Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 104
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

Nigeria
Salim ne zaune bisa Carpert yasa Jidda a gaba cikin sanyi yace.
"Maijidda kalleni”. A hankali ta ɗago kanta ta kalleshi cikin tausasa harshe yace.
"Jidda nifa ɗan uwankine ke ƙanwatace ta jinina uwa ɗaya uba ɗaya muke, Jidda nine fa nasha nono na bar miki, Jidda ina sonki kamar yadda ko wanne ɗan uwa yake son yar uwarsa”. Ido na cike da kwalla tace.
"Yah Salim da gaske kana sona”. Gyara zamansa yayi tare da cewa. "Sosai ma Jidda ina sonki kuma ina son kiyi farin ciki a rayuwarki dan bazan so abinda zai cutar da keba, in kin yarda zan baki shawara”.
Gyara zamanta tayi tace.
"Na yarda Yah Salim”. Gyaran Muryar yayi haɗi da cewa.
"Zan baki shawara a matsayina na ɗan uwanki kuma ɗan uwa ga Mahmoud wanda ni da Sulaiman munfi kowa sanin halinsa Jidda ki cire Mahmoud a ranki kada ki yarda ki bari a aura mikishi, ki fahimci abinda nake guje miki Mahmoud baya sonki so na aure kuma bazai taɓa sonki ba ko ya aureki tozarta ki zai yi dan baya tsoron kowa, ni kuma bana son in tsanesa bana son ki zama sanadin wargaza mana family bana son ki zama haddasanar gaba a Family ɗin mu, dan muddin Mahmoud ya wulaƙantaki zanji zafi a raina dan ke jini nace Please dan girman Allah da Manzonsa ki haƙuri da Mahmoud”. Fuska a tsuke take kallonsa cikin takaici tace. "Ni dama nasan baka sona”. Da sauri yace. "Jidda ina sonki amman ina son ki auri wanda zai soki ya riritaki kiyi zaman mowa ba boraba”. Miƙewa tsaye tayi haɗi da cewa.
"In dai kana sona da gaske to ka barni a aura min Yah Mahmoud zan jirashi duk sanda zai dawo”. Daga nan ta ɗauki jakarta ta fita tana faɗin. "Ni da nasan dan haka ka kirani ma da ban zoba gidanka ba”.
Bayan kwana biyu
Ido Ummi ta zuba wa Amina haÉ—i da cewa.
"Tunda ya tafi fa bai kirani ba, yau kwana goma sha bakwai cib banji munryarsa in na kirasa kuma layinsa baya tafiya”. Sai kuma ta ɗan yi shiru haɗe da jan dogon numfashi taci gaba da magna a hankali cikin so da raunin zuciyar uwa a kan ɗanta tace.
"Nayi kewarsa ina son ganinsa ina son jin muryarsa, ki gaya masa kada yaji tsoron kirana, ni bana fushi dashi na sani matarsace ta Sunnah yadda bashi da laifi ko gaban Allah nima bashi da laifi a wurina ina kuma yi musu addu'a da fatan alkhairi”. Numfashi mai sanyi Amina ta fesar haɗe da cewa. "Alhamdulillah Ummi ni kaina ina tsoron ki kawo min mgnar ne dan a zatona kema fushi kikeyi dashi”. Kai ta jinjina tana kallon yadda Amina ke shirya Zaitoon cikin wasu tattausan riga da wondon bacci na Turkish, gyara riƙon Zaid da ya fara gyangyaɗi tayi tace. "Ni bana fushi dashi, abu ɗaya ne banji daɗinsa ba naso ace yana nan za'ayi auren Sulaiman domin Sulaiman yayi masa hidima a rayuwarsa yana kan yi masa haka ma auren Salim baya nan akayi gashi yanzuma har an fara ribibin auren Sulaiman bashi”. Tana fesawa Zaitoon turarensu tace.
"Ummi yace min Baba Malam da kanshi yace kar ya dawo yanzu har sai ya masa mgna”.
Da sauri tace.
"To wai ina yake sai har yaushe zasu dawo wlh nayi kewarsu”. Amina na kallon Goggo Dada data idar da salla tace.
"Ummi ko su Salim basu san inda yakeba, nima bai gaya min ina sukeba, ke kuma kullum fa sai ya ganki in dai kikaga Hafiz ko Huzaifan sun zo suna riƙe da waya to video call yake yi dasu yace su kawo ya ganki, zakiga kullum da safe Hafiz na zuwa ya ɗauki su Zaid suje cikin garding ko baki gate video call yake yi dasu yaga su Zaid suyi ta hira da mamansu da Appinsu”. Cikin mamaki Goggo Dada tace. "Haba shi yasa da sun dawo zasuyi ta wasa suna Oyoyo Appiy Ammry Ammey ashe suna ganin iyayen nasu ne shiyasa”. Ummi tace. "Kira min shi Amina”. Cikin sauri tace. "To amman karki gayawa Abba”. Da sauri tace.
