Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 30 of 67

PAGE 55-56

Yana cikin wannan haline Aliyu ya shigo d'akin hannun shi rik'e da paracetamol da ruwa a cup na roba, ganin halin da Sabeer yake ciki ne yasa Aliyu ajiye maganin a gefe ya k'arasa wajen shi da sauri ya rik'o shi tare da cewa
"Sabeer jikin ne? "
Jan wani numfashi yayi wanda ya sanya Aliyu mugun tsorata, a hankali kuma ya sauke numfashin nashi tare da zaunawa saman katifar ya jingina bayan shi da bango kallon Aliyu yayi da idanun shi jawur dasu wanda yake afkin yi mishi sannu fuskarshi da tarin damuwa yace

"Kada ka tashin hankalin ka bani maganin nasha "
"Kodai zamu je asibitin nan na kusa damu su duba ka "
Cewar Aliyu d'an murmishin yak'e yayi kafin yace
"Basai mun je ba naji zazza6in ya sauka yanzu sauran ciwon kai bacci zanyi yanzu "

Sannu Aliyu ya k'ara yi mishi kafin ya fita ya bashi gurin dob ya samu damar yin bacci, tunani kawai Sabeer ya fad'a na yanda Suhaima take wulak'anta shi ina laifin shi anan don kawai yace yana sonta da wannan tunanin bacci mai nauyi ya d'auki Sabeer.

Tunda Sabeer ya farka daga baccin yaji da sauk'i ciwon kan ya ragu, tun daga lokacin Sabeer yake kok'arin koyan cin abincin su yana kuma bin Aliyu gona duk da baya kok'arin yin aiki idan sun je zai zauna yana kallon yanda yake yi ko kuma ya dunga zagaye gonar ko kuma Ashiru wanda ya taimake shi ya kawo shi gidan su Suhaima da yamma wani lokacin zai zo su tattaka zuwa cikin k'auyen, gashi yana kiran iyayen shi su gaisa sannan Aliyu, Aliyah da Babaa Lantana da Baba Adamu suna kok'ari wajen janshi a jiki ya sake dasu tamkar 'yan uwan na jini.

Sai dai ta 6angaren Suhaima ne har yanzu babu wani cigaba don har yanzu tak'i bawa Sabeer fuskar da zai bayyana mata yanda yake sonta.

Aunty Aliya kuma tayi nauyi sosai sai ya kasance duk wani aiki na cikin gidan Suhaima ke yi, yayin da Aliyu wani lokacin yake taimaka mata idan ayyukan sunyi mata yawa.

Suhaima ce zaune saman kujera tana yankan salad tana sauraron freedom redio cikin shirin su na duniyar mu a yau wanda Usman Usman yake gabatar wa tana son shirin sosai batason ya wuce ta, Sabeer ne yayi sallama ya shigo gidan tun kafin ta amsa mishi, haushi ya turnik'e ta don haka sai ta fara gunguni tana cewa
"Mutum sai kawai ya shigowa mutane gida kai tsaye tun kafin a amsa mishi sallamar a bashi izinin shigowa sai kace a gidan arna "

D'an murmishi yayi yana girgiza kai don yaji ta tsaf sai kawai ya tashi ya koma zaure sannan yayi sallama mamaki sosai Suhaima taji da taji ya koma sai da ta d'an jima kafin ta amsa mishi sallamar sannan ya shigo yaja kujera ya zauna lokacin har ta gama yankan salad d'in.

Shiru taji bai yi magana ba sai ta d'an d'ago kad'an ta kalleshi duk ya rame yayi d'an bak'i kad'an kamar ba Sabeer ba, gani tayi zai kallo inda take ya sanya ta kauda idonta da sauri zata tashi kenan taji muryar shi cikin sanyi yace

"Baby taimaka min da abinci I'm very hungry wallahi please "

Yi tayi kamar bata ji shi ba ta wuce kitchen kafin ta fito ta wanke salad d'in duk yana kallon ta don tayi mishi kyau cikin wata gown ta atampha duk da basu kamata ba d'inkin amman sun zauna cif a jikin ji yake kamar ya sanyata cikin jikin shi ya dunga fad'a mata irin son da yake mata ko ya samu sassaucin da yake ciki.

Ya fad'a dogon tunani yana yi yaji kamshin turaren Suhaima a kanshi da sauri ya d'ago kanshi ya kalle ta tana tsaye hannun ta d'auke da plate na abinci tana mik'a mishi, hannun shi ya sanya ya kar6a hadda ta6o mata 'yan yatsun ta saboda tsokana yak'i kar6ar plate d'in aikuwa wani irin shock Suhaima taji ajikinta wanda bata ta6a jin irin shi ba da sauri ta saki plate d'in nan yayi saurin tarewa yana sakin murmishi ganin irin yanayin da ta shiga ajiye abincin yayi yana kallon shi shinkafa da wake ne sai salad da mai da yaji gefe d'aya a saman abincin ga kifi nan an sanya sosai abincin ya bashi sha'awa.

