A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 55 of 67
*PAGE 102-103*
Afusace Yah Aliyu cakumi wuyan Sabeer ya matse da k'arfi idanun shi tuni suka yi ja ya fara wani irin tari, cikin fusata yake cewa
'Me kazo yi kuma, bayan ka koreta daga gidan ka ina fatan takardar sakin ta ka kawo min don k'anwata bazata ta6a komawa gidan ka ba? "
Dakyar Sabeer yake jan numfashi don ba k'aramin shak'a Aliyu yayi mishi ba, cikin murya k'asa k'asa yake cewa
"Nazo ne domin na baku hak'uri akan abin da ya faru na kuma dawo da Suhaima gidana "
Dad'a shak'e shi Aliyu yayi kan yace
"Kaiii asuwa da har zaka sanya Suhaima dawowa gidan ka, k'anwata ta barka har abada bakai ba ita "
Sabeer na kok'arin magana Yah Aliyu yaja shi tare da watsa shi waje ya mayar da k'ofar ya rufe har da sanya sakata, kallon su Suhaima da Aliyah yayi ganin yanda suke kuka sosai hararar ya maka musu kan ya wuce d'aki yana huci.
Suhaima ma da gudu ta shige d'akinta tana kuka da ta rasa na mene, yayin da Aunty Aliyah ta tafi wajen Aliyu ko zata rarrashe shi yayi hak'uri amman tana fara magana da ya buga mata wata tsawa batasan lokacin da ta tsallake Ameer ta wuce d'akin Suhaima da gudu ba, wanda har taso sanya Aliyu dariya amman ya matse dariyar.
Afirgice Suhaima ta juyo jin an shigo d'akin ta da gudu ganin Aunty Aliyah ce ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tana goge hawayen fuskar ta tace
"Aunty lafiya kuwa "
Zama tayi kan tace
"Hummm Suhaima Yayan nan naki ya d'auka da zafi sosai wallahi don zuwa nayi na bashi hak'uri amman wata tsawa da kwantsama min bansan sanda na sanya gudu ba, ina tausayin Sabeer nasan ba laifin shi ba ne laifin shi d'aya da yace ki bar mishi gidan shi "
Suhaima bata ce komai ba kawai sai ta zame ta kwanta tare da d'ora kanta saman k'afar Aliyah zuciyar ta a cunkushe take sam ta rasa abin da yake damunta.
Sabeer kuwa tun lokacin da Yah Aliyu ya watsa shi waje kasa tashi yayi awajen kawai ya zauna tare da janyo bag d'in shi ya d'ora saman k'afar shi ya fad'a kogin tunanin yanda zai shawo kan wannan matsalar, gaba d'aya wuyan shi ya rik'e ko iya juyashi sosai baya yi sabida shak'ar da yasha a hannun Aliyu, wai shi Sabeer shine aka watso shi waje kamar shi da kud'in shi da gatan shi amman duk A SANADIN SO komai na rayuwar shi ya canja.
Yana nan zaune aka yi kiran sallahr mangarib yana kok'arin tashi ya tafi masallaci ko zai samu ruwan alwala yaji an bud'e k'ofar an fito, sai da gaban Sabeer ya fad'i ganin yanda Aliyu ya tamk'e fuska tamkar bai ta6a dariya ba.
Kallon Sabeer yake cikin mamaki kafin yace
"Wai kai wanne irin mutum ne nace kabar min gidana bama buk'atar ba ana dole ne k'anwata ta tsane ka bata sonka ina son kawai ka rubuta mata saki ka bata tun muna mu biyu da kai kaji na fad'a maka "
Yana gama fad'in haka yaja tsaki tare da wuce wa, wani bak'inciki ne ya lullu6e Sabeer ganin wanda a girme bazai girme shi ba yake fad'a mishi magana son ranshi, da zai iya cire son Suhaima ya ajiye shi gefe da yayi don kawai samun sauk'in halin da yake ciki da me zai ji abubuwa gaba d'aya sun hargitse mishi ya rasa samu mafita.
