Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 31
By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 103
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*
https://chat.whatsapp.com/F93CYFGSIWA3ewhl8cCAYW
Barkanku da zuwa zauren A.A GARKUWA FOUNDATION inayi mana fatan alkhairi, fatan wannan haɗakar tamu na taimako zata kaimu ga Jannatul Firdausi, *Ga Ramadan ya ƙarato mai akwai da mai niya, taimakon sadaka ga ma buƙata ciyarwa ko shayarwa in Allah ya hore mana kamar yadda muka yi last year ga account da zamu fara tara kuɗin ga mai niya 5843176522 Moniepoint Aysha Aliyu Garkuwa*
jama'ata kune Æ™arfina, domin su jama'a Rahama ne, ba haushe yace hannu É—aya baya É—aga jinka, yan uwa ita sadaka bata yawa kuma bata kaÉ—an ko Naira 500, 1k 2k 3k 4k 5k har zuwa 10k 20k 50k 100k kai har 1million zuwa sama in Allah ya baka iko, kai koda Naira É—arice kike bayar zamuyi farin ciki da ita, kuma ajiyace maidaraja, wacce Allah ne zai bamu sakamakonta kada ki/ka raina abinda ke hannunki domin manzon Allah S.A.W yace muyi sadaka koda da tsagin dabino ne! kada kuma muyi tunanin sadaka zata raunata dukiyar mu ko ta hanamu ci gaba, kada kuma muga sadalar tayi yawa in kina da hali ko 1M kika bayar akwai ma buÆ™atan da in za'a raba musu zasu iya neman Æ™ari ma. Kuma Manzon Allah yace, ita sadaka tana kashe masifa kamar yadda ruwa ke kashe wuta, Allah Ubangijin talikai shi zai yi mana sakayyar al'khairi da zamu wanzar duk Æ™anÆ™antarshi, Allah ya bamu ikon haquri da zama da juna, Allah ya bamu ikon taimako, ya kuma sa mana a mizanin kyawawan ayyukanmu ya taimakemu fiye da yadda zamu ke taimakawa jama'a. mu haÉ—a hannu da hannu mu ciyar da mabuÆ™ata a Ramadan. Afwan In nayi miki/maka wani kuskure cikin rashin sani da ajizanci na d'an adam a gafarceniðŸ¤ðŸ™ðŸ»
A taimaka domin Allah
"To yanzuma can zamu tafiâ€. Ya faÉ—a yana shafa lip É—inta na Æ™asa data tura sai kuma ya É—aura da cewa.
"Amman in baki daina turo lips nan ba yanzu zan warware komaiâ€. Da sauri ta miÆ™e tsaye, shima miÆ™ewa yayi ya riÆ™o hannunta suka fito bayan sun tattara komansu.
Kai tsaye gidan Aunty Amina suka shiga
Bayan sun gaisane ta zuba musu abincin hannu ta miƙawa Mahmoud tace.
"Bani su kuci bincin tunda kukazo sun maÆ™aleku sunÆ™i barinku ku sararaâ€. Ta Æ™are maganar da amsar Zaid dake hannunsa sai kuma ta zuba mishi ido ganin ya jawo Fariyda yana faÉ—in. “Zo kisha damun nanâ€. Ya faÉ—a yana kallon abincin da Aunty Amina ta zuba musu rice and Stew ne mai kyau wanda yaji naman kaza yayi lugub sai damun fura da nono mai kyau haÉ—e da kwakwa da inabi da Apple anyi blending nasu sunyi lugub.
Zaitoon dake maÆ™ale da wuyan Fariyda Aunty Amina ta karba tana faÉ—in kuci abinâ€. Yana mannawa Fariydan mug É—in damun yace.
"Mom Hafiz kawosu suma in basuâ€. Da sauri tace. “Sunfa sha sosai musamman Zaid dan ita Zaitoon saida na dage na samu tasha sam bata son cin abinciâ€. Yana Æ™ara jawo Fariyda yace.