"Tab Hmmm waya isa ya kawo masa maganar Mahmoud ni har tsoron a kira sunansa a gabansa ma nakeyi”. Video call ta kirashi cikin Sa'a ya ɗaga yana amsa sallamarta tace. "Ina Ummina nayi missing nata ina Goggo Dada, Mom Hafiz Ummi tana min addu'a kuwa kodai fushi take yi dani itama, har yanzu batayi miki mgnata ba”. Da sauri Ummi ta amshi wayar tare da zuba masa ido haɗi da cewa.
"Fushi kuwam Babana bazanyi fushi da kaiba, muddin kuma ina raye ai duk lokuta biyar sai nayi maka addu'a. Allah yayi maka al'barka ya karemin kai da kariyarsa da ɗiyata Fariyda”. Cikin jin dadi yake murmushin mai faɗi haɗi da lumshe idanunsa yana motsa lips ɗinshi a hankali. "Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil alamin Allah ya amsa Ummi nayi missing ɗinku ina Goggo Dada na”. Da sauri Goggo Dada ta matso tace. "Gani nan Mahmoud muma munyi kewarka yaushe zaka dawo? Ina Fariyda”. A hankali ya juyo wayar kan Fariyda dake kwance gefensa tayi bacci ta turo ɗan lip ɗin ƙasa tana tsotsar na sama a hankali yace. "Gata nan tayi bacci ko in tada ita”. Murmurshi Ummi tayi tace. "Ashe dai ita Zaitoon ta gada da turo ɗan leɓen ƙasa ta ritsa na sama da tsotso, barta kada ka tashe da safe zamuyi waya”. Kai ya gyaɗa alamar to sai kuma ya kalli Goggo Dada yace. "Goggo Dada baƙin bikin sun fara isowa ko”. Aunty Amina tace. "Gobe tawagar mutanen Bauchi zasu iso dangin babansa Sulaiman. Yau munje munsha kamu gobe walima jibi kuma ɗaurin aure”. Yana ɗan gyara rufewa Fariyda jikinta da jibgegen duvet yace.
"Allah ya sanya al'khairi yasa ayi a sawo a watse lfy”. Nan dai sukayi ta hira har sai kusa sha biyu suka katse kiran.
Gidan Baba Malam kusan duk nan tawagarsu amarya Humarai da Zainab da ƙawayensu duk a nan suke da kuma su Aunty Saddiqa Rashida Khadijah da dai duk matasa matasan harda Raihana ma ta kuma zuwa Amman wannan karon ita kaɗai tazo.
Aunty Saddiqa ta kalli Raihana dake cewa.
"Aunty Fariyda ta gaisheku”. Da sauri Salma tace. "Da me kukayi magna nifa sai in Yah Salim ne ya kira wayar Appiyn Zaid nan muke gaisawa”. Aunty Saddiqa tace. "Nima da wayarsa muke magna dama ai wayarsa na hannunta sai dai WhatsApp call ne zai tafi ina gafa basa ƙasar dan ina son in tambayeta ina suke sai kuma in fasa dan yan manne da ita ko yaushe”. Da sauri Aunty Rashida tace. "Ke Saudia suke bari kiga video da wata ƙawata tayi musu a Madina. Ta turi min jiya tace min.
Ni kam Rashida kwanaki naga wata balarabiya a madaina tayi masifar yi min kama da ƙanwarki Fariyda nan, wlh har video nayi musu ita da mijinta sunyi masifar burgeni yana zaune ita tana kwance kan cinyarsa, shine nace ta turi min tana turo min kuwa naga ai Fariyda ce da Mahmoud a harami kun gani”. Ta ƙare maganar da nuna musu video da ƙawartan tayi musu lokacin da suke masallaci da yaga tana jin bacci ya jawota cikinsa”. Wurmurshi Adda Nana tayi haɗe da cewa.
"Yah Salam mu dai kam dai mata muka rako duniya, ga wannan ruwan so da kulawa sunma mance a bainan nasi suke kai Mahmoud yana son Fariyda”. Murmurshi Aunty Sadiya tayi tace. "Bayan so da ƙaunar da yake mata kuma ya iya tattalin macene, mu ma ɗin ana sonmu kawai mazan ne kowa da halinsa”.
