Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 32 of 67

*PAGE 59-60*

Tana kwance kawai taji an dafa bayanta a d'an tsorace ta d'ago kanta sauke ajiyar zuciya tayi don ganin Aunty Aliya ce ta dafata.

"Tashi mu yi magana Suhaima"
Tashi zaune tayi tana mai sunkuyar da kanta tana murza 'yantsunta batason ta kalli Aunty Aliya su had'a ido kada ta karanci wani abin akan fuskarta.

"Hala Suhaima kin fara son Sabeer ne kike kishi dashi? "
A razane ta d'ago kanta tana kallonta, gid'a kanta Aliyah tayi tare da cewa
"Idan baka son mutum taya zaki fara jin haushi don kin ganshi a tsaye da wata?"

"Ni fah Aunty bason Sabeer nake ba ni ba haushi naji ba fah dana ganshi da wata a tsaye"

"Shikenan tun da ni ban isa ki fada min matsalar ki ba amman tabbas kwanaki biyun nan kin canja don ba haka kike ba, amman tun da kin ce ba haka ba"
Tana gama fad'in haka ta juya zata tafi da sauri Suhaima ta sanya hannun ta ta rik'o na Aunty Aliya da D'an k'arfi ta matse hannunta

"Ni kada ki ji min ciwo kawai ki cikani na tafi tunda ni baki d'auke ni matsayin Yayar ki ba kuma abokiyar shawarar ki, ni da nasan Suhaimar dana sani ba haka take ba bata iya 6oye min komai nata"

"Aunty kiyi hak'uri ki zauna zan fad'a miki koma mene "
Zama Aunty Aliya tayi kusa da Suhaima.

Kamar bazata yi magana ba tayi shiru sai mutsu mutsu take da baki, d'an kallonta Aliyah tayi tare da girgiza kai kawai wani lokacin Suhaima tana bata mamaki idan tana wasu abubuwan.

"Idan baza ki magana ba zan tafi ".
Cikin rawar murya kamar mai shirin fashewa da kuka tace
"Uhm... Uhm Aunty ni kaina na rasa mai yake damuna haka, cikin kwanaki biyun nan idan Sabeer yayi min magana ko muka had'u sai naji gabana yana fad'uwa, sannan kuma kawai d'azu dana ganshi da wata sai naji wani takaici wanda ya sanya ni kuka"

"Kin fara son Sabeer kenan ".
Waro ido waje tayi tare da dafe kirjinta da hannu kafin tace
"Taya na fara son Sabeer Aunty bayan ni kuma sam baya gabana? ".

"Ta yanda kika fara kishi dashi, Suhaima ina mai k'ara tunasar da ke da kada kiyi abin da zai sanya ki dana sani daga baya saboda na tabbatar idan kak'i Sabeer zaki zo kina nadama mara amfani don kafin ki samu wanda zai so ki kamar Sabeer zaki dad'e kina nema, kiyi amfani da damar ki Suhaima kafin ta kubce miki "

Tana gama fad'in haka ta tashi ta fita saboda kiran da Babaa Lantana tayi mata, ta bar Suhaima cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.

"Nayi amfani da dama ta kafin ta kubce min, me Aunty take nufi.....! "

Dafe kanta take wanda ya fara yi mata ciwo gaba d'aya ta rasa me ya kamata tayi shin zata bi shawarar Aunty Aliya ne ko kuwa zata bi abin da zuciyar ta yake kitsa mata na kada ta bari son Sabeer ya zauna mata cikin zuciya idan ba haka ba zatayi nadama don family d'in Sabeer baza su so ta ba a matsayin surukar su duba da wulak'ancin da tasha lokacin bikin Jiddah.

*_After two weeks_*

Acikin wannan satin ne bayan an sha sunan d'an Yaya Aliyu wanda aka sanya mishi sunan Baba Adamu, su Babaa Lantana sun so ya sanya sunan mahaifin shi Umaru amman Aliyu da Suhaima suka k'i aminta da hakan k'ememe don baza su ta6a mance abubuwan da mahaifin su ya aikata musu ba, Ameer Suhaima ta sanya yaron suna fad'a mishi saboda 6oye sunan shi da suka yi.

