A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 67
PAGE 21-22
Cikin nutsuwa Suhaima ta fito daga d'akin ta cikin shirin uniform na tahfiz da yake ranar asabar ce, cikin kitchen ta k'arasa inda Aunty Aliyah take had'a abin karin kumallo ganin sinasir take yi ne ya sanya Suhaima sakin murmishi da yake tana son sinasir sosai, cikin jin dad'i tace
"Wow Aunty sinasir kike mana yau amman naji dad'i sosai bari nayi sauri na tafi kada nayi latti "
Murmishi itama Aunty Aliyah tayi tare da cewa
"Ai shikenan sai kin dawo, zaki sha 'yar tafiya kuwa yau don Yayan ki ya fita tun asuba zuwa kai kaji da kwayaye kasuwar birni "
D'an murmishin ta mai kyau Suhaima tayi tare da cewa
"Yeeeeee ai ni yau naji dad'in haka zan tafi a k'afa saboda kullum shi Yaya shi yake kaini kuma yaje ya d'auko ni ko'ina mutum zai je sai dai a kai shi ni fah yanzu na girma " ta k'arasa fad'i tana rawa har da juyi duk dad'i ya ishe ta.
Rik'e baki Aunty Aliyah tayi tana cewa
"Tabbb kenan dad'i kike ji ai kyasha tafiya kuwa yau "
"Eh naji Allah ya dawo da Yaya lafiya ni na tafi kada ki ja min latti "
Suhaima ta k'arasa fad'a tana dariya ta fice daga gidan da sauri, tabar Aunty Aliyah itama tana dariya kafin ta mayar da hankalin ta kan abin da take yi.
Cikin d'an sauri Suhaima take tafiya saboda ganin ta kusa latti aikuwa tana shiga cikin makarantar aka rufe kofa lokacin kaman 'yan latti yayi, wata ajiyar zuciya Suhaima ta saki ganin Allah ya taimake ta bata sha dukan latti ba da sauri ta wuce cikin ajin su, da yake k'auyen nasu babu laifi akwai masana ilimin addini dana zamani dai dai gwargwado, musamman ma ilimin addini sun fi bashi muhimmanci fiye dana boko, shi yasa suke da makarantar islamiyya da tahfiz.
K'arfe 11 na safe aka tashi su Suhaima nan tayi sallama da k'awayen ta ta wuce zuwa gida, don ba 'yan kusa da su a makarantar, saboda sune kusan gidan su na k'arshe k'arshen k'auyen, a nutse take tafiyar ta kanta a sunkuye yake tana tilawar karatun alqur'an a hankali koda kana kusa da ita ba lallai kaji abin da take fad'a ba sai dai kaga le6en ta na motsawa a hankali alamar dai akwai abin da take karantawa.
Tayi nisa da tafiyar ta don tayi wajen rabin tafiyar da zata kaita gida, horn taji ana yi mata amman sam batasan da ita ake ba tafiyar ta take kawai abin ta hankalin ta kwance.
Bata ankara ba taji mota ta goge ta kad'an a jikin ta har sai da madubin motar na waje ya bige ta a gefen hannun ta, wani irin zafi Suhaima taji a hannun ta da sauri ta d'ago kanta tana kallon motar da ta bige ta zata wuce saboda hanyar bata da kyau sosai akwai 'yan kwazazzabai shi yasa bata sauri, ganin mai motar bashi da alamin tsayawa ya bata hak'uri ko yayi mata sannu ne yasa Suhaima cikin fusata tace
"Kan ubancan! lallai mutumin nan baka da mutunci a bige ka ko sannu babu ka wani wuci kamar ka bige dabba ba mutum ba "
Ta fad'a da k'arfin ta ranta a 6ace, ganin ba alamar tsayawa yasa ta d'auki wani dutsen wuta a k'asa ta saita glass d'in motar ta jefa da iya k'arfin ta sai dai bai samu glass d'in ba sai fitilar motar ta baya ta samu, aikuwa babu 6ata lokaci ya ba da sautin k'arar fashewa, babu shiri mai driving d'in motar yaja motar ya tsaya.
Suhaima kuwa dad'i ne ya kamata da taga hakan taso ma glass d'in ta samu ta fasa tun da bashi da mutunci har da sakin wani murmishin mugunta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.