Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 65 of 67

*PAGE 113*

Bayan sun yi wata biyu da en kwanaki ne Suhaima babu inda taje duk kuwa da nacin da Jiddah take akan Sabeer ya barta taje amman yak'i yarda sai dai ita tazo, duk wani gyara da ya kamata ayiwa wadda ta haihu Suhaima ta samu wannan gyaran daga 6angaren Aunty Aliyah, Jiddah da Babaa Lantana, tuni tayi er kiba kad'an ta murje tayi kyau abin ta duk da kuwa rainon biyu babu sauk'i amman Sabeer yana matuk'ar taimaka mata haka Aunty Aliyah da Babaa Lantana suna taya ta rainon su sosai.

Bayan ta gama yiwa Na'eem da Shaheed wanka ne da yake lokacin zafi ne ta sanya musu powder tare da kaya marasa nauyi gadon su taje ta kwantar dasu tare da yi musu addu'ar tsari ta bacci sannan ta wuce toilet tayi wanka, d'aure da towel ta fito d'an k'arami, had'a ido tayi da Sabeer wanda yake zaune kusa da gadon Na'eem da Shaheed yana lilasu a hankali murmishi suka sakarwa junan su cike da so, wani mayataccen kallo Sabeer yake bin ta dashi wanda tun safe ta kula da irin wannan kallon nashi, ita tsoron ma zuwa kusa dashi take hannun shi ya mik'a mata bata yi musu ba ta mik'a nata ya rik'e shi tare da janyo ta jikin shi ya fara shinshina wuyan ta zuwa bayan ta hura mata iskar bakin shi yayi cikin kunnen ta wanda ya haddasawa Suhaima kasala cikin muryar rad'a yace

"Baby nah ki bani wannan damar please ina son kasance wa dake nayi missing d'in ki da lot "

Duk da ta gane nufin shi amman da taji abin da yace sai da taji fad'uwar gaba amman ya zata yi tunda hakk'in shi ne wanda ya rataya kan wuyanta, don haka k'ara shigewa jikin shi tayi kawai tana cusa face nata a chest d'in shi.

"Bari naje nayi wanka koh? "
Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira, tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tarar da ita har ta shirya cikin wata gown ta bacci iyakar rabin cinyarta (da yake Sabeer ya sanya Jiddah d'ebo mata kayan ta ba tare da wani ya gane ba) ta gyara gashin ta sai tashin kamshi take, kallonta yake kamar yau ya fara ganin ta.

Agurguje ya shirya ya taho wajen ta ya rungume ta cikin jikin shi yana faman aika mata da zafafan sak'onnin shi cikin wani irin salo mai wuyar fassara, wannan daren sun raya shi sosai cikin wani irin kaunar junan su anan Sabeer ya gama tabbatar wa Suhaima itace rayuwar shi haka ita ma a 6angaren ta gwarzon nata shine jin dad'in rayuwar ta suna addu'a da fatan Allah ya barsu har karshen rayuwar su.

Rayuwar su suke cike da jin dad'i da kwanciyar hankali suna kula da yaran su sosai da haka har Na'eem da Shaheed suka tasamma shekara d'aya yaran sunyi wani irin girma gashi suna wata goma suka iya tafiya gudun su suke ko'ina zuwa lokacin Aunty Aliyah tana d'auke da tsohon ciki itama, zumunci Jiddah da Suhaima kuwa kullum k'aruwa yake idan bata zo ba to za suyi waya junan su, tsakanin Suhaima da Sabeer kuwa kullum soyayyar su k'ara k'arfi take kula suke bawa junan su sosai, Daddy kuwa a weekend yake zuwa ganin jikokin shi.

Suna watanni goma sha bakwai Suhaima ta yaye su, yayin da Aunty Aliyah kuma ta haihu aka samu mace sunan Umman su Suhaima aka sanya mata wato Fatima suna kiran ta da Ameerah, Yah Aliyu ma karatun shi ya d'auki zafi yana daf da had'a degree d'in shi a Buk.

Wani zuwa weekend da Daddy yayi yace yana son Na'eem da Shaheed su bishi suyi mishi kwana 2 sunyi matuk'ar shak'uwa da Daddy sosai, a tsorace Sabeer ya barwa Daddy yaran shi don yana jin tsoron kada Mumy ta kashe musu yara, tsaf Daddy ya karance shi girgiza kai kawai yayi yana murmishi bai ga laifin shi ba yana da gaskiyar shi baisan yanzu yanda Mumy ta koma ba ne duk wannan ji da kan babu shi.

**********

Duk wani jin dad'i gashi nan akwai shi sai dai babu kwanciyar hankali, duk tayi bak'i ta rame Dr Faridah kenan wato Mumy abin duniya yayi mata yawa wajen shekara 2 bata sanya tilon d'anta a idon ba tayi neman tayi binciken duk a banza tayi kok'arin tambayar Daddy akan inda d'anta yake but yace shima neman shi yake k'arshe ma rufe ta da fad'a yayi ai duk laifin ta ne gashi ta salwantar mishi da rayuwar d'an shi ba'a san inda yake ba.

