Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 21 of 31
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 108
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Nigeria
Tunda Hantsi Samira ya shiga kitchen ta fara ferf-fere da yan yanke yanke, sha biyu dai-dai ta fito tayi wanka ta tafi school dan tana da lectures ƙarfe ɗaya zuwa biyu, uku zuwa huɗu tare suka tafi da Hafiz shi nashi sai biyu ya tafi da wurine dan ita. Ana yin sallan azahar Humaira da Salma da tun da hatsi ta shigo tana wurin Humaira suka kira Fariyda suka sha hira da neman karin bayanin yada tsarin ayyukan gidan yake.
Suna shiga kitchen suka wuce suka fara aiki da taimakon su Ummi da Goggo Dada na taimaka musu da gyaran fruits da dai yan ayyukan zaune.
Maman Samira kuma da Kande da Biba suna ƙofar Maman sunayin aikin abincin masallaci kama daga kunu, tea, masa, ko ƙosai, ko soyayyan doya da kwai, jolof na shinkafa ko Pasta, Ummi kuma da Goggo Dada suke haɗa ruwan surki mai daɗin gaske wanda wasu har gida suke tutowa a karba musu dan yaran yanzu ba kowa yasan menene surkin bama bare yadda ake yinsa.
Haka abin yake a dukkan gidajen musulmai baki É—aya kowa da iyakar karfinsa.
Gidan Baba Malam tuni Mamy da Aunty Amarya da masu aikinsu biyu duk suna kitchen su masu aiki suna aikin abincin da za'a fidda masallaci su Mamy kuma na gida.
Jidda ne zaune riÆ™e da mug cike da tea cikin sauÆ™e numfashi Mama tace. "Ki sha mana Jiddaâ€. Ido cike da kokonto da tsoro tace.
"Mama anya kuwa wannan malamin ba kafuri bane, kai bama malami ba ince boka kawai Mama ta yaya zaice kar inyi azumi in har ina son cikar burina azumi fa ma? Shinefa ibadar da Allah ya keÉ“e yace muyi duk shekara cikin watan da aka sauÆ™e Alqur'ani mai girma yace kar inyi azumi dan kawai son Yah Mahmoud zan rabu da imanina in bar addinina a karon banza kai gskya bazan iyaba, shiyasama ni dama can na kwana da niyar yin azuminaâ€. Kasake Mama tayi cikin karaya da dukan da gskya takeyiwa Æ™irjin É—an adam duk yadda ya kai ga Æ™inta cikin sanyi tace bari in kirashi gskya a canza wani salon batun hana salla da azumi kam ba namu baneâ€.
Ta ƙare maganar tana ɗaukar wayar ta dake gefenta haɗi da kallon Jidda dake faɗin.
"Gskya dai a sauya salon aikiâ€. Yana amsa kiran ta fara da gaisuwa cikin ladabi da yin Æ™asa da kai cike da tsoronsa tace.
"Malam Jidda fa ta kasa batun ajiye azumin nan, tace bazata iya barin salla da barin azumiba ita kam, in akwai wata hanya da bata shafi ibada a gaya mataâ€. Shirun da yayi ne yasa Mama fara bashi haÆ™uri kamar ubanta.
Cikin daka tsawa yace.
"Akwai wata hanyar amman ta tabbatar dole dolen sai an bita in tana son biyan buÆ™atar ta.â€
Da sauri Jidda dake jinsa tace.
"In dai ba na hanani ibada bana na yarda zanyishiâ€. Cikin tsawa-tsawa yace.
"Sai na tashi zan kiraku muyi mgnarâ€.
Daga nan ya katse kiran.
Istanbul ana idar da sallan la'asar ya nufi gida hannunsa riƙe da jarbi, garin yayi lup-lup ko alamun rana babu shiyasa da kafa yake tattakin zuwa gida kasan cewar masallacin na Suleymaniye mosque ɗin na kusa dasu.
Shiru parlour ba jin alamun motsinta a kitchen yasashi shiga.
Gefenta ya tsaya yace.
"Farriyyhah me zakiyiâ€. Tana É—an murmurshi tace. "Appiy ai duk abinda kakeso shi zan yiâ€. Yana É—an jan roban data É—ebo Arish yace.