Zainab ne tace. "Ai Salim ɗin Salma ma guda ne amman Yah Farooq na da Sulaiman dai da alamun ustazaine”. Murmurshi Humaira tayi tana shan damun kayan matan da Aunty Saddiqa ta haɗa musu wurin Garkuwa tace.
"Ai itama Fariyda Yah Amin ustaz ne kuma taji daɗin zama dashi a haka dan haka muma lfy lau zamu zauna a sirrance zasu nuna mana so”. Khadijah tace.
"Shi Mahmoud ai ko gaban ubanwa baza love yake romantic guy ne ajin farko”.
Canada cikin birnin Toronto a tamfatsetsen Hilton Toronto, hotol ne mai girma na alfarmar zaune yake kan kujerar dake gaban table ɗin da System nashi ke kai, a hankali ya gyara zamansa tare da gyara mata kwanciya a jikinsa haɗi da jawo duvet ɗin ya rufeta da kyau, hannunta duka biyu tasa ta zagayo ƙugunsa haɗi da manna kanta bisa ƙirjinsa. Shi kuwa Mahmoud hannunsa duka biyu na kan system nashi da alamu aiki mai mahimmanci yake yi.
Jin alamun tana motsa lips É—inshi ne yasashi dan sunkuyowa kanta, fuskarta ya shafa a hankali haÉ—i da cewa.
"My Angel bakiyi bacci bane”. Cikin sanyi ta ƙara dugungunewa a jikinsa duk da room heater da kuma tattausan duvet dake jikinta tana ɗan jin sanyi kai ta ɗan jujjuyawa masa alamun a'a cikin kulawa yace. "Kina jin yunwa ne? Ko muje kan gadone in gaisa da Lil Amin zakiji ɗumi”. A hankali ta fara yin rau rau da idonta da suka cika da kwalla, cikin sauri yace. "Subahallahi Babe gaya min me kikeso”. Murya a narke tace. "Appiy Mamy na fa fushi take yi dani, na biyoka ban gaya mataba, ina son yin mgna da ita”. Yana shafa kanta yace.
"Tun yaushe nake ce miki zan kirata kece kike cewa kina kunyarta me zaki ce mata, nace miki bazata miki faɗaba kinga ko Malam bai miki faɗaba da kuka gaisa Al'barka ma yasa mana dayi mana addu'a ko”. Ya ƙare maganar yana kiran Mamy video call ta system nashi ba tare da tasan yana kiran ba sai Muryar Mamy taji tana cewa. “Assalamu alaikum Mahmoud”. Jin haka ne yasa tayi saurin juyowa ido biyu sukayi da Mamynta haka yasa tayi saurin zamewa ta durƙusa kan guiwowinta tana mai sunkuyar da kai murya na rawa tace.
"Mamy ina kwana”. Mamy dake yiwa Mahmoud addu'a.
Cikin kewar ɗiyar tata ta ɗan kalleta haɗe da cewa. "Lfy lau Fariyda ya kewarsu Zaid”. Cikin jin sanyi a ranta tace. "Mamy mun kusa dawowa ai, ina Malam ya su Sadiq da Aunty Saddiqa”. Tana ɗan murmushi tace. "Su Saddiqa amara ƙirjin biki suna can suna shirya amarya in an idar da sallan za'a daura aure angawaye zasu shigo suyi hoto”. Murmurshi tayi cikin jin sanyi a ranta tace. "Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lfy”. mamy tace.
"Amin Ya Allah. Allah yayi muku al'barka”. Tare suka amsa da Amin sai kuma tace.
"Sai anjima ina da baƙi yanzuma ina ɗakin Malam ne shiyasa na amsa na shigo zanyi sallan azahar sai anjima”. Daga nan sukayi sallama. Murmurshi tayi haɗe da zama kan sawunsa tace. "Appiyn Mamy bata fushi dani tasa min al'barka”. Miƙewa tsaye yayi da ita jikinsa yace. "Alhamdulillah hankalinki ya kwanta sai kuje nima zan sawa Lil Amin al'barka”. Da sauri ta zame tayi gefe da ɗan sassarfa ganin ya biyo ta a baya yana murmurshi.
Nigeria
Bappa Lawan ne ya zuba wa Abba ido cikin motar da suka nufi gidan Malam da tawagarsu dan É—aura auren cikin sanyi yace.
"Har yau baka ce komai ba kan batun Jidda Mahmoud”. A kufule yace. "Shi Mahmoud shi ya haifemu ne ko mu muka haifeshi ya gama gudunsa ya dawo ya samu matarda dama munyi da wajewa dashi, zai ɗauki matarsa kuma zan aura masa Jidda zai gama gudunsa ya dawo a yau din nan a yanzu za'a ɗaura aurensa da Jidda.”.........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.