Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 30 of 31

Washe gari da rana. Da sauri Fariyda ta fito jin Zeenat tasa ihu Zaid ta gani a gefe yana zare mata ido.
"Ba nace ki gyara min ɗaki naba”. Tana tura baki tace. "To ai zan gyara”. Fariyda tace. "Dukanta kayi kenan dan kasata sharan ɗaki batayi ba”. Zayyad ne yace. "Ammey bai daketa bafa”. Kwaffa Zu'ayd yayi yace. "Ammey Aunty Zee tana da kukan banza ne fa”. Tana kamo hannun Zeenat tace. "To yasa Zaitoon mana ta gyara manasa ko Yseera ai kuwa kun iya gyara masa ɗakin”. A hankali yace. "My Happiness Zaitoon karatu takeyi shiyasa ban sataba”. Mahmoud dake kallonsu ne yace. "Zee jeki share masa”. Tana yin ƙasa da kai tace. "To Appiey bari in sa wayata a caji”. Daga nan ta shiga bedroom ɗin su ita da Zaitoon tana shiga suka jiyo ihunta kuma. Kwaffa Mahmoud yayi yace. "Me kuma”. A tare suka fito da Zaitoon na faɗin. “Appiy itace fa ta takani dan na tureta ne tayi wannan ihun”. Kamo hannun Zaid da Zaitoon yayi suka haura sama kam 3 seatter ya zauna dasu ya zama yana tsakiyarsu cikin so da kulawa yace. “Zaid Zaitoon kuna ɓatawa Ammeynku rai a duk sanda taji kunsa Zeenat kuka gani take kamar bama sonta ne”. A tare sukace. "Appiey muna sontafa in bata ban gidan ba dadi ko gidan Mamy bana son taje ta kwana sai gidan yayi shiru ba mai ihu da dariyar neman mgna”. Ido ya zuwa Zaitoon dake cewa. "Appiyn ai tare zamu tafi da ita gidan Yah Huzy ko”. Kai ya jujjuya yace. "Ai gani nake bakwa sonta bazan baku Goggo Dada naba kuje kuyi ta dukar min ita kuna sata kuka”. Cikin iya kar gskyar zuciya Zaid yace. "Appiyn ai in nayi aure zata koma gidana”. Yana murmurshi yace. "A hakan kuna cin zalinta”. A tare sukace.
"Appiy bama dukantafa ita ko kallonta akayi in taga dama zata ihu in Ammey tazo tayi mana faɗa kuma tana tafiya zata zo tayi ta bamu haƙuri”. Cikin fahimtar salon shaƙuwarsu yayi ta musu nasiha.
Ita kuwa Zeenat tana parlour ta lakaci Zayyad ta lakaci Zu'ayd Lil Amin da ya shigone yace. "Wannan fa itace Jerry ɗin gidan mu, shiyasa in bakya nan gidan ba dadi yanzu Mom nan tace inzo in kira mata ke wai yau tun safe bataji da ihunki ba”.
Yazeed dake kwance ne yace. "Nima ban ganta bane nace bari unzo in leƙa Jerry wata ƙil bata da lfy ne ko parlour Ummi bata jeba”. Zayyad yace. "Taƙi ta fita ta buwayemu nan da masifar tsokana”. Murmushi Mahmoud yayi yana kallon yadda Zeenat ke murguɗa musu baki, sak Fariyda lokacin da take tashen son girmanta da ce masa ai ta girmeshi tunda ita matar yayansa ne. Ita ma Fariyda murmushi takeyi dan ganin Zeenat take kamar yadda take yi wasu lokutan. Da sauri Zeenat ta zaro ido jin Mahmoud ya riƙo hannunta murya na rawa tace. "Wayyo Allah na Ummi Goggo Dada Abba Appiy zai dakeni”. Gaba ɗaya dariya suka sa gani shima ɗin Appiey zata yi masa yadda takeyiwa su Zaid ta haɗasu da iyayen nasu. Jawo hannunta yayi yana dariya yace. "Zo mu tafi can wurinsu Abba ai anan bazasu jikiba”. Cikin tsoro tace. "Appiey a tuba”. Fariyda kuwa da yaran duk dariya sukayi suka zauna suna faɗin halayyar Zeenat ɗin.