"To bari ban saki aikin komai baâ€. Tana juyowa tace. "Saboda me in ban maka abin buÉ—a bakiba wa zanyiwaâ€. Cikin jinÆ™ai yace. "To na yafe kiji da rainon Lil Amin ma ya isa aiki, azumin ma fa Allah ya baki dama in kinji bazaki iyaba ki bari sai kin haihuâ€. Da sauri tace. "Appiy na iya azumi a Nigeria ma bare nan da babu rana ba zafi ba Æ™ishi bare yunwa kuma Alhamdulillah lfyata Æ™alau bana jin komai ai in banyi azumiba ya zama ganganci da sakaciâ€. Cikin gamsuwa da jin daÉ—in Æ™arfin guiwarta yace. "Ai shi yasa na barki kiyi azumin da ba hujjar hanaki yi, amman aiki dai ki bariâ€. Cikin mmki tace. "To me amafanin kayan abincin da aka libga a gidanâ€. Numfashi ya É—an fesar yana gyara riÆ™on carÉ“insa yace. "Saboda É—an abincin sahur ko in an sha ruwa wuraren goma zuwa sha biyu in kinji kina son wani abu ko zaki min wani abu nan ba matsala sai ki shiga kina aiki kina ci, na buÉ—a baki kuwa a ga Divella kusa damu kullum acan nake buÉ—a baki wasu lokutanma acan nake sahur ma gashi nan kusa damuâ€. Ya Æ™are maganar yana jawo hannunta ganin kallon mmki da take masa tana biye dashi a baya tace.
"Appiy bazan iyaba ina kusa da kai Restaurant ya zama wurin cin abincinka to ni me anfanina kenanâ€. Suna zama a parlour yace.
"Abinda yasa nake son shan ruwa acan ina É—an sayawa wasu ne dan in samu ladan ciyarwa. Amfani kuwa ai kece mai amfaniâ€. Haka dai dole ya hanata.
Gab da magrib ta fito cikin shigar abaya mai faɗin gaske tayi kyau gwanin kyau sai ƙamshi take shima jallabiya ce a jikinsa. Arda suka samu cikin mota, suna shiga yaja motar a bakin Divella Bistro Restaurant.
A tare suka fita, Arda ne ya zagaya baya ya É—auko wanni babban Basket guda biyu masu girma wanda ke cike da dabino É—an gaske Ajwa mai kyau, wurin babbane irin sosai É—in nan dan Restaurant ne na alfarma tables É—in akwai mai kujeru bibbiyu akwai mai uku uku akwai mai bibbiyu. Kan mai biyu suka zauna, ido ta zuba wa Arda ganin yana bin ko wanne table yana ajiye É—an kwalin dabinon in mai kujeru biyune ya ajiye biyu in mai ukune ya ajiye uku in mai huÉ—une ya ajiye huÉ—u a haka har ya iso inda suke kamar na kowa suma ya jiye musu haka yasa ba wanda yake fahimtar Mahmoud ke rabawa sadakar sai wanda yaga fitansu mota tare da kuma iya Werters É—insu.
Da sauri ya koma motar roll din gorunan ruwa ya kawo ya fara rabawa ɗaya bayan ɗaya, sai kuma robobin Yogurt yana gama rabawa masallacin dake wurin na kiran sallan magrib, kusa duk a tare mutane suka fara cin dabino kasan cewar ƙasace mai cikar musulmai.
Bayan duk sun sha ruwane sai kuma É—aya daga cikin ma'ai katan ya fito yana faÉ—in. "Komai da suke dashi nan free ne akwai wanda ya zai biya duk adadin abinda kowa yaci, aje ayi salla sai azo aci abinci.
Mafi akasarin mutane sun san da hakan shiyasa duk suka miƙe sai ƙalilin waɗanda sai sunci suke iya sala.
Gefen inda mata suke salla ya nuna mata kana suka zo suka shiga gefen maza. Bayan an idar da salla duk kowa ya dawo mazauninsa sukaci suka sha, wasu harda tafiya dashi. Kiran isha da akeyi ne yasa ma'akacin kawo masa jadawalin kuÉ—in da zai biya na wannan ranar. Kai ya É—an juyo yna kallon Fariyda wayarsa ya zaro yayi musu transfer kana suka wuce masallacin. Anan sukayi sallan isha da asham. Daga nan suka dawo gida.
A hankali ya É—an gyara kwanciyarta a jikinsa cikin raÉ—a yace.
"Wa da wa kika cewa kina da cikiâ€. Cikin kunya ta lumshe idonta haÉ—e da cewa. "Ba wanda na gayawa sai kai kuma ba wanda zan iya gayawa in ba kaibaâ€. Yana shafa bayanta yace. "Har yanzu ba wanda yasan Lil Amin na hanya sai mu kaÉ—aiâ€. Kai ta gyaÉ—a mishi alama eh, É—an kwantar da ita yayi ya sunkuyo kanta haÉ—e da tattare rigarta É—an cikin ya foto fili sumbatar cikin yayi haÉ—e da cewa. "Nima ba wanda zan gayawa in sun gani kawai zasufi farin cikiâ€. Ya Æ™are maganar yana shafa cikin. Washe gari da rana Video call yakeyi dasu Zaid da wayar Ummi. Zaid yasa hannunsa ya kamo gashin Zaitoon yana ja alamun ta matsa mishi. "No Zaid ka sake mata gashi ba kyau cin zakiâ€. Murmurshi yayi haÉ—e da tafa hannu kana ya buÉ—esu yace.
