Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 31 of 31

Ba iya dan shauƙi da nishaɗi kawai bane manufar alƙalami na, Duba darrusan littafin
SAƘAR MAKAFI
1 Ƙarfin addu'ar uwa kan ƴaƴanta.
Da addu'a ɗaya Ummi tayi yajawa Mahmoud jarrabawar rayuwa ƙaddarar tauyewar halitta kamar yadda ta roƙa Saida ya shekara goma sha bashi da lfy kunga ƙarfin addu'ar uwa da wani kekkyawan fata tayi masa ma hakan zai kasance da izinin Allah.
Iyaye duk ɓacin rai mu san addu'ar da zamuyiwa yaranmu.....
2 Kambun baka gskya ne kan kyau. kyau ne ya zamewa Mahmoud masifar da tasa mata sashi a gaba harda sihiri Saida sukaci nasarar medashi mazinaci.
3 Sirrin Hasbunallahu wa ni'imal wakheel.
Kamar yadda likitoci suka tabbatar Fariyda bazata iya haihuwa da kantaba, gashi data riƙe ambaton Hasbunallahu wa ni'imal wakheel ta haihu a sauƙaƙe
4 Illar bin bokaye ma yaudara. Kamar yadda Boka yayi ta yaudar Mama da Jidda da Mujahid ya maidasu ATM dinsa, haɗi da rabasu da imaninsu da nufin hanasu azumi da salla a ƙarshe ya yi harin ketawa Jidda haddinta.
5 Son ɗan uwa da riƙon amana. Irin son da Mahmood keyiwa Yah Amin da yaransa har a bayan ransa.
6 Zafin nema baya kawo samu da Jidda ta samu Mahmoud.
7 Sihiri gskya ne karkayi zaton kafi karfisa yana iya kama mutum kamar yadda Idaya ta samu nasara akan Mahmoud lokacin da yake wasa da ambaton Allah.
8 Riƙe Azkarul Sabah wa masa shine babban rigakafin da Mahmood ya riƙe tun bayan nasarar da malam Yayi ya karya sihirin da Idaya tayi masa da ayatul shifa.
Shi yasa Jidda bata sake nasara a kansa ba.
9 Sakayya duk abinda kayi sai an maka.
Yadda idaya tayi masa sihiri haka wani katon banza yayiwa yarta ya maidata jaririyar karuwa.
10 Ƙarfin ikon iyaye da ribar musu biyayya.
Ma karanta a rinƙa kula da darrusan cikin littafi ba iya nishaɗin ba...

Alhamdulillah Allah na gode maka da haɗani da masoya makaranta ma biyan littafifaina mutane na gari masu sanin ya kamata da kara da kawaici Alhamdulillah mun fara littafin SAƘAR MAKAFI lfy mun gama lfy ko musu ba'a tabayi a group ɗin Arewapen comments ba kullum ana cikin hira da raha da nishaɗi da barkwanci wlh ina alfahari daku mutanen Arewapen ku mutanena na musamman inaji daku ina alfahari daku. Kutanen SAƘAR MAKAFI group 1 and SAƘAR MAKAFI KRM group ngd matuƙa da ƙauna

Wlh nama fi jin kewarku akan kewarsu Mahmoud É—in dan yadda ake hira da dariya ayi raha.
An samu kekkyawar fahimtar juna.
An fara lfy an gama lfy ba faÉ—a ba fushi Alhamdulillah. Da ni'imar samun abokan zama na gari.
Duk makaranta book ɗin SAƘAR MAKAFI mutanen kirkine da suka mallaki hankalin kansu masu kara da kawaici da uzuri ngd ngd mgd muku matuƙa Allah ya bar zumunci da qauna ya nuna mana sabon littafina da zana fara bayan salla lfy in sha Allah mai ɗan karen daɗin CHUƁAƊO🙏🏻🤝😘😘😘 Ina mai neman yafiya ga duk wacce nayiwa ba dai-dai ba ko cikin rashin sanine ki/ka yafe min wani lokacin yawan mutane ga typing ga editing ga ƴan comments kansu suna buƙatar lokacina ga masu biya sabbin shiga group ga masu son kaya ga hidimar gida gana aiki ga yara ga yan uwa baƙi da yan gida. Kuyi min uzuri in na miki wani abin da ya ɓata muku rai babba ko yaro mace ko na miji na kusa ko na nesa ku yafe min ni Na yafewa kowa Allah ya yafe mana, Allahumma Balligna Ramadan bil imana Allah ya nuna mana azumi lfy ya nuna mana salla lfy in sha Allah bayan salla ina tafe da zazzafan littafin na CHUBAƊO ma'ana zaɓeɓɓe kenan. Alhamdulillah

By
*GARKUWAR MARUBUTA*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.