Trending Hausa Novels

Sakar Makafi Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Sakar Makafi Book 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 18 of 31

By
*GARKUWAR MARUBUTA**SAƘAR MAKAFI*
Page 105
Na
*Aysha Aliyu Garkuwa*

https://arewapen.com/u/garkuwa
*Mutanen Arewapen fatan alkhairi garemu baki daya, Please ga link na Arewapen kuyi following na ku danna min like*

*Gareku masu son buɗe Arewapen ko suke da wata matsala da Arewapen ga number Umar mai Arewapen ɗin kuyi masa magna in sha Allah zai gyara muku matsalarku 09031774742 idan kuma baki da App ɗin Arewapen ɗin ne kwata-kwata ki fara sauƙe App ɗin kafin kiyi masa magna*

Bayan an taso daga É—aurin aure.
Wuraren ƙarfe uku.
Numfashi mai nauyi Aunty Amina ta sauƙe tana kallon Hafiz da dake ci gaba da musu bayani.
"Wlh ba'a ɗaura auren Uncle Mahmoud da Aunty Jidda ba, ina jinsu a mota suna hira Abba na cewa dole sai anyi auren. Bappa Lawan yace. "A'a babu dole fa Yaya tunda har Mahmoud baya so kuma ya nuna mana dukkan alamu a karshe ya fito ya faɗa baki da baki yadda saƙo zai isa garemu, ya kuma ɗauki matarsa ya gudu da ita dan an tauye masa haƙƙinsa haka yasa ni kam abin ya fita raina”. Cikin yanke magna Abba yace. "Dama ba don kai za'ayi ba sai dan Jidda tunda har tana sonshi kuma taƙi ta saurari kowa a saboda shi dan haka dole shi zan auramata duk halinshi zata juri zama dashi kamar yadda itama Fariyda ta jura”. Cikin sanyi Bappa Lawan yace. "To ai ita kanta Jidda tace min ta haƙura”. Cikin rashin gamsuwa Abba yace masa anya kuwa? Juyowa Bappa Lawan yayi da kyau cikin iya kar gskya yace. "Wlh tallahi da kanta tazo jiya da dare tace min ita kan ta haƙura da batun auren Mahmoud itama bata so tunda shima baya sonta a barshi kawai”. Kai ya jinjina yacewa Hafiz.
"Kai juya muje gidan Lawan ina son magna da Jidda.
A hankali ta kuma yin ƙasa da kanta ido na zubda ƙwallan murya na rawa tace. "Abba da gaskene na haƙura da Yah Mahmoud tunda har baya sona a bari kawai”. Da sauri yace. "Ko baya sonki in dai kina sonsa sai an ɗaura”. A hankali tace. "Abba nima bana so”. A hankali Yah Ahmad da Salim suka sauƙe numfashi jin daɗin yadda ƙanwar tasu ta nemawa kanta salama. Abba yace. "To in bakya sonsa wa kikeso kin san dai bazan barki kici gaba da zama ba aure bako?”. Cikin sauri Yah Ahmad yace. "Ai tunda abokina Jamil yazo ya ganta yace min yana sonta, in dai har ta amince sun fahimci juna ai shike nan ɗan Adamawa ne yana aiki a Abuja.” cikin kulawa Abba yace. "Kin ganshi ne?”. Kai ta gyaɗa. "Yayi miki kina sonshi”. A hankali tace.
"Abba ban sanshi ba tukun”. Cikin gamsuwa yace. "To Allah yayi miki zaɓi mafi alkhairi in shine alkhairi Allah ya daidaita ku in Kuma bashi bane Allah yayi miki zaɓi mafi alkhairi. Daga nan Abba yace mu wuce masallaci mukaje aka ɗaura auren Uncle Sulaiman da Aunty Humarai kaɗain.
Cikin jin dadi Ummi ke hamdala hakama Goggo Dada.
Harda mata Uncle Ahmad na Katsina da duk sauran yan uwansu.
Alhamdulillah ansha biki lfy amaraya ta tare a cikin gidansu Ummi a part ɗin da aka gina da sunan Mahmoud wanda komai na cikinsa iri ɗaya ne dana Yah Amin wanda yanzu babu komai a ciki tunda aka tattara gado komai aka Saida sai ɗaki daya inda Hafiz ke kwana da Sulaiman ɗin kafin ayi aure baƙi kowa ya koma har Aunty Saddiqa ma ta koma Yola da Amira.