"Appiy anjoâ€. Zaitoon Fariyda dake zaune gefensa take ta kira. "Ammey owo Ammeyâ€. Yana musu kallon dake nuna tsamtsar so da kaunarsa a kansu yace. "Ok Sweetheart ni baza ki min oyoyo bakoâ€. Kamar ta gane me yace tace.
"Owo Appeyâ€. sai kuma kuma ta kai bakinta kan screen É—in wayar ta manna Æ´an lips É—inta tayi kissing nashi. Dariya Ummi tayi tace. "To kaima tayi maka harda kiss ma, ai sunfi kiranka mafa motsi ba motsiba zasu fara owo Appiyn sun medashi kamar waÆ™a, Huzaifa ma Owo Appiyn yake kiransu.
Fariyda da ne tace. Ai ina gaya mishi Ummi nasan sunfi sonshiâ€. Murmushi Ummi tayi tace. "Kada ki damu Fariyda na kema suna sonkiâ€. Daga nan yayi ta wasa dasu har Saida aka kira la'asar ya barsu ya tafi masallaci. Yauma kamar jiya gab da magrib suka tafi, cike da mmki tace. "Appiy naga mutanen yau sunfi na jiya yawaâ€. A hankali yace. "Eh haka za'ayi ta Æ™aruwa ai suma akwai mabuÆ™a kamar dai Æ™asarmuâ€. Bayan kwana biyu wuraren Æ™arfe sha É—aya ta dafa musu indomie mai É—an ruwa-ruwa yaji dukkan abin buÆ™ata, sunaci haÉ—e da tea É—an guntun rigar baccin dake jikinta yasa duk cinyoyinta na fili hannusnhi ya É—aura kan cinyarta yana faÉ—in. "Babe kwana biyu kina samun hutun tunda azumi yazoâ€. Ido ta É—an É—ago ta kalleshi sai kuma tayi Æ™asa da kai fahimtar yana buÆ™atar ta kusa dashi ne yasa tace.
"Akwai abinda kake buÆ™ataneâ€. Da sauri ya gyaÉ—a mata kai kamar Æ™aramin yaro ya nuna mata Æ™irjintaâ€. Shigowar kiran Ummi ne yashi É—agawa da sauri yayi sallama ya É—aura da cewa. "Ummi lfy ko yasu Zaid ina Abba na da Goggo Dada dasu Salim da iyalansuâ€. Fahimtar ganin kiranta a lokacin ya É—an sashi fargabane yasa tace. "A'a ba komai fa lfy lau kowa, batun Abbanku ne na tuna shiyasa nace bari in kirakaâ€. Numfashi ya sauÆ™e yace. "Fatan dai yana lfyâ€. Da sauri tace. "Eh nace ma kowa lfy, ina sone in gaya maka ka gwada kiranshi mana ko yi masa saÆ™on Barka da shan ruwa, bana jin daÉ—i abinda ke faruwa tsakaninku faâ€. Murya a sauÆ™aÆ™e yace. "Ummi ai tunda muka tafi kullum sai nayi mishi message da safe, ranar juma'a kuwa kullum sai na kira baya É—agawane, kuma ina sa mai kati data duk jumma'a, yanzu kuma da azumi ya shigo kullum ina mishi Barka da shan ruwa da safe kuma ina gaidashiâ€. Ajiyan zuciya mai nauyi tace. "Alhamdulillah kaci gaba da hakan in sha Allah wata rana zai amsaâ€. Yana É—an jawo Fariyda jikinsa yace. "In sha Allah Ummi bazan bari baâ€. Daga nan sukayi Saida safe.
Washe gari bayan an idar da sallan isha kamar kullum Abba ya shigo tare dasu Salim Sulaiman Hafiz Huzaifa Bala Kabiru da Baban Samira duk a parlour suka zauna Hafiz da Huzaifa ne ke zubawa kowa abinda yake so haka yauma suke zaune.
A parlour Ummi kuwa Salma da Humiara da Samira suna Dinnin table su Ummi kuwa da Goggo Dada da Maman Samira suna tsakiyar parlour.
Bayan duk sun gama ci da shane, Huzaifa ya fito da duk plate, mugs, spoons and wermers na parlour Abba duka.
Habiba da ta wanke komai ta tattare kitchen kana ta tafi.
Mamy na zaune gefen Baba Malam dake waya da Mahmoud da Fariyda bayan sun gama wayar Aunty Amarya ne tace. "Wannan aure da an dage sai an rabasufa lamarin zai zama tashin hankali Babba itama Fariyda tana son mijintaâ€. Mamy tace. "Bar ja'irai ai yanzu da suka ga za'a rabasu duk sun natsu sun riÆ™e junaâ€
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daÉ—e ba'a jeba, yau har anyi goman farko cib an gamashi gobe za'a tashi da goma ma na biyu.
Bayan sallar la'asar tun daga harabar gidan yake jiyo kamshi mai daɗin shaƙa.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.