Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 31 of 67

PAGE 57-58

Ta dad'e kwance a hakan don batasan iyakacin lokacin da ta d'auka ba jin dawowar su Yaya Aliyu taji daga hospital, nan ta tashi da sauri tana zira kaya tana mai mamakin dad'ewar da tayi don ma ta gama dukka ayyukanta, wani siket ta sanya pink colour mai turuwa sai T-shirt in black colour mai k'aramin hannu tana da tattara daga gaban rigar sai ta gyara gashin kanta tayi rolling da pink d'in veil kalar siket d'in batayi wani make-up ba daga powder da ta sanya sai lips gloss mai kamshin apple tayi kyau sosai duk da batayi kwalliya ba.

Nan ta fito tsakar gidan babu kowa d'akin Aliyah ta wuce sai ta tarar da Babaa Lantana da Aliyu sai Sabeer a palour babyn na hannun Sabeer yana faman kallon shi addu'a yake cikin zuciyar shi Allah ya nuna mishi auren shi da Suhaima ta haifa mishi kyakkyawan babyn yanda yake shi d'aya yana rok'an Allah yasa ya haifi yara da yawa don bazai sassautawa Suhaima ba duk shekara yake son tana haifa mishi baby shi zaina yin zaman rainon su.

Yana cikin wannan tunanin yaji sassanyar kamshin turaren ta sai da ya lumshe ido kafin ya bud'e su ya sauke su saman beautiful face d'in Suhaima sai akayi dace ita ma ta d'ago idanunta ta kalleshi nan suka fara kallon junan su, dakyar Suhaima ta iya controlling d'in kanta ta janye idanunta ta wuce ta samu ta zauna kusa da Aunty Aliyah, shima Sabeer d'auke idon nashi yayi yana wani shan kamshi ji yake tamkar ya lasheta don tayi mishi kyau.

Duk wannan kallon da suke yiwa junan su Aliyah da Aliyu suna kallon su suna kyautata zaton Suhaima an fad'a tarkon Sabeer, wayar shi ya d'auko ya d'auki babyn pic's yana d'an yin hira da Babaa Lantana wadda yake zaune kusa da ita, sun jima a zaune a haka Suhaima tana son d'aukan babyn don bata ganshi ba gashi Sabeer yak'i ajiye shi gajiya tayi don haka cikin muryar shagwa6a tace

"Wai ni Aunty Aliya baza'a ban na d'auki babyn ba ni fah tun da aka haife shi ban d'auke shi ba sosai "

Rik'e ha6a Aliyah tayi tare da cewa
"Ni zan hana ki d'auka ne ai gashi hannun mutumin na ki sai kije ki kar6a "

D'an jim tayi kamar bazata je ba sai kuma ta kasa jurewa don haka sai ta mik'e a nutse ta nufi inda Sabeer yake zaune, kamar an tsikare shi ya mik'e tsaye da sauri ya mik'awa Babaa Lantana babyn tare da cewa
"Nayi mantuwa Babaa rik'e minshi ina zuwa "
Yana mik'a mata ya fice da sauri har yana mance wayar shi, baki sake Suhaima take bin shi da kallo tabbas akwai wani abin d'an ta6e bakinta tayi ko maye ruwanta ma, kar6ar babyn tayi ta rungume shi a jikinta k'aunar shi na ratsa cikin zuciyar ta.

Wayar Sabeer ce take k'ara kira na biyu kenan da ake yi mishi gashi tun da ya fita bai dawo ba.

"Suhaima ajiye babyn ki kai mishi wayar tunda bai dawo ba "
Cewar Yaya Aliyu, Babaa Lantana ta mik'awa babyn ta mik'e tare da d'aukar phone d'in nashi ta fita daga parlorn, kallon phone d'in take sosai tayi mata kyau da gani mai tsada ce sosai bana kad'an ba.

Bata ganshi a tsakar gida ba don haka tayi sallama d'akin shi sau uku ba'a amsa ba, sai kawai ta tura kanta cikin d'akin wayam bata ga Sabeer, abin ya d'aure mata kai ina ya shiga ne.

Fitowa tayi ta duba don ta duba kofar gida tana lek'awa ta hango abin da ya kusan sumar da ita saboda tsanannin tashin hankali, tuni jikinta ya hau rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi nan da nan idanun ta suka rikid'a daga farare sol zuwa ja, ba komai ta hango ba sai Sabeer da yake zaune saman wani d'an reshen bishiya da ya karye ya fad'o k'asa sai ake zama a kanshi sai wata budurwa wadda bata gane fuskarta ba tasha uwar d'amara a kugunta a tsaye gaban Sabeer suna dariya hankalin su kwance ita kuma tana wani jan mayafi tana rufe fuskarta tamkar mai jin kunya.

Shi kuma yana mata magana, tuni Suhaima taji wani mugun kishi ya tokareta wanda batasan tana da irin kishin nan ba, batasan lokacin da ta k'arasa inda suke ba ta tsaya ranta a mugun 6ace.

Tun tahowar ta Sabeer ya hango ta yana kallonta ta gefen idon shi ganin yanda fuskarta ta koma yasa shi narke murya yana dad'a jan budurwar da hira wadda kasance k'anwa ce ga Ashiru.

Ganin ta d'auki tsayin seconds a tsaye babu wanda ya kulata yasa taja wani mugun tsaki tamkar zata tsinke harshenta, da sauri suka jiyo suka kalleta.

"Laaa Suhaima ashe kece "
Cewar budurwar yarinyar tana washe baki, wata harara ta gallawa buduwar wanda batasan ta iyata ba, sauran kad'an dariya ta kubcewa Sabeer ganin abin da tayi.

D'an wani tunani Suhaima tayi sai kawai ta k'ak'alo yak'en dole tace
"Eh ni ce Sadiya ya kike? "
Tana washe hakora tace
"Lahiya lau wallahi yanzu tahowar da zanyi gidan ku zan shigo ganin jaririn Aunty Aliya sai wannan d'an binni ya tsayar da ni "

"Hmmm "
Abin da Suhaima ta fad'a kenan, sannan ta mayar da hankalin ta kan Sabeer ta mik'a mishi wayar shi ba tare da sun had'a ido ba tace
"Kiran ka akai "
Bata bari ma ya kar6a ba ta sakar mishi ita Allah ya sanya yayi saurin cafewa ba don haka ba da ta kwankwatse sai kawai ya bita da kallo har ta wuce cikin gida kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mik'e shima ba tare da ya kula Sadiya ba ya wuce cikin gidan d'akin shi ya shiga ya rufe k'ofa tare da kwanciya saman katifa yana son fassara abin da yake kan fuskar Suhaima amman ya kasa tantacewa nan ya fara juyi kawai.

Suhaima kuwa tana shiga gidan ta wuce zuwa cikin d'akin ta idanun ta sun rufe da wani irin abu da ta tabbatar da ba komai ba ne sai kishin Sabeer, fad'a wa tayi kan gadon ta tare da fashewa da wani irin kuka, tasan idan ka fara son mutum dole kayi kishin sa kenan ya ita ta fara son Sabeer tunda gashi daga nin shi da wata batasan dalilin tsayuwarta ba ta ji wani abu ya tokare mata wanda tasan ba komai ba ne sai kishin Sabeer!......

_ku cigaba da hak'uri fan's da ni, ga wannan ku yi manage da shi please_

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/28, 5:42 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.