Yau mako biyu da bikin Sulaiman.
Zaune suke gaban bokan cikin gamsuwa da yaƙini Mama tace. "In dai zai dawo da kanshi yace ya yarda yana sonta ya hurawa ubansa da uwarsa wuta har sai sun sa an ɗaura auren to kawai ka gaya min duk abinda kakeso na aiki zamu kawoshi”. Wuƙi-wuƙi yayi da ƴan mitsi-mitsin idanunsa ya shimfiɗe shapcecen leɓensa yace. "Ku fara ajiye min 700k idan buƙata ta cika ku cikato 300k sai kuma kuɗin kayan aiki su sai mutanena ɗin sun faɗi me da me akeso zan kiraku a waya in gaya muku, wannan aikin daga shi babu wani sama dashi yadda nayi aiki aka bada sadaki haka zanyi wannan ayi aure idan sun lissafa min kayan aikin da sukeso zan kiraku a waya in gaya muku”. Da sauri Mama tace. "Ka tabbatar aiki zaiyi”. Cike da shirka yace. "Kina kokontone? Ko so kike ki ɓata mana aiki tun kafin mu farashi, maza kuje in sun faɗi abin da sukeso na aiki da zan gaya muku”. Jidda tace. "To batun kuɗin Mama akwai sune?”. Tana kallon bokan dake fakewa da sunan malam tace. "Kai baka karbar transfer ne dole sai cash sai in mun koma in ka gaya mana abin da ake buƙata na aikin sai mu kawo da 700k ɗin”. Boka yace. "Tashi ku tafi kada ku yarda ku gayawa kowa”. To sukace kana suka tafi.
Canada.
Yau garin Toronto ya ɗebi masifeffen sanyin mai ratsa jiki da zuciya tun da safe ake Snow har yanzu sha biyun rana snow akeyi tamkar ruwan sama, duk garin yayi fari fat ko ina dusar ƙanƙara ta rufe komai hakan yasa garin yin shiru mafi akasari mutane suna gidaje dan har hutun aiki aka bada saboda tsananta sanyin da tun shekaran jiya ya ɗan fara ta'azzara Vibrating da wayarsa keyi da numfashi dake fita haɗe da sambatu da surutai ne kaɗai ke tashi a ɗakin sai muryarta Fariyda can ƙasa-ƙasa da take amsa kiran da yake auna mata da sanya al'barkarsa.
Room heater ne ke busawa babu ƙaƙƙautawa hakan yasa ɗakin yin ɗumi bugu da kari ga hidimar yiwa Lil Amin taki da ake fafatawa. Cikin rawan jiki ya zame ya kwanta gefenta haɗe da yin rigingine manyan idonsa ya lumshe yana mai jan dogonon numfashi haɗe da yunƙurowa ya sunkuyo kanta, girarsa ɗaya ya ɗaga mata haɗe dasa yatsarsa manuniya ya sharce mata zufar daya tsatstsafo mata kan goshinta ya ɗan yarfa.
"Allah yayi miki al'barka ya biyaki da jannatul Firdausi Babe Ngd Ngd”. Ya ƙare maganar da kife tafin hannunsa duka biyu kan ɗan cikinta ya fara shafawa a hankali sai kuma ya sunkuyo ya fara kissing ɗinta tako wani sashin jikinta.
Tafin hannunta tasa kan kafaɗunsa da suke da damshin zufa kaɗan a hankali tace. "Appiy ana kiran wayarka tun ɗazu”. A hankali ya mirgina ya kwanta rigingine ya jawo ta jikinsa ya kwantar da ita kan ƙirjinsa haɗi dasa hannunsa ya jawo duvet ya rufesu, hannunsa ɗaya yasa kan bedside drawer ya lalubo wayarsa tsaki mai tsawo yaja ganin sunan Salim picking call ɗin yayi haɗe da cewa. "Wai dan Allah Salim kai wanne irin mutum mai jarabar nacin tsiya ne, miss call nawa kayi min”. Tsaki Salim yaja haɗe da cewa. "Ban san uwar me kakeyi ba 5 miss call nayi ma baka ɗaukaba kusa 47 minute ina kira shiru kamar matacce”. Yana gyara mata kwanaciyarta yace.
