A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 67
PAGE 49-50
Bayan tafiyar Sabeer Mumy kasa danne kukan ta tayi da gudu ta wuce side d'in su bedroom ta shige ta hau kuka sosai na tausayin halin da Sabeer zai shiga da kuma kukan takaici da bak'in ciki akan wata banza 'yar k'auye d'anta kamar Sabeer zai tafi neman soyayyar ta.
Da haka Daddy ya shigo ya fara rarrashin ta bayan ya janyo ta jikin shi, dakyar ta shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai da Daddy yaga tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya fita duk jinshi yake babu dad'i na tafiyar Sabeer.
Daddy yana fita daga bedroom d'in Mumy ta bud'e idanunta tare da sakkowa daga saman bed dama tayi hakan ne don Daddy ya fita ya bata waje, tana son ta samu nutsuwar da zatayi tunani na d'aukan mataki akan shegiyar yarinyar nan da zuri'ar ta don sam bazata ta6a amince wa Sabeer ya auro mata d'iyar talakawa ba, talakawan ma na k'auye wanda basusan komai ba sai nemo da kiwo inaaa abin da bazai ta6a yiwuwa ba, daman ta barshi ne don kafin ace za'a yi auren tasamu mafita haka ta tsunduma a tunani sosai na samun mafita kuma bazata yi abin da Sabeer da Daddyn shi zasu zargeta da hana wannan auren ba.
***** ***** *****
Suna tafiya a mota Sabeer kuma ya kwanta tare da tukunkune jikin shi waje d'aya tamkar mai jin bacci, hawaye ne suke fita a idon shi yana kewar iyayen shi yana kuma tunanin yanda zaman shi anan zai kasance shin Suhaima zata kar6e shi matsayin masoyin ta sannan ya 'yan uwanta zasu kar6e shi matsayin mai son 'yarsu, wannan tunanin shi yake dad'a dagula lissafin Sabeer kada su kore shi su hanashi Suhaima tsoron shi d'aya kada su hanashi neman soyayyar Suhaima.
Sai da driver yazo wurin da suka ta6a had'uwa da Suhaima anan Sabeer ya bashi umarnin tsayawa, bayan yayi parking ne sosai Sabeer ya tsaya yana kallon wurin yana tuna wani al'amari da ya ta6a faruwa a wajen har wani murmishi ne ya su6uce mishi.
Nan Sabeer ya yiwa driver magana akan ya fito mishi da kayan shi, bayan driver ya fito dashi ne nan Sabeer yace mishi ya koma gida, yana nan tsaye driver yaja motar ya tafi zuciyar shi fal tausayin Sabeer don yasan bazai ta6a iya zaman wannan k'auyen mai kama da daji ba nan cikin zuciyar shi yayi mishi addu'ar fatan dacewa.
Sabeer ya d'an jima a wajen yana dad'a nazarin wajen gaban shi na fad'uwa saboda ganin garin ya fara d'an duhu don dab ake da akirawo sallahr mangarib.
Wani d'an saurayi ne yazo zai shige Sabeer ya rasa ta yaya zai mishi magana da yaga yana kok'arin wuce shi ne yasa shi yin kar6in hali yace
"Assalamu Alaikum"
D'an jiyowa yayi ya kalli Sabeer kafin ya tsaya nesa kad'an dashi yace
"Waalaikumussalam "
"Ammm inason zan yi mata tambaya please "
Saurayin cikin mamaki ya ke kallon shi don bai zaci Sabeer yana jin hausa ba ya d'auka bature ne ko balarabe yazo yin wani abin a k'auyen nasu.
"Allah yasa na sani"
D'an sauke numfashi Sabeer yayi tare da cewa
"Don Allah ko kasan gidan wani uhm... "
Ya d'an yi shiru kad'an yana tuna sunan Yayan Suhaima da Jiddah ta sanar dashi d'an murmishi ya saki tare da ya tuna sunan yace
"Yawwa sunan shi Aliyu yana da k'anwa Suhaima kuma manomi ne "
D'an murmishi saurayin yayi kafin yace
"Na gane shi nasan gidan "
Wani sanyin dad'i ne ya kwararanya cikin zuciyar Sabeer cikin murna yace
"Yawwa don Allah taimaka min ka kaini gidan "
"To shikenan "
Nan saurayin yayi gaba Sabeer kuwa sai ya tsaya kamar an dasa shi ta ina zai iya d'aukar trolley d'in nan, ganin Sabeer ya tsaya yasa saurayin dawowa yace
"Lafiya? ".