Dakyar ya lalla6a yaje masallaci can ya samu ruwa yayi alwala tare da bin jam'in sallahr mangarib bayan an idar ne yana zaune a masallacin yana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Aliyu ya kyale mishi Suhaima kada ya rabasu, har aka kira sallahr ishsha bayan an idar da sallahr ne kowa ya watse sai shi kadai ya rasa wajen zuwa.
Yana nan zaune har wurin 9 na dare ga wasu sauro da suke kai mishi cafka ga zafi da duhu dulum a wajen ga wata azababbiyar yunwa da take k'ulle mishi ciki, kamar a mafarki yaji ana kiran shi cikin mamaki da sauri ya tashi ya fito daga cikin masallacin.
Baba Adamu ya gani tsaye da torchlight a hannun shi, tsugunnawa Sabeer yayi ya gaida shi amsa wa yayi kan ya kama hannun Sabeer suka doshi gidan Aliyu.
Atsakar gidan ya tarar da Aliyu, Suhaima, Aliyah, Babaa Lantana suna zaune ran Aliyu a 6ace yake don sosai Aliyah ta shammace shi taje ta fad'a wa su Baba Adamu halin da ake ciki sai aika mata da harara yake yi saboda yaso ya kar6i takardar sakin Suhaima ya fatattaki Sabeer kafin su ankara, sai gashi Aliyah ta shammace shi.
Zama Sabeer yayi gefen Baba Adamu sanann ya fara magana akan rashin kyautawar da Sabeer yayi na tsayawa yayi bincike kafin ya kori Suhaima, sanann ya d'ora da yiwa Aliyu nasiha tunda ya gane gaskiya bai kuma kyauta da abin da yayi ba har yazo domin ya nemi afuwar su ya kamata ya hakura kowanne d'an adam bai cika goma ba.
"Baba ni kawai ya bata takardar ta kawai yayi tafiyar shi Suhaima bazata koma gidan shi ba"
"Baza'a yi haka ba Aliyu a tambayi Suhaima tana son komawa tunda ya gane laifin shi har ya bada hak'uri kamata yayi ayi mishi afuwa "
Kallon ta Baba Adamu yayi kan yace
"Suhaima ina son ki fad'a min tsakani da Allah kina son komawa gidan Sabeer? "
Da sauri ta d'ago kanta ta kalli Baba Adamu kafin ta mayar da kallonta kan Sabeer gaba d'aya ya wani marairaice fuskar shi ta koma kalar tausayi sosai yana rok'an ta da tayi hak'uri ta amince, d'auke idonta tayi akan shi ta mayar dashi kan Yah Aliyu sai taga yanda ya wani had'e fuska gashi ya tsattsare ta da ido, ta rasa yanda zata yi zata bi bayan Sabeer ko zata bi bayan Yayan ta idan bata mance ba Yayan ta shine uwa ubanta don bata da wanda ya fishi duk duniyar nan, idan matsala ta sameta shi zata tunkara taya zata dubi tsabar idon shi ta za6i miji wanda bashi da tabbas.
"Kin shiru ke muke jira Suhaima "
Cewar Babaa Lantana kenan.
Kasa magana kawai tayi ta fashe da kuka sosai don batasan wanda zata bi bayan shi ba da gudu ta shige d'aki tare da sanya key.
