A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 59 of 67
*PAGE 106-107*
Kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su tare da wata irin zazzafar kauna, sun d'auki wajen 5 minute suna aikawa da junan su kallo yayin da Sabeer ya kasa jure kallon da suke aikawa junan su ya fara matsar da fuskar shi saitin fuskar ta da niyyar yayi kissing d'in cute pink lips nata wanda yayi tsananin missing d'in su a lot.
Jin saukar numfashin shi kusa da hancin ta sosai ya sanya Suhaima dawowa cikin hayyacin ta ta daddage ta fiske jikin ta daga jikinshi, sai dai yanda ta fisgi jikin nata ne ya sanya ta tafiya baya da d'an k'arfi kamar zata fad'i k'asa yayin da Sabeer wanda gaba d'aya kasala ta baibaye shi ya biyo ta shima.
Sauran kad'an Suhaima ta saki ihu na tsoro sai taji ta fad'a saman bed yayin da Sabeer ya biyo ta shima cikin jikinta, lokaci d'aya suka sauke wata ajiyar zuciya sai dai kowannen su da banbancin ajiyar zuciyar tasu Suhaima ita ta jin dad'in bata fad'i k'asa ba shi kuma Sabeer na jin shi rungume da Babyn shi a jikinshi wanda ya d'auke tsayin lokaci da su had'u kamar haka.
Kok'arin tashi take amman ya wani rik'e ta k'am kamar wanda za'a kwace mishi itaa haushi ne ya ishe Suhaima ta d'aure fuska cikin fusata tace
"Malam wai me kake nufi ne haka ni ka d'aga ni wallahi ko nayi maka ihu "
Murmishi Sabeer yayi kafin yace
"Haba Baby nah kinsan nayi missing d'in ki da yawa ki barni ko na samu kwanciyar hankali da nutsuwa cikin zuciya ta "
Haushi ne ya k'ule Suhaima don haka tace
"Kada ka mance da bakin ka kace min ka tsane ni me yasa zaka zo inda nake nima kasani na dad'e da tsanar ka tun lokacin da ka furta min haka "
Jikin Sabeer ne yayi wani irin sanyi wanda Suhaima har ta samu ta ture shi daga jikinta ta mik'e tare da d'aura d'an kwalin kanta ta wani kalle shi taja tsaki ta fice daga d'akin gaba d'aya.
Tana fitowa suka had'a ido da Aunty Aliyah da take zaune can gefen kitchen tana aiki, sake d'aure fuska Suhaima tayi don duk ita taja gashi ba don tayi kok'arin yakice shi ba da tuni ta bada kai bori ya hau, don haka ta samu waje ta zauna kawai ko kula Aliyah bata yi ba, sauran kad'an dariya ta kubce wa Aunty Aliyah amman ta danne ta kada ta janyo tayi mata kuka da rigima don kad'an daga aikin Suhaima don haka taja bakinta tayi tsit ta cigaba da aikinta.
Wani zafi da zugi ne yake ji cikin zuciyar shi kalaman Suhaima ne kawai suke fad'o mishi a rai da jan tsakin da tayi mishi don yaji ta ya dad'e kwance a haka yana tufka da warwara tare da yin d'unbin nadamar abin da yayi dakyar ya iya shiryawa cikin wani jeans blue da T-shirt fara mai k'aramin hannu ya d'an fesa perfumes kan ya zauna ya sha tea d'in da ya fara sanyi ma.
Yana gama sha ya mik'e ya d'auki kayan shi ya rik'e mai dattin a d'ayan hannun ya fito waje kallon Suhaima ya d'an yi kan ya kalli Aunty Aliyah yace
"Auntyn mu nagode bari na d'an fita waje ko zanga Ashiru don bamu had'u ba tun da nazo "
"Toh Sabeer sai ka dawo, amman ina zaka tafi da kayan nan masu datti haka a hannu? "
D'an murmishi yayi yana cewa
"Anjima zan wanke su ne zan ajiye su a inda nake kwana "
Tausayin Sabeer ne ya kama Aunty Aliyah tasan bai ta6a tsammanin zai yi irin wannan kwatankwacin rayuwa ko zuwan da yayi na farko baya yin wanki Yah Aliyu ne yake had'a wa ya wanke musu da nashi.
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
â™» *єχ¢ℓυѕινє ωÑιтєÑ'Ñ• fσÑυм*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.