Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 31
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 91
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
Bayan kwana biyu.
Shiru tayi tana mai ƙara rungume su Zaid a jikinta, rashin wayarta yasa take jinta kamar kurma.
Shigowar Saddiqa ne yasa ta buÉ—e idonta, gefenta ta zauna haÉ—e da cewa. "Fariyda meke damunki ne wai dukfa kin zama sai a hankaliâ€.
Numfashi ta É—an fesar a hankali tace.
"Dan Allah ki roÆ™a min Mamy ta bani wayata, wlh rashin wayar ba daÉ—i sai in jini cikin kewa kamar akwai wani babban abun da na rasa a kusa dani duk sai nakejin duniyar ba daÉ—i kamar banda lfyâ€.
Kai ta É—an jinnina haÉ—e da cewa.
"Ai dama haka ne in ba waya a hannunka, zan gwada mgna muji me zatace, yau kusan kwana gomafa kenan ai yaci a baki wayarki duk dai ke ba iya rashin wayar bane da alamu dai kewar Appiy ne. Fuska ta kwaɓe tare da jingina bayanta tana taɓe baki.
Amira ne ta shigo da plate a hannunta cike da awaran couscous yaji ƙwai a tsakiyarsu ta ajiye musu plate ɗin tana faɗin.
"Gashi na gamaâ€. Hannu Saddiga tasa ta dauko É—aya tare da sa yaji ta kai baki itama Amiran ta zauna a gefe suka fara ci. "Fariyda muci manaâ€. Kai ta girgiza tana gyara rufe jikinta dan sanyin da takeji a hankali tace.
"Aunty Saddiqa wai kun kusa komawa inji Sadiqâ€. Tana É—aukar wani Awaran tace.
"Da karshen watannan zan koma to kuma ma yanzu naji batun auren Humaira da Sulaiman ya kankama jiya ma su Abba sun zo an tsaida rana 27 zan jira bikin dama on 31 Abban Amnah zai dawo ana gama biki zan wuce Yolaâ€. Shiru tayi haÉ—e da jingina kanta jikin gadon.
Mama ce zaune ita da Jidda suna sauraron Bappa Lawan dake faÉ—in.
"Jidda ki shirya gobe kuje gidan Abbanku zakuje ay muku gwajin genotype, yanzu kam an tsaida sahihiyar rana in sha Allah ba É—agawaâ€. Cikin tsananin jin dadi tace.
"To Babaâ€. Mama kuwa zama ta gyara tare da cewa. "Sun bada sadaki ne?â€. Tayi mgnar zuciyarta cike da burin a basu sadaki dan boka ya tabbatar musu kuÉ—in sadakin shi za'a bawa akwai aikin da zai musu dashi daga nan kamar yadda kowa ke son kuÉ—i haka Mahmoud zai rinÆ™a sonta.
Bappa Lawan yace. "Ba'a bayarba tukun amman kada ki damuâ€. Cikin zaÆ™uwa tace.
"To ayi ayi dai a kawo dan muna da bukatar kuÉ—inâ€.
Mujahid ne zaune gaban iyayensa cikin karaya yace. "Abba ni kam na haƙura da Fariyda tunda an tabbatar cewa mijinta bai saketaba, kawai a aura min Murjanatu ƴar ƙanwar baban nashi kenan. Cikin jin dadi yace.
"Ai dama ni nafi son ka auri Murjanatu fiye da Fariyda dan ita murja ita ke sonka, Fariyda kuma kai ke sontaâ€.
A daren ranar juyi kawai yakeyi amman ya kasa bacci yau kwana na huÉ—u kenan bacci na kaurace masa.
Washe gari wuraren ƙarfe goma zuwa sha ɗaya zaune suke a parlour Ummi yau harda Salma Salim da Sulaiman, abincin da Aunty Amina ta kawo musu sukeci.
A karo na biyu Goggo Dada ta kalleshi tace.
