A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 67
PAGE 28-29
Tun daga lokacin ya kasance Aunty Aliyah bata da ishashshiyar lafiya a jikin ta yau lafiya gobe ciwo, duk ta rame sosai saboda laulayin da ya sanya ta a gaba, aiyukan gidan kuwa Suhaima ce mai yin su don Aliyah bata iya komai sai kwanciya saboda rashin k'arfin jikin ta dakyar take iya tashi zaune, ga baccin da take sosai abinci ma ba kowanne take iya ci ba ba k'aramin walaha take sha ba.
Da haka aka cinye kwanaki biyar Aunty Aliyah tana fama da azababben laulayi, ya rage sauran kwanaki biyu a fara bikin Jiddah kuma ayau ne ranar da Jiddah ta fad'a zata zo ta dauk'i Suhaima su tafi gidan su don fara hidimar biki, gashi Aunty Aliyah ba lafiya Suhaima ma ta fitar da ran zuwa bikin Jiddah saboda ganin yanda jikin Aunty Aliyah yak'i sauk'i duk hidiman gidan ita kad'ai ce mai yi don ma wani lokacin Babaa Lantana na zuwa taya ta 'yan ayyuka.
Wajen k'arfe biyun ranar laraba Jiddah ta zo lokacin Suhaima ta kammala girkin rana tana share gidan taji da sallamar ta aikuwa yar da tsintsiyar hannun tayi da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su cikim tsananin jin dad'i.
"Amarya kinsha k'amshi sai wani kyalli kike tun kafin a fara jin amarcin "
Cewar Suhaima cikin murya k'asa k'asa tana dariya, dukan wasa Jiddah ta kawo hannu zata yi mata da sauri Suhaima ta goce suna dariya.
"Allah Suhaima kin fara zama mara kunya, zan fad'a wa Yaya Aliyu yayi miki aure ke ma "
Rik'e bakin ta Suhaima tayi da hannun ta d'aya kafin tace
"Wooh rufa min asiri ni har yanzu yarinya ce da saura "
Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa
"Uhm a hakan kike yarinya ai kuwa ki zuba ido ina aure zan ziga Yaya Aliyu yayi miki ke ma nace ke kika fad'a min na fad'a mishi aure kike so kina jin kunyar sanar dashi shi yasa kika aiko ni "
Jiddah ta k'arasa magana tana dariyar mugunta, kwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Wayyo Allah nah Jiddah ki rufa min asiri, waiii idan Yaya yaji hakan ina tunanin 6a66ala ni zai yi "
"6a66alawar lafiya, ai ba wani mugun abu kika yi "
"Besty albishirin? "
"Goro fari tas mai ya faru k'awata? "
"Aunty Aliyah tana da ciki taawon 3 month's "
Wani uban tsallen murna Jiddah ta doka tare da rungume Suhaima tana cewa
"Da gaske kike Suhaima don Allah? "
Cikin tabbatar wa Suhaima tace
"Da gaske ne wlh Jiddah, sai dai yana bata wahala baki ga yanda ta koma ba duk ta rame ko abincin kirki bata iya ci "
Suhaima ta k'arasa maganar cikin yanayim damuwa, nan take Jiddah ita ma fuskarta ta koma kalar damuwa, hannun Suhaima ta rik'o suka nufi d'akin Aunty Aliyah tana cewa
"Kada ki damu Suhaima Aunty Aliyah zata samu lafiya, kinsan wani cikin yana bawa mace wahala sosai kafin ya girma, da zarar ya girma insha Allah zata samu sauk'i addu'a zamu cigaba da yi mata "
Gid'a kai Suhaima tayi kawai a lokacin suka k'araso kofar d'akin Aunty Aliyah sallama suka yi mata, dakyar ta iya amsa musu sallamr k'asa k'asa cikin irin sanyin muryar mara lafiyar nan wanda yake jin jiki sosai, d'aga labulen d'akin suka yi tare da shiga ciki tana kwance a falo saman sallaya da hijab a jikin ta alamar yanzu ta idar da sallahr azahar.
Zama suka yi kusa da ita sosai Jiddah hankalin ta ya tashi ganin yanda Aunty Aliyah ta koma wata iri duk ta rame sosai ta fita a hayyacin ta tamkar ba ita ba.
"Sannu Aunty Aliyah Allah ya baki lafiya "
Cewar Jiddah kenan, murmishin yak'e Aunty Aliyah tayi tare da cewa
"Yawwa Jiddah, Amin "
Dakyar take maganar tana jan numfashi irin wanda yake idan mutum yana jin ciwo sosai idan yayi magana yake yi.