"Ga wacce ta gado sam bata son cin abinci ai kinga shi Zaid da ya gadoni baya cutar da kansa da yunwaâ€. Tana kallon Fariyda dake zamewa rungumar da yake mata tace.
"Gasky kam dan da Zaitoon ta fishi komai lokacin da baida lfy, daya warke kuma yana cin abinci gashi ya fita da komaiâ€. Shigowar Daddyn Hafiz ne yasa Fariyda saurin matsawa tare da gaida Daddy Hafiz É—in dake miÆ™awa Mahmoud hannun. Bayan sun gaisane ya wuce parlour sa yana cewa. "Naga Birthday yayi kyau sosai yau duk Hafiz ya zuÆ™e mana data da ganin hotunankuâ€. Bayan sun gama cin abincin su fito ne ta zubawa Salma ido.
Salim kuwa Baya ya buÉ—ewa Mahmoud yana faÉ—in mu tafi dama can wurin naku zamu tafi sai Hafiz yace min kuna nan.
Bayan ya zauna Salma kuwa Zaitoon ta karba a hannun Aunty Amina ita kuwa Fariyda gyara riƙon Zaid tayi ta shiga baya kusa da Mahmoud ɗin.
Ita kuwa Salma gaba kusa da mijinta.
Gidan Bappa Lawan kuwa. Kuka Jiddan keyi tamkar zata shiÉ—e, tun Mama na lallashi har ta fara hatsala cikin takaici tace.
"Tunda bazaki daina wannan kukan akan hotunan banza da hofin da kika ganowa kankiba sai kiyi tayi har hawayenki su kare na gaya miki ki kwantar da hakalinki in dai sihiri gasyane to wlh sai Mahmoud ya sonki ya mance wannan mayyar yarinyar, ai magna ta Æ™are tunda mun samu an bada sadaki kuma har na kaisu wurin Malam ki jira sakamako kawaiâ€. Cikin disashesshiyar murya tace. "Dan Allah Mama ki kira Yah Salim kice masa yazo wlh ina son yin mgna dashi neâ€. Tana jawota jikinta tace.
"Ai tun dazu na kirashi yace min wani É—an aiki yake yi anjima kaÉ—an zai zoâ€.
Acan wurinsu Mahmoud kuwa, tunda suka shiga Airport Fariyda ke binshi da ido cikin mmkin tace.
"Appiy me zamu yi a Airport kuma?â€. Yana mikawa Salim Zaid yace.
"Zo mu shiga ciki kiga abinda zamu yiâ€. Kai ta gyaÉ—a mishi haÉ—e da mikawa Salma hannun tace. "Kawo Zaitoon naga tana ta kallonaâ€. Da sauri Salma tace. "Ke zata ragewa kwalliyarki armashi kije yanzu zaku fito muna jiranku a mota.â€
Shafa kan Zaitoon É—in tayi haÉ—e da cewa.
"To kinji me Auntyki tace koâ€. Sai kuma ta meda kallonta kan Zaid tace. “Zaid ku jiramu yanzu zamu fitoâ€. Daga nan tabi bayansa, suna shiga Salim yaja hannun Salma suka koma cikin motarsu yaja suka tafi kai tsaye gidansu suka wuce da yaran.
A anan Aminu Kano international airport kuwa, wani irin kallon Fariyda ke masa lakacin da suka shiga cikin jirgin hannunta da ya riƙe yake jane yasata kasa masa turjiya a hankali tace.
"Appiy jirgi kuma ina zamuje su Mamy basu sani bafa?â€. Fuska a tsuke yace.
"Nine mijinki nine wanda sharia ta bawa damar zaɓa miki wurin zama a duk inda nakeso nake da dama, in kuma ban kai bane sai ki gaya min.†a hankali ta jujjuya mishi kai dan ganin yadda fuskarsa ta koma Mahmoud ɗin baya data sani mara wargi mai tsauri da mgnar da ba fashi.
Ido na zubda wahayen tayi Æ™asa da kanta zuciyarta cike da tunani iri da ban da banâ€.