"Mahmoud a zuba maka abinci kaci dan ka daina zama da yunwa kaga yadda ka faÉ—a kuwaâ€. Kai ya jujjuya haÉ—i da cewa.
"Sai an jima zanciâ€. Sallamar Jidda ne yasa suka kalli Æ™ofar shigowa da harara Salim ya tarbeta hakama Salma, Sulaiman kuma murmushi yayi haÉ—e da cewa. "Gafa Amaren January she shiyasa gidan ke Æ™amshiâ€. Tana kallon Mahmoud da yayi tamkar baya parlour tace.
"Aifa dole gida yayi kamshi ga angawaye har biyu da amaryaâ€. Sai kuma ta kalli Amina dake cewa. "Oh jidda ko kunya a gabansu Ummi faâ€. Murmushin jin dadi tayi haÉ—e da cewa.
"To ni da iyayena nifa su Ummi ba surkai baneâ€. ÆŠan guntun murmushin Ummi tayi tace.
"Ai dai kamâ€. Goggo Dada kuwa filin zama ta nuna mata kusa da Hafiza kai ta jujjuya ta zauna kan 1 seatter dake manne da É—aya 1 seatter da Mahmoud É—in ke zaune akai cikin yauÆ™i da zumuÉ—i da zokoÉ—i ta É—an ronÆ™ofo tana É—an leÆ™a fuskarsa daya kauda gefe idonsa a lumshe kamar maiyin bacci.
Ɗan ƙara matsowar da tayine ya bawa damtsen hannunta zuwa sharabar hannunta mannewa da damtsen hannunsa zuwa sharaɓarsa da hannunta ɗaya kuma kan fuskarsa ta kife ganin hawaye dake ɗan tsilalo mishi, a hankali yaja hannunsa dan a zatonsa Amina ce ko Ummi, jin ana share mai hawaye bayan tafin hannunta ne yasa shi ɗan ɗago kanshi ba tare da ya buɗe idoba.
Ummi kuwa É—akinta kawai ta nufa Goggo Dada ido ta zaro cike da kaÉ—uwa, Amina kuwa da hannu ta fara yiwa Jidda alaman ta matsa ita kuwa da yake hankalinta na kanshi batama lura da abinda Amina ke mataba Sulaiman kuwa murmushi yake a zatonsa idon Mahmoud a buÉ—e yake, Salim kuwa da yake iya hango idon Mahmoud É—in a rufe yake murmushin mugunta ya saki, Salma kuwa a kufule take kallonta cikin jiwa yar uwarta kishi.
Hannunta da damtsen hannunta da ya kuma gogar nasa a take wani irin masifeffen ƙaiƙayi na fitar hankali ya fara ratsa fatarsa ne yasa shi buɗe ido dai-dai lokacin da ta sunkuyo kanta kan fuskarsa tana ƙara share mai sabbin hawayensa dake zubo.
Ido biyu yayi da Jidda cikin wani irin fusata da zafin zuciya ya ɗago hannunsa dake ɗaya gefen wani irin makantaccen marin ya yarfa mata da hannunsa na hagu, wasu irin taurari masu tartsatsin wutane suka fara gilmawa ganinta wani marin ya kuma sharara mata kan kunenta haka yasa ta miƙe tsaye cike da gigita ido baya gani kunne baya ji, cikin jin daɗi Dakin ya saki dariya mai sauti haɗe da tafa hannu da jinjina kai.
Shi kuwa Mahmoud wani irin mugun kallo ya watsa mata haɗe da yarfa mata tagwayen marukan da suka sata sakin wani irin ihu ƙara mara daɗin amo, hannunsa ya shaƙo wuyanta haɗe da fara magana da murya mafi bada tsoro.
"Ke dan uwarki ni kike taÉ“awa, ni mate É—inki ne zaki nuna min ke yar iskace da zaki zo ki shafa min jikinki a nawaâ€.
Ido ta zazzaro tana neman iskar numfashi hannunta duka biyu ta kai kan nasa tana kiciniyar ceton kanta haka yasa duk hannunsa biyu suka fara ƙaiƙayin.