A can waje kuwa hannunta na cikin nashi ya ƙara jawota jikinsa da kyau cikin nuna kulawa da so yace. "My life meyasa bakya jine kina son ki rinƙa tsokana ana dukanki ina jin zafi a raina kina sa Ammey fushi dasu Hamma Zaid ko”. Murmurshi tayi tana juyowa ta kalli mahaifin nata tace. "Appiyn ka cewa Ammey kartayi fushi dasu ta daina yiwa Hamma Zaid faɗa bana so”. Suna shiga parlour Ummin yace. "Zan kaisu California bazasu ganki bama bare su dakeki har ran Ammey ya ɓaci ai in basa nan shike nan kin huta su Lil Amin da Yazeed da Ayman ma duk tare zan kaisu Istanbul gidan Yah Hafiz suyi karatunsu a can. Yaseer da Yaseera kuma zasu tafi Sudan gidan Aunty Samira acan zasu karatunsu. Afif da Zayyad Zu'ayd kuma India zan kaisu a bar miki gidan ke ɗaya”. Fuska ta kwaɓe ido na cika da kwalla tace. "Please Appiey kuyi haƙuri kada a barni ni kaɗai zanbi su Hamma Zaid ko a kaini Qatar gidan Aunty Hafiza”. Murmurshi Ummi tayi tana kallon yadda yake shafa kanta yana faɗin. "To Goggo Dada na ki daina neman tsokana Allah yayi miki al'barka zaku tafi tare dasu Yah Huzy ya matsa a barki kiyi karatu a can”. Goggo Dada tace. "Takwarata zamuyi kewarki duk gidan zai zama ba daɗi in bakya nan”. Ummi na dariya tace. "Kunnen mu zai huta da ji ihun banza”.
Alhamdulillah an É—aura auren Huzy da Zaitoon.
Zaid da Nuraiha.
Salim da Salma ne suka raka Æ´an California.
Sulaiman da Humaira suka raka Æ´an Sudan.
Mahmoud da Fariyda suka raka Æ´an India.
Cikin birnin Ahmedabad a Airport sukayi kiciɓis da Sa'ad da matarsa da ƴan yaransu uku. Bayan sun gaisa da gabatar da yaransu ne ganin su Zayyad da Zu'ayd yasa Sa'ad cewa. “Twins kune kuka sa aka ɗaureni nida Faisal ko, Big broz ina my princess Zaitoon da Zaid”. Cikin yar kunya Mahmoud yace. “Zaiton tayi aure shima Zaid nayi mishi aure”. Kai ya jinjina haɗe da cewa. "Ikon Allah abin ba wuya, ga kuma Zayyad da Zu'ayd Allah ya raya mana su bisa inami”. Fariyda da Sa'ida matar Sa'ad a tare suka ce Amin shi kuwa Mahmoud yan kwawan yaran Sa'ad ya zubawa ido yana faɗin.
"Masha Allah ga Ziyada dai da Zayyad kamar zamuyi haɗin da Allah baiyi a baya bako”. Da sauri suka meda yaran kan Zayyad da Ziyarar ke ta kallo shima ita yake kallo sai kuma suka meda kallonsu kan Zu'ayd dake cewa Zubaida. "Kuma karatu zakuyi a nan ne”. Cikin sakin fuska da jin daɗi Sa'ad yace. "To ni dai na bawa Zayyad Ziyada Zu'ayd kuma na bashi Zubaida in dai har sun haɗa kansu”. Daga nan suka karɓi number juna.
Suna shiga garin Ahmedabad É—in komai ya fara dawo musu a idon zuci. Su Zayyad É—in suka fara kaisu har cikin makarantar su har É—akunan kwanasu inda yake makarantace ta musamman makarantar da Dr Imran Patel ya buÉ—e ne.