Suna shiga First class É—in ya zauna tare da jawota jikinsa ya manna kanta da kafadarsa ya rungumeta da hannunsa É—aya É—aya kuma ya manna kan cikinta murya cikin sanyin yace.
"Duk inda zamuje bazan cutar da keba, kiyi haÆ™uri ban gaya Miki bane dan gudun kada kiÆ™i yarda, Please My Angel ki saki ranki, na zaÉ“i barin kasar da kene dan kada su Abba su rabamuâ€. Murya can Æ™asa tace.
"To ina zamujeâ€. Yace.
"Yanzu dai Saudia zamuje muyi Umrah mu roÆ™i Allah ya dauwamar mana da zaman lafiya da farin ciki, ya kare mu da sharrin masu sharri ya É—auramu kansu Abba su barmu mu rayu cikin aminci ba tare da sun sako mana wata a tsakaninmu baâ€. Ya Æ™are maganar yana kissing Cheek É—inta dai-dai lokacin kuma jirginsu ya É—aga.
Gidan Bappa Lawan Salim ya wuce. Shiru Salma tayi rungume dasu Zaid tana jiyo sautin muryar Jidda dake magna cikin kuka da disashesshiyar murya take faÉ—in.
"Yah Salim ka tabbatar Wannan number Yah Mahmooud ne ke amfani dashiâ€. A kufule yace.
"Ni abokin wasan kine ko na taÉ“a miki karya, layin Yah Amin ne wanda suke amfani dashi na kasuwanci, kuma wayar da layin duka Mahmoud ke amfani dashi shi yasa wayar da sim nashi suna hannun matarsaâ€.
Da ƙarfi ta saki kuka haɗe da cewa.
“Mama da gaske kenan Yah Mahmoud ne yayi min wannan text message ɗin.†shiru Mama tayi cikin ƙuna da rashi abin faɗa, ita kuwa Jidda cikin rauni tace.
“Yah Salim dan Allah menene aibuna da zaisa Yah Mahmood ya kasa sona, Kalli text message É—in da yamin faâ€.
Amsar wayar yayi ya fara duba saƙon tabbas number wayar Yah Amin ne kuma salon rubutun Mahmoud ne komai a ƙayyade.
*“Iyayena sun isa dani kuma sun kai su sani inyi koda bana so, sai dai ina baki shawara kada ki yarda ki bari a É—aura miki aure da inuwar ajalinki, dan idan har zan yi zaman aure dake to zanyi zaman aure da kare da in rayu dake gwara na auri kare ko ba komai nasan dama dabbace ita, idan har manufarki ki haÉ—ani da mahaifina ne ki sani, duk yadda yake son in aureki bazai kai matsayin da zai iya fushi dani ko ya tsine min ba, nasan bazaiyi hakaba ki gayawa mai kaiki gidajen bokaye duk abunda kukeyi a kaina, Allah yana nuna min a mafarkina baki da nasara shawarata kada ki bari ki rasa imaninki da Æ™uruciyarki a karkashin fasiÆ™in boka zindigi maÆ™iya Allah da Manzonsa ba majuse mai bautar wutaâ€.
Numfashi mai nauyi Salim ya sauke kana a hankali yace. "In dai Mahmoud ne to ya bar kasar ma baki É—aya ya gudu da matarsa dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya sai kuma abi wani sarkinâ€.
Kai Jidda ta riÆ™e da hannun duka biyu tana faÉ—in. "Yah Allah ka yaye min son Yah Mahmoud ko ka kasheni in huta da wannan azabarâ€. Kwaffa yayi ya juya ya fita.
A parlour ya samu Salma rungume da yaran Zaid ya karɓa suka tafi babu sallama.
Gab da magrib Mama ta gayawa Bappa Lawan abinda ke faruwa haÉ—e da nuna masa hotunan birthday da videos da kuma text message É—in da Mahmoud É—in yayiwa Jidda.