Da gudu Ummi ta iso parlour dai-dai lokacin da
Sulaiman ya miƙe da sauri ya tsaya gaban Mahmoud Goggo Dada kuwa Mahmoud ɗin ta zuba wa ido ganin yadda ya fara wani irin gigitaccen susa in one second fatar hannunsa daga sama har zuwa ƙasa ta feso masifaffun ƙurajen masu jarabar ƙaiƙayi tuni hannunsa duka biyu sunyi jazir kamar wanda soyeyyen man gyaɗa ya zube masa a jiki, kan fuskarsa ta meda idonta duk inda fatar hannun Jidda ya taɓa yayi jazir ya feso ƴan ƙurajen tuni duk fuskansar ta kumbura haka yasa Amina fara kamo hannun tana sosa mishi dan ya samu ɗayan ya sosa masa fuskarsa Ummi kuwa Jidda data faɗin ƙasa saboda yadda ya hankaɗata da ƙarfi yasa ta faɗi a gigice, da sauri ta kamo hannunta ta tsaida ita, har yanzu idonta baya ganin komai sai taurarin, kunnenta kuma dumm yayi shiyasa bata jin me suke faɗa sai wani irin tarin azaba da takeyi dan neman numfashinta da ya maƙale a maƙoshinta dan azabar shaƙar da yayi mata ƙulu-ƙulu take zaro ido gami da tari da riƙe wuyanta da sauri Ummi ta zaunar da ita tana faɗin,
"Innalillahi Jidda sannuâ€.
Abba kuwa da tun ihun Jidda na farko ya shigowa parlour ta ƙofar parlour Ummi wanda dama zai fitane jin ihu yasashi shigowa abakin ƙofar ya tsaya haɗi da zuba musu ido.
Salma kuwa cikin jin daɗi take dariya tana kallon Jidda da tasha shaƙar mutuwa, Salim kuwa kai ya jinnina yace.
"Madallah maganin ki kenan, Allah ya maka al'barka Mahmoud maganin mayun mata masu naci kenanâ€.
Shi kuwa Mahmoud Æ™arÆ™arwa jikinsa ya farayi tamkar mazari, susa yake yi a gigice, murya na rawa alamun zazzafan zazzaÉ“i ya diro masa kenan, da sauri ya rinÆ™a miÆ™awa Salim É—aya hannun yana cewa. "Salim help me tayani sosawa. Ummi a bani Duvet sanyi-sanyi nakeji kamar zai kasheniâ€.
Sai kuma kawai duk ya fara wani irin ƙarƙarwa har ya zamo ya faɗi ƙasa duk da tareshi da Amina keyi, da gudu Goggo Dada taje ɗakinta ta ɗauko Duvet ta dawo parlour a guje.
Sake duvet ɗin tayi tare da dafe ƙirji murya a hautsine tace.
“Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un Mahmoud! Mahmoud!! Mahmoud!!!â€
Ta kirashi karo na ukun da ƙarfi ganin yadda yake ƙaƙƙandarewa yana mummurɗewa da lauyewa jiki duk na rawa sai kuma ya fara jan wani irin nannauyan numfashi ido na kafewa.
Kuka Amina tasa tare da kallon Abba da ya iso kansa Goggo Dada ma kuka ta saki tana faÉ—in.
"Yaya Mahmoud Yaya kaga yadda yakeyi fa.
Dai-dai lokacin Yah Ahmad da yazo daren jiya ya shigo da sauri ta ƙarasa ciki ganin halin da Mahmoud ɗin ke cikin yasashi sunkuyowa ya tallaboshi jikinsa cikin tsananin kiɗima ya dakawa Salim tsawa.
"Kai É—aga min shi mu tafi asbitiâ€. Da sauri Salim É—in ya sunkuyo jiki na rawa suka É—agashi suka fita.
Sulaiman da Abba na biye dasu a baya.