Wayar da Fariyda keyi da Ammar ɗan Aunty Saddiqa ne yasa batama lura da hotel ɗin da suka sauƙaba. "Eh Ammar Zeenat ɗinka tana California”. Sai kuma tayi shiru jin yana faɗin. "Ammey to mu sai yaushe zamu girma”. Murmurshi tayi tace.
"Kun ma kusa girma ai Ammar kada ka damu”. Gani ɗakin da suka shiga ne yasata sauri katse kiran. “Ya Salam ta faɗa rungumeshi ƙamƙam jikinta haka shima ya rungumeta tsam a jikinsa yana faɗin.
“Kin tuna”. Kai ta gyaɗa mishi haɗe da cewa.
"Inada ka ɓalla min hannu”. Yana kissing Cheek ɗin ta yace.
"Inda kika soke min zuciya da dafin sonki”.
Watansu É—aya a Ahmedabad kafin suka koma hakana su Salma da Humaira.
Bayan shekaru huÉ—u.
Aka sake É—aura auren zuminci. Lil Amin Ya auri Yaseera yar Humaira.
Su Zayyad sun auri yayan Sa'ad, Ammar ɗan Aunty Saddiqa ya auri Zeenat. Yazeed ya auri ƴar Raihana ƙaramar haka dai duk kayi auratayya cikin zumunci da aminci Alhamdulillah an samu kekkyawan zaman lafiya da amana da yelwan arziƙi.
Yau Aunty Amina tazo sun wuni saboda zuwansu Zaitoon da Huzy kuma anan gidan suka sauƙa harda Huzy Hafiz ma da matarsa.
Sun wuni hira sai dare da Aunty Amina ta tafi ne.
Mahmoud ya ɗan juya ganin ba kowa a parlour sai Hakim ɗan su Zaitoon dake bacci akan sofa a hankali ya sunkuyo kan Fariyda yace. "My Angel zo muje ciki inyi miki tausa sun zo sun gajiyar min dake”.
Ya ƙare maganar yana mai ɗagata cak ya nufi bedroom ɗin. Cikin raɗa tace. "Appiy mu huta a parlour”. Cikin raɗa yace. "No my Angel mu gudu bedroom mu buyawa al'ƙalamin Aysha Aliyu Garkuwa YAR FULANI. murmurshi tayi a hankali tace. "Gwara kam mu buya kada ta gane min miji nasan MI WAMITI. Yana kwantar da ita yace. "Idonta na ciwo ai ko ta ganni ba matsala ɗan yaro nefa ni”. Da ta saƙalo wuyansa da hannunta duka biyu tace. “Appiy kasan NAMIJI BAYA KAƊAN fa”. Hannunsa ya fara cusawa cikin rigarta cikin wasa yace. "Babe ina so A TASAYAWA JUNA ki barni in ƙaro wata. BANDIROWA ta tayaki kula dani”. Tana sunkuyowa kanshi tace. "Koda gaddara bana fatar ta sako wannan RUBUTACCEN Al'AMARI a rayuwata bana. Cikin raɗa yace. “Cikin HUKUNCI ALLAH ma da ke kaɗai zan ƙare rayuwata koda ace bakya ji bakya gani iya ke kaɗai kin ishe dan NAKASA BA KASAWA BACE bare ma kuma Alhamdulillah ke lafiyeyyiyar mace ce mai cike ni'ima dan ke GARKUWA tace, kuma TUBALI na farin cikin rayuwata bani da abinda zan miki SAKAYYAH dashi sai in zauna dake ke laɗai IN DA RAI dai kin isheni har gaban Abadan duk rintsin SAƘAR MAKAFI ya ƙare maganar da jawo duvet ya rufesu ruf.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Mun godewa Allah dani daku makaranta Allah ya nuna mana ƙarshen littafin SAƘAR MAKAFI lfy.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.