Zuwa wannan lokacin Sabeer ya dad'a ramewa sosai sakamakon tunani da ya sanyawa kanshi gashi yaja baya da al'amarin Suhaima da yana da ikon da zai cire sonta cikin zuciyar shi da yayi, duk wanda yasan Sabeer a baya yanzu ya ganshi sai ya tausaya mishi musamman akasan A SANADIN SO ya zama hakan gaba d'aya ya fita hanyar Suhaima tunda ko ya kulata ba wani sauraren shi take ba, sosai Aunty Aliya da Yaya Aliyu suke tausaya mishi don yayi alkawarin bazai yiwa Suhaima auren dole ba sai dai kawai taji ana d'aura auren ta da Sabeer sosai Aliyu yana bashi tausayi.

Ta 6angaren Suhaima ma duk ta wani rame saboda son Sabeer da kullum yake shiga cikin zuciyar ta yana nuk'urk'usa kowanne sashi na cikin zuciyarta, sai dai ta kasa bawa zuciyar ta aminta har takai da ta furtawa Sabeer cewa tana son shi zata aure shi sannan zata iya jure duk wani wulak'anci na family d'in shi zata jure shi indai Sabeer zai rik'e ta cikin mutunci bazai juya mata baya.

Da wannan tunanin take kwana take tashi tana jiran Sabeer ya k'ara furta mata kalmar so a time d'in take son sanar dashi ita ma ta kamu da son shi, a lokacin da take kok'arin fad'a mishi ta kamu da sonshi a lokacin kuma ya canja mata ko magana bata had'a su yanzu ya zatayi kenan.

Zaune take a d'aki tana wannan tunanin da ya zame mata kamar karatu don a kullum makamancin tunanin take yi, runtse ido tayi hawaye masu zafi suka samu sauka asaman face nata, zafi zuciyar take mata.

Zumbur ta mik'e tsaye da zaunen da take ta fito tsakar gida nan ta fara shara gyara gidan tsaf tayi sannan tayi wanke wanke da wanke toilet kafin ta wuce d'akin Aunty Aliyah ta gyara mata shi tsaf ta sanya turaren wuta, kallonta kawai Aunty Aliya take saboda ganin yanda take rama gashi kana kallon face nata zakasan tana d'auke da damuwa, har ta gama sanya turaren wuta ta fita daga d'akin tana kallonta ajiyar zuciya ta sauke tana mai taya Suhaima da addu'a Allah ya yaye mata abin da yake damunta.

Agurguje tayi wanka ta shirya cikin wasu kaya pakistan dogon wando white ne sai rigar da tsayinta wajen gwiwar ta ne itama farace rigar sai touch d'in flower's blue ajikin gaban rigar body spray ta fesa bayan ta shafa powder da man le6e, tayi kyau duk da ba wani make up tayi ba.

Hijab dogo mai hannu blue colour ta sanya sannan ta zura flat shoes akafanta white ta fito ko d'akin Aunty Aliya bata shiga ba ta fita, a k'ofar d'akin da Sabeer yake ta tsaya tana son shiga tana kuma tsoro gabanta sai fad'uwa yake, ta dad'e a haka kafin dakyar ta iya d'aga kafarta ta shiga d'akin sai dai kuma wayam babu kowa sai dai da alama bai dad'e da fita ba don ga kaya a zube a k'asa wanda ta ganshi ya sanya da safe.

Da sauri ta k'arasa shiga ta tattara d'akin ta gyara ta share shi tas sannan ta hango wani diary nashi akusa da pillow d'auka tayi ta fara karanta wa.