"Uhm sauran ruwa Baby "
Ya fad'i hakan a lokacin da Suhaima take kok'arin shiga d'akin ta ta huta don ta gaji tun safe take aiki, haushi ne yake kamata tun lokacin da Sabeer ya koyi ce mata Baby kuma ko a gaban su Yaya Aliyu haka yake fad'a mata, komawa tayi kitchen ta samu jug k'arami mai murfi ta d'ebo mishi na randa mai sanyi ta kawo ta dangwarar mishi a gaban shi.

"Sannun ki Baby nah Allah ya bani ke "
Ko kallon shi bata yi ba ta juya ta wuce d'aki sai kawai taji zuciyar ta tak'i aminta ta furta ba Amin ba daga addu'ar da Sabeer yayi.

Cikin kwanciyar hankali ya fara cin abincin yayi mishi dad'i sai dai ko rabi bai ci ba ya ture shi saboda yayi mishi yawa yasan da gayya ta zubo mishi da yawa, yana nan zaune ya fara jiyo muryar Aliyah k'asa k'asa tana kiran Suhaima daman yinin yau a d'aki ta yini bata jin dad'in jikinta.

Jin wannan kiran yasan Suhaima bazata ji ba ya sanya shi tashi ya nufi d'akin Suhaima ya shiga ba tare da neman izinin ta ba tana kwance saman bed tayi kwanciyar ringingine tana duba littafin addu'o'i.

Tsayawa kallonta kawai ya tsaya yi don wannan kwanciyar ba k'aramin sanya shi a wani yanayi na daban, Suhaima ji take kamar ana kallon ta sai ta kawar da littafin daga saitin fuskar ta fuska a d'aure tace
"Malam lafiya zaka shigo min d'aki ba neman izinin? "
D'an sosa kai yayi kafin yace
"Aunty Aliyah tana kiran ki "
Yana gama fad'in haka ya fita, d'an tsaki taja kafin ta mik'e ta fita d'akin Aliyah ta shiga sai ta tarar da ita cikin wani hali don nak'uda ce ganga ganga ta taho mata da sauri ta k'arasa inda take durk'ushe ta rik'o ta tana kuka.

Sabeer zai fita kenan yaji kukan Suhaima nan ya fara kiran sunan ta hankalin tashe gashi bashi da damar shiga d'akin, nan Aliyah dakyar ta fad'awa Suhaima taje ta kirawo mata Babaa Lantana.

Tana fitowa taci karo da Sabeer wanda yake tsaye a bakin k'ofar hankalin shi a tashe kamar ya fad'a d'akin haka yake jin shi.

Ganin Suhaima zata fita yasa shu rik'o hannun ta yace
"Baby what wrong with U? "
Kamar ta share shi sai kuma tace
"Aunty ce zata haihu tana shan wahala "
"Innalillahi bari naje na kirawo Yaya da Babaa Lantana ki zauna kusa da ita "

Da sauri ya juya ya fita yayin da Suhaima ta koma cikin d'akin, babu dad'e wa da fitar shi sai ga Babaa Lantana da Aliyu sun shigo gidan tare da Sabeer nan suka shiga cikin d'akin ban da Sabeer wanda yake tsaye zuciyar fal tausayin Aliyah.

Yana nan tsaye Suhaima ta fito tana kuka da Aliyu wanda idanun shi suka yi ja na tausayin halin da matar shi take ciki akabar Babaa Lantana a cikin d'akin
"Ya kamata mu tafi hospital "
Cewar Sabeer da ya matso kusa da Yaya Aliyu, d'an girgiza kai Aliyu yayi kafin ya bud'e baki yayi magana sun ji kukan jariri.

"Alhamdullilah "
Suka furta gaba d'aya suna nan tsaye Babaa Lantana ta fito fuskarta d'auke da farinciki tace
"An sauka lafiya mun samu namiji "
Nan fuskar su ta fad'ad'a da fara'ar farinciki, Suhaima mai kuka ta dawo dariya har da buga tsallen murna ta rungume Yayanta, kallon su Sabeer yake cike da sha'awa daman shima yana da k'anwa ko Yaya wanda suka fito ciki d'aya da shima ya nuna mishi irin son da yaga Aliyu da Suhaima da suke yiwa junan su.

