunƙuri idonta sunyi jazir.
ÆŠan dukan bayanta Aunty Saddiqa tayi kamar yadda taji Mahmoud É—in na gaya mata.
Kusan a tare suka rinƙa sauƙe ajiyar zuciya ganin ta samu ta haɗiye maganin da kyar.
“So sorry my Happiness in sha Allah zamu gudu mu bar musu Æ™asarma sannuâ€. Kai take gyaÉ—a mishi ido cike da Æ™olla murya sanyaye tace.
“Kaga na sha ko, ai na girma ko?â€. Murmushi mai cike da jin daÉ—i ya subce masa girarsa ya É—aga mata haÉ—i da cewa.
"Yesss My princess yau na Æ™ara yarda Babe na ta girma, sai ranar da kika cika alqawari da kikayiwa Papi in mun haÉ—u zan gama yarda My Angel ta gama girmaâ€.
Idonta ta lumshe haÉ—i da cewa. "Okayâ€. Komawa gefe Saddiqa tayi.
Kusan kwana waya sukayi ranar.
Washe gari bayan sun dawo sallan asuba kamar kullum duk suna zaune Parlour Abba tea suke sha suna É—an hira bayan duk sun gaggaisa Ummi tace.
“Ni kam Abban Aminullah kun kai sadakin Sulaiman kuwa, gashi mu har za'a kai kayan yau.â€
Yana kallon Mahmood da yasa tea spoon a cikin mug É—in tea É—in yana ta jujjuyawa ba tare da ya kurÉ“a ko sauÉ—aya ba, sai kuma ya maida kanshi kan Sulaiman da yake ta smiling cike da farin Salim ne ya É—an dunÆ™ureshi a hankali yace. “Kai kada dai ka yage bakinka da murmushi kaya akace za'a kai ba itace za'a kawo maka yau baâ€.
Gyaran Muryar da Abba yayi ne yasa duk suka meda hankalinsu kanshi.
"In sha Allah yau muma zamu kai Sadakin Sulaiman É—in da kuma na Mahmoud É—inâ€.
Ido Ummi ta maida kan Mahmoud da ko motsi baiyiba bare yace wani abu, sai caccaka tea spoon da ya farayi cikin mug É—in wanda ba dan mai Æ™arko bane da ya dare. Goggo Dada shi take kallo Salim kuwa fuska ya kwaÉ“e a hankali yace. "Hmmmmâ€. Shi kuwa Abba ido ya É—an zuba musu kana yace.
"A lissafin dai yau saura kwana 18 bikin a yadda muka ajiye date É—in mu mun gama namu shirin kuma kuyi kokarin haÉ—a komaiâ€. Salim ne yace.
"Abba muma ai a shirye muke duk da daima satin nan ma muna da bikin Dr Fadil da Fadilansa ranar Saturday ne É—aurin aure in sha Allahâ€. Ummi tace.
"Haka dai ni bamuyi mgnar ba ai shekaran jiya yazo da kansa ya kawowa Abba IV kusan anan ma ya wuni da Mahmoudâ€. Abba yace.
"To Allah ya sanya al'khairi yace ai anan Kano za'a zo ayi bikin dukaâ€. Amin sukace.
MiÆ™ewa Abba yayi ganin lokacin yin walaharsa yayi bedroom nasa ya nufa. Da sauri Salim yace matso kusa da Mahmood a hankali yace. "Kada ka damu ina neman mafita faâ€. Yana kallon Ummi da Goggo da suka miÆ™e suka fita yace. "No barshi kawai ni bana son taimakon kowa, nima inada Æ™waÆ™walwar tunanin aiâ€. Ya Æ™are maganar da barin Parlour Yana hararan Sulaiman gami da cewa.
"Ganshi kamar wani sakarai daga jin za'a kai sadaki ya susuceâ€.
Dariya Salim yayi ya bishi da ido, sai kuma ya kalli Sulaiman daya rakashi da harara yana faÉ—in.