"Ko zaka iya taimaka min da trolley d'in bazan iya d'auka ba please "
Saurayin bai yi mamaki ba don kallo d'aya zaka yiwa Sabeer kasan cewa d'an hutu ne, d'an murmishi yayi tare da kinkimar jakar, nan Sabeer ya rataya jakar laptop d'in shi suka tafi, tun ana tafiya ba'ayi nisa ba Sabeer ya fara gajiya ga wani uban tsoro da ya mamaye zuciyat shi ganin babu gidaje sosai, amman suna dad'a gaba sai ya cika da mamaki da yaga sun shiga wata unguwa duk gidaje sosai ba kamar inda suka baro ba.
A k'ofar wani gida yaga sun tsaya saurayin yace
"Ga gidan nan "
"Yawwa sannu thank U so much "
Nan ya shigar mishi da trolley d'in cikin zaure ya ajiye, laluba aljihun shi Sabeer yayi na jeans ya zaro 1k ya mik'a mishi tare da cewa
"Gashi abokina na gode sosai but ka kar6a don Allah "
Hannu biyu saurayin yasa ya kar6a tare da zuba godiya har zai wuce da sauri Sabeer yace
"Hmm jimana abokina ya sunan ka? "
D'an murmishi yayi tare da cewa
"Sunana Ashiru kuma ga gidan mu nan "
Ya k'arasa fad'i yana nunawa Sabeer gidan su wanda gida d'aya ne tsakanin su da na Suhaima.
"Ni kuma Sabeer "
"Sunan ka mai dad'i irin na 'yan birni "
Dariya ya bawa Sabeer wanda ya sanya sai da ya d'an yi murmishin dariya saboda ya kula zai yi abin dariya, daganan ya wuce ya tafi Sabeer kuwa babu neman isowa ya kutsa kai cikin gidan tamkar irin gidan nan nasu.
Suhaima tana zaune kan wani dutse tana alwala ta sallahr mangarib, ga Aunty Aliya kuma tana kok'arin sauke miyar abincin dare kenan daga saman murhu suka yi wata sanyayyar murya tayi musu sallama.
Amsawa Aunty Aliya tayi yayin da Suhaima ta tsinci kanta da bugawar zuciya na lokaci d'aya, kafin su ankare sunga mutum a filin tsakar gida a tsorace Aunty Aliya ta kalle shi yayin da Suhaima ta kusan zubewa a k'asa saboda tsabar kid'ima da tsorata na wanda ta gani a k'auyen su kuma cikin gidan su.
"Malam lafiya wa kake nema "
D'an murmishi yayi tare da d'auke idanun shi daga kallon Suhaima ya dawo dasu kan Aunty Aliya yace
"Nazo neman Suhaima ne sunana Sabeer "
"Suhaima kuma? "
Aunty Aliya ta furta hakan tana kallon Sabeer kafin ta jiyo da kanta zuwa kallon Suhaima wadda jikin ta yake rawa na tsorata.
"Eh Suhaima nake nazo nema, idan babu damuwa zanyi sallah sai nayi miki bayanin ko ni waye? "
Aunty Aliya sai tsoron nata ya ragu don kallon da tayi wa Suhaima ta karance ta tsaf alamar tasan shi amman tayi mamaki sosai na yanda Suhaima ta iya 6oye mata abu, don haka sai tace
"Toh ai babu damuwa "
Nan ta je inda suke ajiye botocin gidan ta d'auko babbar butar Yaya Aliyu da bata rabo da ruwa aciki ta ajiyewa Sabeer a gaban shi, d'an murmishi yayi tare da cewa
"Na gode "
Murmishin yak'e Aunty Aliya tayi, tana nan tsaye ya ajiye jakar laptop d'in shi dake rataye a kafad'ar shi saman wani dutse sannan ya tsugunna yayi alwala, abin sallah Aunty Aliya ta bashi sabida masallacin da nisa daga gidan ba lalle ya gane ba yana bak'o, kar6a yayi ya shimfid'a ya fara sallahr har zuwa yanzu Suhaima na tsaye tamkar wadda aka dasa a wajen ko kwakkwaran motsi bata yi, ganin haka ya sanya Aunty Aliya janyo hannun Suhaima suka wuce d'akin ta.
Cikin tsoro tace
"Suhaima wane ne wannan? "
Suhaima itama a tsorace tace
"Na shiga uku Aunty yanzu sai da Sabeer ya biyo ni "
"Ki fad'a min wane shi kafin Yayan ku ya dawo daga masallaci "
Murya na rawa ta bud'e baki zata yi magana suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gida, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa......
Aishat A Muh'd âœðŸ»
[2/10, 5:16 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.