Tun da ta fara karantawa take kuka a hankali har takai da ta bud'e baki sosai tana kukan tausayin Sabeer daman ashe haka yake sonta, me yasa ta wulak'anta shi da tasan haka yake sonta da a lokacin da ya furta mata so ta amince dashi, me yasa bata tsaya ta fahimce shi ba ita wacce iri ce da bata tsaya tayi nazari akanshi ba.

"Wayyo Allah nah...! "
Fad'in Suhaima hawaye na zuba a idanunta.

"Allah sarki Sabeer ashe kai masoyina na gaskiya dole a yau ba gobe ba na bayyana maka zuciyata ta dad'e da kamuwa da son ka!, i luv U Sabeer with oll my heart! "

Tashi tayi tsaye bayan ta ajiye mishi diary d'in ta fita daga gidan gaba d'aya ma, a k'ofar gidan ta tsaya tana kalle kalle ta inda zata hango Sabeer, amman ko mai kama dashi bata hango ba sosai tayi mamaki don bai fiye yawo sosai ba sai dai idan Yaya Aliyu zai je wani wajen ya rakashi shima ba koyaushe ba sai abokin shi Ashiru da suke d'an fita amman basa nisa kuma basa dad'ewa sosai.

"To ina yaje!? "
Cewar Suhaima a fili ta furta hakan tana furzar da iskar bakinta, cikin sanyin jiki ta juya zata koma cikin gida kenan ta hango Ashiru, wata ajiyar zuciya ta sauke kafin ta k'arasa kusa dashi da sauri tace
"Ashiru don Allah ko kaga Sabeer? "

Da murmishi a fuskar shi yace
"Eh yana cikin gonar Yaya Aliyu a zaune yanzu na barshi acan na taho d'auko abu "
ajiyar heart Suhaima ta sauke tare da hamdala jikin zuciyar ta kafin tace
"Yawwa nagode Ashiru"

Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri zuwa cikin gonar Yaya Aliyu, yayin da Ashiru ya wuce cikin gida.

Tana k'arasa gonar ta fara dube duben inda yake ta d'an jima tana dubawa kafin ta hango shi kan wani dutse mai d'an girma a zaune, kallo d'aya zaka yi mishi ka fuskanci yana cikin damuwa.

Ta jima tana kallon shi hawaye na zuba a idanunta na tausayin Sabeer kasa k'arasa wa inda yake tayi kawai ta tsaya tana kallon shi, jikinshi ne ya bashi ana kallon shi yasa shi d'ago kanshi yana dubawa ya hango Suhaima a tsaye ta zuba mishi ido, d'an murmishi ya saki na yak'e kafin kuma lokaci d'aya ya zaro ido waje fuskarshi d'auke da tsantsar tashin hankali da k'arfi ya furta

"Suhaima! "
Bazato Suhaima taji ya kirawo sunanta fuskarta d'auke da murmushi itama ta furta
"Sabeer! "
Ganin batasan abin da ya hango ba ne bane yasa shi zabura ya mik'e da wani irin gudu da zafin nama ya k'arasa inda take tsaye bai yi wata wata ba ya ture ta gefe guda ta fad'i k'asa.

Arud'e ta d'ago kanta ta kalle shi inda kuma a daidai lokacin Sabeer ya saki wata k'ara da k'arfin gaske ya fad'i k'asa yana wani irin abu kafin kuma jikin shi ya sandare kamar matacce ya zama, cikin hargitsi Suhaima ta mik'e tsaye ta taho inda Sabeer yake kwance, sauran taku d'aya tayi ta k'arasa wajen ta hango abun da ya matuk'ar firgitata ya tsorata ta lokaci d'aya jikinta ya hau rawa na tsoro ko kwakkwaran motsi ta kasa balle ta nemi agaji.......

Uhm ga Sabeer a kwance kamar matacce ko mene ya same shi sai ku biyo ni don jin abin da ya faru, mu had'u a next page don jin yanda zata kasance, ku cigaba da hak'uri fan's.

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/28, 9:04 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.