"Da yake kuma kanka babu daɗi sai kaci gaba da yi min kiran mafarauta, dole sai ka matsa min yanzu wannan kayi aikin hakali kiran magidanci a safiyar nan dole sai ka katse min hamzari bazaka barin in samu gamsuwa cikin salamaba”. Dariya mai ƙarfi Salim yayi haɗe da cewa. "Banza kar dai ka kashe yar mutane, ni ka tashi ka hau online mu ƙarasa aikin nan ka dai ga Ramadan saura kwana biyar ko shida lissafin nan yamin yawa Abba ya zuba mana idone kawai kai ka gudu Sulaiman ya kasa komawa Gomba tunda ya ɗanɗana ya haukace yaƙi ya koma, ni kaɗai kuka bari da aikin fa najima Abba na cewa Sulaiman ɗin bazai koma ba zai maida Ishaq ne Gombe”. Cikin haki da sauƙe numfashi dake ƙara tabbatarwa Salim yanzu ya gama jihadi murya a sarƙafe da ajiyan zuciya yace. "Ba matsala ni na gama komai akwai ɗan abinda nake ƙara dubawa ne zan tura maka zuwa gobe”. Cikin tsiya Salim yace. "Ya naji kana ajiyan zuciya ne kam kuka kayi ne”. Da sauri ta rumtse idonta jin yana faɗin. "Ban saniba”. Daga nan ya katse kiran yana mai tashi zaune da ita yace. "Muje muyi wanka azahar tayi”.
A hankali ta ajiye cup É—in coffee da tasha kana ta zame ta kwanta haÉ—i da yin pillow da cinyarsa.
"Na gajiyar da ke ko my Angel? Ya faɗa yana shafa kanta. Tace. "Bacci nakeji”. Yana ɗan turo Tray abincin da aka kawo musu daga kitchen ɗin hotel ɗin yace.
"Zo ki kwanta in miki massaging cinyoyinki”.
Bayan kwana biyu zaune suke gaban Abba Salim ne ya fara ajiye wasu manyan files guda 28 kanshi na ƙasa yace. "Abba gashi duk Mahmoud ya gama haɗa jadawalin mallakin ka da za'a cirewa Zakka!”. Kai Abba ya jinjina haɗi da amsar file ɗin, yana kallon Sulaiman da ya miƙo masa guda 17 yace. "Wannan duk na lissafin kayan da muke dashi a ƙasa ne a Gombe Adamawa, Zamfara, Lagos, nan kano Katsina, Sokoto, da dai duk 17 state inda muke da branch”.
Amsa yayi yana kallon Salim da ya miƙo masa wasu biyu yace.
"Wannan na bashin da muke bine ɗaya, ɗaya kuma na biyan bashin da ake bin mune duk Mahmoud ya biya ba bashin kowa a kanmu”.
Zamansa ya gyara yace.
"Allah yayi muku al'barka ya albarkaci zuriyar ku, yau zan zauna da Malam Ibrahim dan kirdade nawane adadin zakkar mu na wannan shekarar”. Da sauri Sulaiman yace. "Abba Mahmoud ya tura maka adadin ribar da muka samu a wannan shekarar ta email address ɗinka. Sosai kasuwa tayi kyau bana mun samu ribar da muka daɗe bamu fidda kamar taba kuma Alhamdulillah da yake Mahmoud ya daɗe da fara tattara komai yasa dukkan MD ɗinmu na ko wanne gari ya haɗa komai akan tsari abun yazo da sauƙe gsky Mahmoud yayi ƙoƙari sosai”. A take launin fuskarsa ya sauya hanyar fita ya nuna musu yace. "Kuje na sallameku Allah yayi muku al'barka”
Amin sukace kana suka fita.
Yau garin Canada hidima akeyi sosai ko ina na garin ƙyalli yake sabida yau jumma'a gobe week end ne ga kuma Valentine Day.
Anan Nigeria ma wasu na hidimar ranar masoyan.