Cikin fargaba Ummi ta koma ta zauna dirsham gefen Jidda da har yanzu jinta da ganinta bai dawoba shiyasa batama san sun fitaba.
Amina kuwa da Sauri tabi bayan Sulaiman kafin su fitoma Yah Ahmad da Salim sun sa Mahmoud É—in a mota har sun ja sun fita.
Motar Abba suka shiga Sulaiman ya zauna mazaunin driver Abba a gefensa Amina a baya har ya ja sai kuma ya tsaya ganin Goggo Dada ta fito baya ta shiga wurin Amina kana suka bi bayan su Salim É—in.
Salman kuwa hannun Hafiza ta kamo ta zaunar da ita cikin tausarta tace.
"Kiyi shiru Hafiza in sha Allah ba abinda zai sameshi zai samu lfy, Allah ya kareshi da sharrin tsoffin da sabbin mayuâ€. Tayi mgnar tana hararan Jidda da sai yanzu jinta da ganinta ya dawo shiyasa taji abinda Salma ta faÉ—a ta kuma fahimci zaurance da tayi mata na ramawa Fariyda abin da sukayi mata ranar da suka je gidansu, amman neman numfashi da takeyi da zafin da wuyanta keyi yasa bazata iya cewa komai ba.
Maman Samira da Samira da Huzaifa ne duk sukayi jugum a tsaye.
Cikin jan dogon numfashi ta miƙe tsaye.
Da sauri Ummi tace.
"Jidda zaunaâ€. Ido na zubda wahaye da fizgo numfashi tace.
"Ummi zan je dubashi neâ€. Ta Æ™are maganar tana kallon Hafiz da yanzu ya dawo daga makaranta.
Kallon tambaya yake musu sai kuma ya matso wurin Ummi dake cewa.
"A'a Jidda ai bamu san wanne asbiti suka nufaba kije gida Hafiz meda ita gidaâ€.
Juyawa tayi ta fita tana faÉ—in. "Hafiz yi sauri zomu tafiâ€. Bayanta yabi suka fita.
Salam na rakata da harara ta miÆ™e ta fara tattare parlour, da sauri Samira ta matso tana faÉ—in. "Aunty bari zanyi tattararâ€. Tana kallon Ummi da tayi tagumi tayi shiru tace.
“Ummi ki kwantar da hankalinki In sha Allah zai samu lfy. Allah ya yaye masa wannan larurarâ€. A hankali tace. “Amin ya Allah Salma am. kuma wai a haka ake batun haÉ—asu aure taya zasu rayu a haka ina fatarta ta taÉ“a tasa ya shiga irin wannan halinâ€. Cikin sauri da jin daÉ—i da samun dama da kara bawa Ummi tsoro tace.
"Innalillahi Ummi ai zata masa illar da zata kasheshi in ance ya aureta kallifa iya hannunta ne ya taba nashi ga yadda yake yiâ€. Numfashi mai nauyi taja kana ta miÆ™e ta nufi bedroom É—inta tana faÉ—in.
"Bar aikin Salma je É—akin Goggo Dada Samira zata tattara.â€
Da sauri ta É—auki hand bag dinta da wayarta ta nufi bedroom É—in Goggo Dada tana kiran layin Mamy.
Samira kuma ta fara tattare wurin Mamanta kuma ta koma kitchen taci gaba da aikinta. Hafiz kuwa Mamanta ta kira dan jin ya jikin Mahmoud É—in kuma ina suke.
A can gidan Baba Malam kuwa, tana tsaye a kitchen ita da Saddiqa tana haɗawa baba Malam abincinsa Mamy ta shigo kitchen tana miƙa mata waya tace.
"Gashi Salma ceâ€. Amsar wayar tayi ta kara a kunne.
A can hospital ɗin kuwa Su Salim da Amina da Sulaiman ne tsaye a bakin ƙofar ɗakin cike da ruɗu, a cikin ɗakin kuwa kusan Dr ukune a kanshi Abba na gefe shi da Yah Ahmad
Da ƙarfi ya fara sa...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.