"Gwara ni kai da kake kuka da rarrafe fa kamar É—an yaro â€. Shi kuwa Mahmoud
Yana shiga bathroom ya wuce wanka yayi ya shirya cikin datatstsun suit masu zafin gaske mulk collar mai sheƙi da ƙyalli, sai ƙamshi yake bazawa, a haka ya sauƙo ƙasa parlour Abba ya shiga yana ɗan kaɗa car key ɗinsa.
Shiru parlour sai kamshi yake alamun a gyara ko ina, bedroom ya nufa bakimshi É—auke da sallama, a hankali ya shiga bayan Abba dake zaune kan darduma ya amsa mashi.
Gaban Abba ya zauna kan guiwowinsa yana mai gyara net É—in wuyansa.
Shi kuwa Abba fuska a tsuke yake kallonsa cike da mmakin shigo masa har bedroom.
"Ka tasani gaba kayi shiru TV na zama ko madubiâ€. Abba ya faÉ—a a daÆ™ile, kai ya É—an jujjuyawa cikin Æ™anÆ™an da kai da salon neman alfarma da rauni yace.
"Dan Allah Abba kayi haÆ™uri ka gafarta min ka yafe min kayi min rai ka jiÆ™ainaâ€. Shiru Abba yayi yana kallonsa a gyatsine, idon na tsatstsafo hawaye masu zafi yace.
"Abbana kayi haÆ™uri ka taimaka min in É—auko matata, nasan ni mai laifine nayi kura kurai da yawa marasa daÉ—i, amman na tuba kuma nasan Allah zai yafe min dan nayi taubatunnasuha bazan Æ™ara cin zarafin igiyar auren da matataba, Abba Allah yana son masu yafiya ga wanda ya tuba dan Allah ka yafe min ka bani matata Baba Malam yace shi ya amince in ka amince min inje in É—auÆ™i matata kayi haÆ™uri ka yafe min ka amin cemin inje in É—aukota?â€. Ya Æ™are magiyar murya na rawan kuka hawaye na kwaranyo masa, a taÆ™aice Abba yace.
“Ban amince baâ€. Da sauri ya Æ™ara matsowa gaban Abba da rarrafe hannunsa ya É—aura kan guiwowinsa ido na zubda Æ™wallan murya cike da gskyar zuciyarsa yace. "Abba kayi haÆ™uri ka rufa min asiri kar in faÉ—a tarkon zina wlh ina gazawa, haÆ™urina yazo maÆ™ura inaji tamkar zan mutu saboda begen matata Please dan girman zatin Allah Abba ka barni in kusan c halal É—ina kar matsi da bukata ya kaini ga kusantar haramâ€. A faÉ—ace Abba yace. "Dama ka saba ai wani baÆ™on abune yin zinar a wurinkaâ€. Da sauri ya fara jujjuya kai murya na rawa yace. "A'a fa Abba ba haka nake nufiba wlh har abadan bazan kuma kusantar zinaba, kawai dai yanzu inajin tamkar in fara yin istimna'i samun sauÆ™i kuma ka sani ba kyau Allah ya hana kuma yana haddasa cuta ga zunubi ina tsoro kar in kuma shiga wannan masifarâ€.
A kufule Abba yace.
"Tashi ka bar min É—aki da waÉ—annan kafuran kalaman naka, in mata kakeso ai ga Jidda na kusa zan aurama ita in yaso sai anyi auren sai ka É—auko Fariyda in fa har ka amince anyi aurenka da Jidda cikin daÉ—in rai kenan, in ta tare da mako É—aya sai ka É—auko Fariyda bazan hanaka itabaâ€. Da sauri yace. “Abba na yarda amman dan Allah a bani da ma in É—auko Fariyda kafin lokaci bikin wlh bazan iya kai wannan lokaci ba mataba, kayi haÆ™uri ka yardar min in É—aukota ko kuma a bani dama in rinÆ™a zuwa inda takeâ€.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.