Amsar wayar Jidda yayi ba tare da yace mata komaiba ya fita da alamun masallaci zai wuce. Daga nan Masallacin ƙofar gidan Abba yazo bayan an idar da sallan magrib ne kafin ayi ishe Bappa Lawan ɗin ya nunawa Abba videos and pictures da kuma saƙon Mahmoud da kuma faɗa masa wai ya ɗauki matarsa sun bar ƙasar. Kamar yadda Bappa Lawan ɗin bai cewa Mama komaiba haka shima Abba ba abinda yace sai tasbihi yaci gaba dayi sai dai duk jikinsa na tsuma.
Washe gari bayan sallan Asuba kamar kullum suna shan tea Abba ya kalli Goggo Dada dake cewa Sulaiman.
"Kai wai ina Mahmoud ne nifa tun shekaran jiya da dare da muka haÉ—u daku zaku fita wunin jiya duk ban ganshibaâ€. Sulaiman ya miÆ™e yana faÉ—in.
“Nima dai ban ganshibaâ€. Salim ya gyara zamansa haÉ—e da cewa.
“Ni dai yace min zai yi tafiya jiya, ina ta kiran layinsa dai baya shigaâ€. Cikin É—imuwa da tashin hankali Ummi tace.
“To ina yaje? Mahmoud ne zai yi tafiya bai sallamemu baâ€. Fuska a tsuke Abba yace. “Ai ba tafiya yayiba guduwa yayi da Fariyda shi kuwa Salim ya saniâ€. Ya Æ™are maganar cikin tafasasshiyar muryar dake nuna fushinsa da fusata.
Sai kuma ya nunawa Sulaiman da Salim hanyar fita. Da sauri suka fita. Goggo Dada kuwa bayan Ummi tabi, suna shogowa Parlour Ummi ta kira Mamy tana É—agawa tace.
“Hajia Asma'u Barka da safiyaâ€. Mamy tace.
“Barka dai ya gida“. Ummi tace. “Alhamdulillah ina É—iyata Fariydaâ€. ÆŠan jim Mamy tayi sai kuma tace.
“Hmmm tabi mijinta sun guduâ€. Murmurshi mai sauti Ummi tayi cikin sauÆ™e numfashi tace.
“Dasu Zaitoon É—in suka tafi ne?â€. Da sauri Mamy tace. “A'a yanzu da Malam ya ritsa Saddiqa tace mana bada yaran suka tafiba wai suna gidan Salim wurin Salma amman zasu maidasu wurin Aminaâ€. Ajiyan zuciya Ummi ta sauÆ™e ta É—aura da cewa. “To ina suka tafi yaushe zasu dawoâ€. Mamy na kallon Baba Malam dake jinsu tace. “Gaskiya su kansu Salma da Salim basu san ina Mahmoud ya nufa da matarsaba sun dai san da tafiyar amman basu san ina zasu jeba ko yaushe zasu dawo, ita Saddiqa dai tace dama tun last week Mahmoud É—in ke ce mata zasu guduâ€. Murmurshi Ummi tayi haÉ—i da cewa. “Allah ya karesu ya tsaresu a duk inda suke Allah ya huci zuÆ™atan su Malamâ€. Mamy tace. “Yoh ai shi malam abinma dariya ya bashiâ€. Numfashi mai nauyi Ummi ta fesar haÉ—i da cewa. “To Alaji kam abun ya fusatashi fusata mafi tsauri dan wlh fuskarsa kamar zatayi ruwan jini, kuma ban san waya gaya masa sun gudun ba, ban taÉ“a ganin fushi ziraran miraran a fuskarsa irin na yau baâ€.
Baba Malam ya miƙawa Mamy hannu alamun ta bashi wayar.