Wata ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yayin da Sabeer kanshi yake sunkuye wasu hawaye na zuba daga cikin su duk shi yajawa kanshi yayi wasa da damar shi gashi komai ya rikice mishi, tsugunnawa yayi tare da cewa
"Ina rok'an ka Aliyu ka taimaka min kayi hak'uri akan abin da nayi wa Suhaima wallahi nayi nadamar korar ta da nayi bazan sake maimaita hakan ba insha Allah kuma zan sanya ido sosai tare da d'aukan mataki ga duk wanda yake kok'arin cutar min da ita "
Tsaki Aliyu ya saki tare da d'auke kanshi yana cewa
"Tun da Suhaima tak'i amincewa sai ka tashi ka koma inda ka fito "
"Babu inda zanje har ina nan har sai lokacin da Suhaima ta yafe min ta amince zata koma gidana "
Ta6e baki Aliyu yayi kan yace
"Ba dai agidan nan ba kuwa "
"Bashi da inda ya wuce nan Aliyu dole ya zauna tare da ku "
Cewar Baba Adamu yayin da Aliyu yace
"Baba ni bani da wani d'akin kwana anan gidan "
"Ga d'akin matar shi nan "
Fad'in Babaa Lantana kenan da duk tausayin Sabeer ya lullu6e ta.
"Babaa kiyi hak'uri amman gaskiya ban amince mishi da ya kwana anan d'akin ba "
Duk yanda yaso su Baba Adamu su taushi Aliyu yak'i basu had'in kai har sai da ran su Baba Adamu da Babaa Lantana ya 6aci sosai kafin dakyar ya amince da sai dai ya kwana a zauren gidan.
"Kana ji Sabeer zaka iya kwana a zauren gidan? "
Da sauri Sabeer yace
"Eh Baba zan kwana nagode sosai Allah ya k'ara girma "
"Amin Sabeer ba komai, yanzu Aliyah tashi ki zuba mishi abinci yaci "
Aunty Aliyah da tunda aka zauna bata tsoma baki ba ta tashi ta nufi kitchen tana zuba mishi abinci, bayan ta zuba ta kawo mishi gaban shi ta ajiye tare da kawo mishi ruwa mai sanyi na randa ta ajiye mishi.
Saboda yunwar taci ta cinye shi kad'an ya iyacin abincin yasha ruwa, zama yayi kawai tare da zabga tagumi abin duniya yayi mishi yawa, bayan su Baba Adamu sun gama ta6a hirar su ne suka yi sallama suka tafi nasu gidan.
Tashi Sabeer yayi ya koma zaure saman wani dutse ya zauna wanda ake tokare k'ofa dashi duk kayan jikin shi sunyi squeezing gashi sunyi datti wanka yake son yi sai dai babu fuskar hakan, had'e kai da gwiwa kawai yayi ga wani zafi, kukan sauro da cizon shi da suka addabi Sabeer dashi.
Yah Aliyu ne ya shigo gidan ya dawo daga rakiyar su Baba Adamu kenan, rufe k'ofar gidan yayi sannan ya wuce cikin gidan ko kallon inda Sabeer yake bai yi ba.
Sabeer na zaune anan yaji motsi d'ago kanshi yayi suka had'a ido da Aliyah saboda akwai hasken farin wata, tabarma ta mik'a da pillow tace
"Gashi nan Sabeer kayi hak'uri "
Girgiza kanshi yayi kan yace
"Auntyn mu nine da baku hak'uri don ku nayiwa laifi, nagode da kulawar ki agare ni ina rok'an ki da ki cigaba da bawa Suhaima hak'uri har ta huce "
Girgiza kanta tayi cikin tsananin tausayin shi don kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana tattare da damuwa sosai, kar6ar tabarmar yayi da pillown yayin da Aunty Aliyah tace
"Insha Allah zanyi kok'arin daidaita ka da Suhaima da Yayanta "
Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri don fakar idon Aliyu tayi ta fito ta kawowa Sabeer tabarmar, kallon ta yake irin kallon tuhumar nan d'an 6ata fuska itama tayi kan tace
"Lafiya kake kallo na haka kamar wadda tayi mata sata? "
D'an girgiza kanshi kawai yayi baice komai ba ya kwanta, ajiyar zuciya Aliyah ta saki ganin bai fahimci inda taje ba, kwanciya ita ma tayi gefen shi tana tunanin yands zata 6ullo wajen ganin Aliyu ya sassautawa Sabeer............
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»
[4/18, 8:32 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
â™» *єχ¢ℓυѕινє ωÑιтєÑ'Ñ• fσÑυм*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.