Zaune suke a parlour Ummi. Humaira ne gefen Ummi tana yiwa Zaitoon kitso Sulaiman na bisa kujerar dake bayanta. Tsaida Zaitoon tayi tana faɗin. "Mun gana tsaya munga kitson yayi kyau Masha Allah”. Goggo Dada tace. "A dole dai wai son gyara ƴar taku kukeyi ko”. Aunty Amina dake shigowa ne tace. "Kai Goggo Dada abin ya motsa kenan ai dama ita yar tamu a gyaren take”. Tayi mgnar tana zama kusa da Goggo Dadan.
Ummi tace. "In dai kun yarda yar taku a kekkyawarce ai sai ku bari mu muyaba”. Salim dake shigowa ne yace.
"Ai mun lura ba yabawar zakuyi ba shiyasa gwara mu yaba abun mu da kanmu”. Goggo tace.
"Yabon kaifa”. Da sauri Sulaiman yace. "Ilimi ne”. Dariya sukayi baki ɗaya.
Salma dake bayan Salim ne ta zauna gefen Humaira tana shafa kan Zaitoon dake tsaye tsakaninsu.
Bayan sun gaggaisane.
Aunty Amina tace.
"Alhamdulillah gidanmu ya cika har fiye da da, ga Humaira ta meye gurbin Fariyda ga Sulaiman ga Salim da Salma a kusa,
Yanzu kam in sha Allah farin cikin gidanmu zai dawo, more Especially ranar da su Mahmoud suka dawo, gashi da mukayi Sa'a basu tafi dasu Zaid ba.
Goggo Dada tace. "Ai gwara ma da basu tafi da suba dan da sun tafi dasu ma da tuni Abba ya kwaƙulosu a duk inda suka buya”. Salim na dariya yace. "Ai shima Mahmoud haka yace. Ya san in ya tafi dasu Zaid duk inda suka shiga Abba bazai barsu ba”.
Amina tace. "Ai kuwa suna kewar yaran, Hafiz yace har ya gaji da amsa call ɗi Uncle Mahmoud”.
Ummi tace.
"Nima yanzu muka gama waya, saida aka farayiwa Zaitoon kitsone suka kashe kiran”.
Humaira ta É—an kalli Ummi da Goggo Dada cikin girmamawa tace.
"Ummi zan shiga kitchen me zan dafa na lunch?”. Kafin Ummi tace wani abu Salma ta miƙe tana faɗin. "Muje in tayaki”. Aunty Amina ta kamo hannun Salma ta zaunar da ita tana faɗin.
"Na hutar daku gobe ranar masoyace, yau kuma jumma'a nasan gobe Daddy Hafiz na gida bazan samu fitaba, shiyasa ni yaune yawa ranar mosoya. Abbana da Goggo Dada da Ummina sune masoyana da ƴan ƙannena daku matansu shiyasa na shirya muku lunch and dinner duka ku huta ku kular min da ƙannena kawai”.
Kai Humaira ta jinjina tace. "To Aunty Amina ke me zan dafa miki”. Tana ɗan kallon Salim tace.
"Kada ki damu fa nayi girki mai yawa su Hafiz da Hafiza na zuwa dashi sun biya karɓar E password ɗin Huxy ne shiyasa basu iso ba, ni Daddynsu ne ya sauƙeni”.
Goggo Dada tace. “Allah yayi miki al'barka yadda kike jinƙanmu kema Allah yasa Hafiza ta jinƙanki haka, kuma Allah ya muku al'barka yasa surkanku su muku fiye da yadda kuke mana”. Amin sukace a tare. Maman Samira dake kitchen ne da alamun gyara kitchen ɗin tayi, tana ganin Amina tace.
"Ato yau dai zamu huta kenan”. Murmurshi tayi tace. "Ina Samira ƴan makaranta”. Tace. "Taje wanke kai”. Salim ne ya ɗan kalli Sulaiman da tun dazu yake ta taɓa Humaira da ƙafarsa ganin bata kulaba ne ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Aisha kawo min tea”. Daga nan ya juya ya fita.