"An kaita hospital kuwa Suhaima? "
Jiddah ta tambayi Suhaima tana kallon ta.
"Eh Yaya ya kaita amman magani suka bata "
"Wanne hospital ne wannan da ko drip baza su sanya mata, jiki babu kwari ga ba cin abinci, yanzu da sun sanya mata drip zata ji k'arfin jikin ta "
Tana gama fad'in haka ta ciro wayar ta dialing d'in digit na Yaya Aliyu tayi bayan sun gaisa ta fad'a mishi tazo tana son ganin shi, babu dad'e wa sai ga Yaya Aliyu ya shigo bayan sun dad'a gaisawa ne tace
"Yaya Aliyu don Allah ina son kayi min alfarma mu kai Aunty Aliyah hospital d'in da muke zuwa, ba don na raina kulawar da kake bata ina son zan kaita inda zasu duba ta sosai "
Girgiza kai Yaya Aliyu yayi tare da cewa
"Baza'a yi haka ba Jiddah wahalar zata yi yawa, ki fad'a min sunan hospital d'in gobe zan kaita da kaina a duba ta "
"Don Allah Yaya ka daure mu je na roke ka "
Nan Jiddah tayi ta rok'an shi dakyar daga k'arshe ya amince don har Jiddah ta fitar da ran zai barsu, nan da nan suka shirya tafiya hospital a motar da Jiddah tazo, Yaya Aliyu da driver a gaba Jiddah, Suhaima da Aunty Aliyah a baya su bayan sun yiwa Babaa Lantana sallama, sai addu'ar fatan alkhairi Babaa Lantana take yiwa Jiddah.
Wani had'add'en private hospital wanda Jiddah da families d'in ta suke zuwa nan ta sanya driver ya kaisu, babu 6ata lokaci aka kar6i Aunty Aliyah saboda sunsan wace Jiddah, nan aka shigar da Aunty Aliyah special room ita d'aya sai doctor da kuma nurse guda biyu.
Sun d'auki tsawon lokacin suna checking nata kafin daga k'arshe su sanya mata drip tare da yi mata injection na bacci kafin su fito a room bacci mai nauyi ya d'auke ta.
Bayan sun fito ne likita ya buk'aci ganin su cikin office d'in sa bayan sun shiga sun zauna ne, sai da yayi rubutu cikin file sannan ya fara cewa
"Ciki ne da ita na tsayin 3 months so kunsan kowacce mace da irin halittar ta na laulayi ciki kafin yayi kwari, shine yake bata wahala baya ga wannan babu wani abu babba sai malaria, zamu yi iya kok'arin mu na ganin koda cikin kashi biyar ne ta samu saukin kashi uku sauran kuwa sai a hankali don haka mun bata gado zamu rik'e ta har zuwa gobe insh Allah "
"Okaya doctor thank U very much, yanzu zamu iya ganin ta?
"Why not sai dai ban da hayaniya please and kuma ga maganin da za'a yi amfani dashi na rubuta ana buk'atar shi da wuri don tana tashi zata sha "
"Okay doctor ba damuwa"
Nan doctor ya bawa Aliyu suka yi musabiha tare da cewa
"Allah ya bata lafiya ya kuma raba su lafiya congrats Yalla6ai "
"Amin nagode likita "
Sam doctor yayi tuanin cousins d'in Jiddah ne ganin su suma kyawawa dasu tamkar family d'in su Jiddah shi yasa bai kawo komai a ranshi ba, sai dai yanayin su da ya nuna basu da kud'i kamar su Jiddah.
Bayan sun shiga room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah ne suka zauna shiru kowa da nashi tunani ta 6angaren Aliyu yana tunanin da kunya ya iya kallon idon Jiddah yace bazai bar Suhaima ta tafi bikin ta ba ganin irin d'umbin hallacin da tayi musu bai kamata ya hana Suhaima zuwa ba, gashi kuma Aliyah na buk'atar kulawa sosai gashi idan suka koma gida gobe Suhaima ce k'arfin ayyukan gidan idan ya barta ta tafi ya zasu yi?...
Kuyi hak'uri da wannan fan's sai gobe kuma insha Allah.
Aishat A Muh'd ðŸÂŒðŸÂ»â€Â♀
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœÂðŸÂ»: 💠A SANADIN SON KI ðŸ’Â
Written by
Aishat A Muh'd
â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
This page is for U my Ramlat ar manga (Real mai dambu 🥗) thanks for luv nd everything Allah ya bar zumunci ya raya zuri'a, ina matukar alfahari dake wannan shafin naki ne kyauta 👄
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.