Suhaima ruwa ta d'ora kan wuta bayan ta hura itace bayan yayi zafi ne ta kwashe takai toilet sannan ta d'ebo wanda za'a yiwa jariri wanka ta kai d'akin Aliyah inda har Babaa Lantana ta gyara ko'ina fes ta sanya turaren wuta na kamshin d'akin.

"Sannu Aunty Aliya "
Suhaima ta furta tana rik'o hannunta fuskarta d'auke da murmishi,
"Yawwa kanwata ke ma sannun ki "
Kamata Babaa Lantana tayi ta kaita band'aki wanka tayi mata suka fito sannan tayi wa jariri lokacin da suka gama tsaf suka shirya sai ga Yaya Aliyu nan da taxi ya taro zasu je asibitin da Jiddah ta kaisu lokacin tana laulayin ciki.

Suka tafi aka bar iya Suhaima a gidan tana dad'a gyarawa, bayan ta gama ne sai tayi wanka ita ma ta fito d'aure da zanin wanka ko hijab bata sanya ba da yake tasan a tunaninta Sabeer ya bi su hospital ne.

Tsayawa tayi bayan ta fito daga wankan tana taje dogon gashin kanta ta sunkuyar da kan gashin yayi gaba tana taje shi, bayan ta gama irin ta d'ago kanta gashin yayi baya sai a fuskar Sabeer wanda shigowar shi kenan gidan, ya hango ta tana taje kanta.

"Wash! kin sanya min gashi a ido da bakina fah"
A d'an tsorace Suhaima ta jiyo jin muryar Sabeer a kusa da ita, suna had'a ido nan gabanta ya hau fad'uwa ganin irin kallon da yake jifanta dashi idanun shi har sun fara canja launi, na shiga uku ni Suhaima daman wannan mutumin bai bi su ba, ta fad'i hakan cikin zuciyar ta tana mai ja da baya shima yana bin ta da haka har bayanta ya jingina da bangon d'akin ta sai kawai ta runtse ido tare da k'ank'ame jikinta waje d'aya.

Hannun shi ya sanya ya d'auke gashin da ya rufe mata face nata ya zuba mata ido musamman pink lips nata wanda ta d'an danne na k'asan kad'an da hak'orinta na k'asa ji yake kamar yayi ta kissing d'in su sai dai ba yanzu ba da sauran lokaci amman duk lokacin da ya mallake su sai ta gane kurenta sai ya ladaftar dasu ta tsiwar da suke mishi.

"Baby open your eyes please "
A hankali ta bud'e idanunta gabanta na cigaba da fad'uwa ta zube idanunta saman fuskar Sabeer wanda batasan lokacin da suka d'auki mintuna 2 tana kallon cikin idanun shi wanda daga k'arshe kasa jure kallonsu tayi sai kawai ta sunkuyar da kanta k'asa jikinta yayi sanyi wani irin abu ne yake fisgarta game da Sabeer amman tana kok'arin yaki ce shi don batason yayi mata tasiri akanta.

"Baby mene aibuna da baki sona why Suhaima? "
Shiru tayi babu amsa hannun shi ya sanya ya d'ago face nata cikin muryar shi da ta soma rawa tamkar wanda zai fashe da kuka yace
"Saboda me baki sona ni d'an iska ne ko kuma ban cancanta a so ni ba? "
Girgiza kanta tayi don bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana.
"Toh kina sona? "
Nan ma ta girgiza kai, wani abu ne ya tokare wuyan Sabeer wanda ya sanya wasu hawaye fita daga idon shi.

A hankali ya saki fuskarta jikin shi yayi sanyi sosai goge hawayen face nashi yayi tare da sakin murmishin yak'e yace
"Ni kuma ina son ki kuma insha Allah zai kin zama tawa, ina son ki Baby "

Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi har yana cin tuntu6e da abu sauran kad'an ya fad'i saboda gaba d'aya ba'a hayyacin yake ba.

Hankali Suhaima ya tashi da sauri ta ce
"Sabeer kayi hankali kada kaji ciwo"
D'an jiyowa yayi ya kalleta kafin ya juya ya bar gidan gaba d'aya zuciyar shi sam babu dad'i.

Jikinta a sanyaye ta shige d'aki ta kwanta rub da ciki a saman bed wasu hawaye ne suka fara zuba a idanunta me yasa bata ta6a jin tausayin Sabeer irin na yau, me yasa ta fara jin wani yanayi game da Sabeer wanda bata ta6a jin irin shi ba, anya kuwa zuciyar ta bata fara son Sabeer ba kuwa?......

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/24, 9:00 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.