Salma ta jawo Zaitoon ta fara yi mata hoto tana faɗin. "Kaima Zaid zo in muku hoto in turawa Appiey da Ammey”. Murmurshi Humaira tayi tace. "Ni kin tuna min ma nace mata gobe dai suyi pictures ɗin Valentine Day ta turo mana”. Aunty Amina tace. "Ai kuwa nima ɗazu mukayi waya dasu”. Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye tace. "Bari inje musha hira da Abbana”. Salim ne ya mara mata baya dan yau ya makara bai samu yaje masallaci ba sai yanzu zaije ya gaidashi. Ummi tace. "Humaira Sulaiman yace zai sha tea”. Cikin girmamawa tace. "To Ummi bari in kai mishi”.
Salma kuwa bayan Salim tabi dan zuwa gaida Abba hannunta riƙe da Zaitoon. Goggo Dada kuwa Zaid ta fara bawa indomie da tasa Maman Samira ta dafa masa.
Humaira na shiga part nasu a bakin ƙofa ta samu Sulaiman yana ganinta ya buɗa mata hannunsa yana faɗin.
"Aunty Amina tace ku kular mata da ƙannenta fa shi yasa ta hutar daku girki”. Tana manna kanta da ƙirjinsa tace. "Ai duk lokacina nakane Hubbi”.
Canada cikin birnin Toronto.
Yau Jumma'a ma gobe asabar itace ranar masoya wato Valentine Day kenan.
Hakan yasa ko ina na garin an gyarashi sai sheƙi da ƙyalli garin Toronto yake, duk da snow da akeyi bai hana hada-hada ba a cikin garin dan fita sayyayyar kyaututtukan da za'a bawa masoyan juna, da fita kama wuraren zuwa asha shagali.
Tun yamma garin snow akeyi har zuwa yanzu takwas na dare haka yasa mafi akasari shigar sanyi sukayi. Kasan cewar ƙarfe sha biyun dare dai-dai na bugawa asabar ɗin ta shiga itace kuma, Valentine Day shi yasa tun da magrib tayi duk garin ya cika da hada-hadar jama'a duk da sanyin da ake tsalawa mafi aksarin matasan garin duk sun baro gidanjesu mazansu da matansu, dan da yawa so suke sha biyun daren na bugawa dai-dai su gabatar da soyayyarsu.
Fariyda tsaye take cikin shigar sanyi T shirt maroon color da wondon blue jeans sai blue crarf dake naÉ—e a wuyanta sai Long coat maroon wanda yake har guiwarta sai hula shima blue, sai takalmin sau ciki mai tsinin gaske wanda yake har kusan guiwarta.
Shima Mahmoud komai na jikinsa blue collar ne and maroon.
Wani irin kamshi sukeyi tamkar furanni tun bayan sallan isha suka fito suna ɗan zagaya wurare da dama na garin dan yau da daren nan jirngisu zai tashi zuwa Istanbul acan zasu ƙarasa shagalin Valentine Day ɗina zasu farashi a Toronto Canada su ƙarasa a Istanbul Turkey.
Sanyi da yake ƙaruwane saboda tsanantan zubar snow yasa su shiga Goldstruck coffee dan su sha coffee mai zafi dan rage sanyin. bayan sun sha sun fitone suka ɗan tsaya bakin wurin inda yake cike maƙil da matasa wasu na zaune wasu na tsaye na wasa cikin Snow da wasu na rungume-rungume a hankali ya ɗan zauna kan kujerar dake bakin wurin tare da kamo hannunta ya jawota kan cinyarsa ya daurata haɗi dasa hannunsa kan cikinta cikin raɗa yace. "three months fa kenan amman har yanzu bai fitowa”. Kanta ta kwantar kan kafadarsa idonta na kallon cikin taron mutanen dake cike a wurin, da sauri ta miƙe tsaye cikin sauri shima ya miƙe haɗi da kamo hannunta ganin ta juya zatabi bayan wasu mutum uku da suka wuce gab dasu, da sauri ta fizge hannunta tare da bin bayan mutane ukun da suka wuce kusa dasu. Ta fara bin bayansu harda sassarfa tana faɗin.
"Yah Amin”. Da sauri Mahmoud ɗin ya sha gabanta yana faɗin.
"FARRIYYHAH Yah Amin kuma a ina ɗin, Yah Amin kuma wanda ya mutu yana dawowa ne”. Cikin hamzari ta ratsa gefensa cikin kaɗuwa tace.
"Appiy Yah Amin........

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.