Cikin kamala yace. “Hajia Fatima kiyi shiru kada ki sake kawo masa maganar har sai randa shi ya kawo miki ita, dan kina mgnar zai huce a kanki, yaran kuma zan kira Salim É—in a kawosu gida wurinki ko akawosu nanâ€. Cikin sauri da kawaici tace. "A bar Hajia Asma'u ta huta haka, gashi yanzu babu Raihana ba mahaifiyarsu idan Saddiqa da Amira suka koma dai bata da mai tayata raino, ya kawosu nan gani ga Goggo Dada ga Samira da maman Samira Hafiza ma yawanci nan take yanzuâ€. Cikin gamsuwa da hakan yace. "To ba matsala zai dawo dasu nan É—inâ€. Da Yamma Salma ta dawo dasu da rakiyar Aunty Amina da tazo da nufin É—aukarsu nan Salim ke gaya mata Baba Malam yace a kaisu wurin Ummi.
**************
Yau kwana goma sha uku cib da tafiyarsu. Zaune suke a harabar farfajiyar Masallacin Madina tunda aka idar da sallan isha basu tashi daga inda suke ba, a hankali ta kwanta kan tattausan dardumarsu blue color, sanye take da Abaya Brown color mai masifar kyau da ƙyalli sai ɗan mayafi Black blue data yane kanta dashi sai wani irin ƙyalli fuskantar keyi yana fidda bayyanennen kyanta, shi kuwa Mahmoud Farar jabbilace a jikinsa kanshi babu ko hula sai sumar kansa dake ɗan kwance ta gaba kaɗan sai wani irin ni'imtaccen ƙamshi mai sassayan ƙamshi suke bazawa, wayarsa na gabanshi yayinda yake motsa lips nashi a hankali yana tasbihi . A hankali ta ɗan lumshe idonta tare da ɗan zamewa ta kwanta gabanshi tana fuskantarsa tare da yin pillow da hannunta cikin sanyi take sauƙe numfashi jiki cike da kasala tayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali dabino da zaman da laban haɗi da Apple da Grapes ya ratsasu sai wani irin ƙyallin madara sukeyi.
A hankali ya ɗan ture wayarsa dake gabansu gefensa kaɗan hannunsa ya buɗa mata tare da yi mata alamun tazo, cikin kasalar da baccin daya ƙara sata yin lip ta ɗan yunƙuro tare da kwanciya kan cinyarsa, kusan a tare suka lumshe ido kanta ya ɗan sunkuyo ya manna lips nashi kan goshinta haɗi da ƙara rungumota da hannunsa ɗaya ɗaya hannun kuma ya ɗaura kan cikinta a hankali ya fara shafa cikin sasssyan lafazi yace.
"So sorry Lil Amin na wahal min da my princessâ€. Ƙara mannewa tayi a jikinsa tana shaÆ™ar Æ™amshin jikinsa. Yana kallon kwayar idanunta data buÉ—e yace. "Alhamdulillah mun gama Umarar fatan Allah yasa munyi karÉ“eɓɓeâ€. A hankali tace. "Amin Ya Allahâ€. Cikin kulawa yace.
"Batun tafiyar mu ina son ki gaya min Æ™asar da kikeso mu wuce daga nanâ€. Tana shafa sajensa tace. "Appiy ni Canada kawai nake son zuwa a wannan weather É—in ina son zuwa canâ€. Fuska ya É—an Æ™wabe a hankali yace. "Babe meyasa sai Canada a wannan watannin sanyinsu yana yawa kuma gashi baki cika lfy ba, ni kuma in na shiga irin wannan weather É—in bani da haÆ™uri zanyi ta takura miki a ko da yaushe zan kasance manne dake, gwara ma Istanbul nasu bai kai Canada baâ€. Cikin sanyi tace. "Ni dai Canada nake son zuwaâ€. A hankali yace. "Meyasa sai canâ€. Tana Æ™ara mannewa a jikinsa tace.
"Haka kawai nakeji ina son zuwa Canada ji nake yi tamkar akwai wani abuna mai mahimmanci wanda nake so da fatan gani a can. Please Appiy ka kaini Canada.†cikin sanyi yace. "Yadda kike so haka za'a yi daga nan sai *Canada*...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.