Ta 6angaren Dr Ahmad d'an fillo dasu Hajjah Hauwaa suma suna cikin wannan tsantsar tashin hankalin na rasa sanin inda Sabeer sunyi binciken iyakar iyawar su amman basu ji d'uriyar inda yake amman Dr Ahmad d'an fillo yaso d'ago Daddy yasan inda Sabeer yake ganin yanda hankalin shi yake kwance bai d'aga hankalin shi sosai ba akan 6atan Sabeer amman sai Daddy ya nuna mishi ba haka, tun daga lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya kwanta rashin lafiya saboda 6atan Sabeer d'an lelen shi yayi kuka sosai yana mai nadamar da tun lokacin yayi magana matar shi ta dawo gare shi tun da dalilin ta suka neme shi suka rasa, Haka ma Mumy ta kwanta ciwo a tsaitsaye ko hospital bata iya zuwa jinin ta hau sosai damuwa biyu ce ta had'e mata rashin tilon d'anta da kuma juya mata baya da mijinta yayi duk a dalilin Suhaima, wadda zuwa wannan lokacin tayi nadamar abin da ta aikata yafi sau ba adadi tayi kukan sosai da bata aikata hakan ba da tuni d'anta na kusa da ita har da jikokin ta ma, har tana fatan ta d'an samu sauk'i ta nemi garin su Suhaima taje ta nemi yafiyar ta ko zata samu sassauci cikin zuciyar ta da rayuwarta gaba d'aya.

Tun safe yau jikin ta ya rikice ga Daddy baya nan yafita tana kwance a falo wajen 4 na yamma ne jefi jefi tana kallon tv tana kallon African Tv suna wa'azi na marigayi sheik Ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya jik'an shi da rahma Amin), lokaci zuwa lokaci gaban ta na fad'uwa.

Sallama Daddy yayi ya shigo palourn hannun shi rik'e da Na'eem da Shaheed suna d'an tsalle tsallen su, wata zabura Mumy tayi ganin wasu kyawawan yara masu matuk'ar kama da junan su kuma abin da ya k'ara hargitsa ta ganin yanda suke matuk'ar kama da Daddy da kuma Sabeer, nan take wani tunani ya d'arsu cikin zuciyar ta ko Daddy aure ya sake bata sani ba matar ta haifa mishi yara.

Da d'an gudun su suka k'arasa inda take tare da rungume mata k'afafun ta, sakin baki kawa tayi tana kallon su wani irin sanyi taji jikinta yayi ta zame ta zauna lokaci d'aya wani mugun son yaran ya ratsa mata cikin zuciyar ta da zuciya d'aya ta d'ago su zuwa jikin ta cikin murmishi take cewa

"Ya sunan ku yara nah?"

Na'eem da yafi surutu cikin muryar shi wadda bata kware ba yace
"Ni sunan Na'eym wannan kuma Sha'eed"

Ya k'arasa fad'i yana Shaheed da d'an yatsan shi,
"Masha Allah sunan masu dad'i Allah ya albarkaci rayuwar ku "

"Amin "
Daddy ya amsa cikin zuciyar shi, d'agowa tayi ta kalli Daddy tare da cewa
"Daddy yaushe ka sami yara masu kama da kai bansani ba? "
Murmishi yayi yana tafiya Stairs yana cewa
"Bana wa bane aron su aka bani na kwana 2 "

Cikin d'okin murya tace
"Da gaske kake Daddy?"

"Ban ta6a yi miki wannan wasan ba gaskiyar kenan "

Washe baki tayi duk yanda jikinta babu dad'i amma sai taji lokaci d'aya kamar an cire mata ciwon cikin farinciki take cewa
"Nagode Thank U very much Daddy naji dad'in ganin yaran ji nake kamar my Son nake gani Allah ya biyaka "

Ta k'arasa maganar hawaye na fita daga eyes nata sosai Daddy yaji wani mugun tausayin ta lokaci yayi da Dr Faridah ya kamata tasan ainahin inda d'anta yake yana gama wannan tunanin ya wuce stairs da sauri.

Dad'i ya ishe Mumy ta rasa inda zata sanya yaran duk wasu kayan kwad'ayi na yara haka ta cika musu gaban su dashi, koya ta kalli yaran wani sonsu ne yake sake ratsa zuciyar ta ji take tamkar da Sabeer take tare lallai idan tasan iyayen yaran nan dole ta k'ulla zumunci dasu kodan suna zuwan mata, a baki ta dunga basu abinci bayan sun gama ci ne ta shiga bedroom d'in Daddy tana tambayar shi kayan yaran ce mata yayi bai taho musu dashi ba.
"Don Allah ka barni muje wani mall d'in sai na siyo musu kayan har da na wasa kada kace a'a please dear "

Murmishi yayi sannan yace
"Okay, amma ke da baki da lafiya zaki fita? "
"Zan iya wallahi "
Ta fad'i hakan tana yin gaba da sauri kamar wata yarinya da kallo Daddy ya bita dashi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana cewa
"Ina son ki Faridah naji dad'in yanda kika daina daukan kanki kamar kin fi kowa "

Cikin farinciki ta shirya agurguje ta fito car key kawai ta d'auka tare da rik'o hannun su suka fito zuwa compound na gidan shigar dasu tayi ta zaunar dasu sannan ta rufe k'ofar, sit na drive ta zauna da kanta tayi motar key cikin kwarewa take driving d'in ta tana jin wani nishad'i cikin zuciyar ta.

Bayan sun shiga wajen kayayyakin wasan yara nan ta sake su aikuwa da gudu suka tafi wajen kowanne na d'aukan abin da yake so, sosai ta kashe kud'i wajen siya musu kayan wasa, sannan ta siya musu kayan sawa masu kyau da tsada 6angaren kayan ciye ciye ma haka ta siya musu duk abin da suke so sannan daga k'arshe suka taho gida, idan kaga Na'eem da Shaheed tare da Mumy bazaka d'auka jikokin ta bane zaka fi zaton yaran ta ne wanda ta haifa...........

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[5/8, 5:07 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ

ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ

♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.