Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 25 of 67

PAGE 46-47

Daddy kasa jure ganin tilon d'an nashi a haka yayi don sam bazai iya ganin Sabeer cikin mawuyacin hali ba don haka ya bud'e baki yace
"Ammm ku d'an bamu wuri zamu yi magana da Sabeer please idan muka gama zan kirawo ku"

Tashi suka yi suka fita kafin Daddy ya matso kusa da Sabeer ya dafa kafad'ar shi da hannun shi d'aya, zame hannun Daddy yayi tare da juyawa ya kalli wani 6ari daban, d'an murmishin yak'e Daddy yayi wai yau Sabeer d'in shi akan soyayya yake juya mishi baya wannan wanne irin so yake mata, bar tunanin yayi ta hanyar cewa
"Son look at me please"
Fuska a had'e Sabeer ya jiyo yana kallon Daddy sai wani had'e rai yake. Girgiza kai kawai Daddy yayi kafin yace
"Son bazan iya jurar ganin ka cikin wannan yanayin ba, na amince ka auri wannan yarinyar sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba tace maka bata son ka ya za'a yi? "

Tuni fuskar Sabeer ta fad'ad'a da wani irin fara'a na tsantsar farinciki saboda jin abin da Daddyn shi yace, rungume shi yayi cikin dariya mai hawaye yace
"Thank U Daddyna nasan kai mai k'aunar farinciki na ne duk abin da nake so kana kok'arin yi min, sannan zan tafi inda Suhaima take nayi rayuwa irin tasu don na sami soyayyar ta A SANADIN SON Suhaima zan iya jure duk wata wahala Daddy indai zan same ta "

Kallon shi Daddy yake kawai cikin d'umbin mamakin abin da Sabeer ya fad'a ajiyar numfashi yayi kafin yace "Son kana nufin k'auyen zaka koma da rayuwa, kaci irin abincin su, ruwan su ka kwana irin d'akin su?"

"Yes Daddy zan iya indai zan samu Suhaima "
6ata fuska Daddy yayi tare da cewa "ina Son bazai yiwu ba, kaje dai ka taho dasu ita da Family d'in ta zan basu gida da kud'i sosai sannan na bawa mahaifin ta aiki amman kaje k'auye kana matsayin jikan mafi soyuwa acikin family d'in d'an fillo kaje ka zauna a k'auye haba Son "

D'an yatsina fuska yayi tamkar zai fashe da kuka yace "ni dai zan iya Daddy idan naje zanyi musu maganar dawowa nan da abin da zaka yi musu nasan zasu biyo ni "

Girgiza kai Daddy ya fara alamar bai yarda ba, aikuwa Sabeer ya ta6e fuska irin ta shagwa6a66un yaran nan zai fashe da kuka da sauri Daddy ya rungume shi yana bubbuga bayan shi yace
"Nooo Son don't cry please na amince Allah ya baka nasarar sace zuciyar ka kamar yanda ta sace maka zuciya lover boy"

Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer, kafin ya saki wani murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ganin tafe zuwa gare ki Suhaima, rungume Daddy yayi cikin farinciki yace
"Thank U so much Daddy i am proud of U"
Bubbuga bayan shi Daddy yayi kafin yace
"Don't worry Son farinciki ka shine nawa all the best"

"K'arya kake Sabeer daman akan 'yar talaka 'yar k'auye kake wannan haukan duk ka d'aga mana hankali, danasan saboda haka kayi wannan abin da wallahi bazan zo wajen ka balle har na zubar maka da hawayen tausayi "

Gaba d'aya suka jiyo a matukar razani daga Daddyn har Sabeer d'in had'a ido suka yi da Mummy tana tsaye sai faman sauke numfashi take fuskar nan ko kad'an babu fara'a.

"Nima ina goyan bayan ta bazan ta6a zuba ido ya auro mana 'yar matsiyata ba daman akan haka kake wannan haukar to ko zaka mutu baza mu ta6a yarda ba, amman Sabeer ka bani kunya da mamaki, kai ma Hussein ka ban kunya da ka amince da buk'atar shi " cewar Hajjoh cikin tsananin 6acin rai.

Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya kasa magana ma saboda tsantsar 6acin rai har wani rawa fuskar shi take lol, saboda 6acin rai magana ma ya kasa yi. Had'e fuska Sabeer yayi alamar ba wasa ya mik'e tsaye yana d'ingishi ya k'arasa wajen Hajjah yace
"Hajjah kada ki k'ara kiran Suhaima da 'yar matsiyata ni Suhaima nake so ba ruwana da kud'in su don haka sai na aure ta babu wanda ya isa ya hanani! "

Tasss Sabeer yaji saukar zazzafan mari a saman kuncin shi wanda tunda Mumy ta haifo shi ba'a ta6a marin shi ba, marin ba k'aramin shigar shi yayi ba don sai da gefen bakin shi ya fashe kad'an jini ya fito, dafe kumatun shi yayi cikin mamaki ya d'ago kanshi ya kalli wanda ya mare shi ba kowa bane sai Alhj Ahmad d'an fillo sai huci yake zuba kamar wanda ya had'iyi kunama har da had'a gumi tamkar babu ac da fanka a bedroom d'in yayin da Daddy, Mummy da Hajjah suka kusan suman tsaye tsabar kid'ima da abin da akayi wa Sabeer.

Yana dafe da kumatun shi yana kallon Alhj Ahmad kafin kuma ya lumshe idon shi sai gani suka yi yayi baya luuu zai fad'i k'asa cikin zafin nama Alhj Ahmad da Daddy suka taro shi ya fad'o jikin su. Daddy jiki na rawa ya d'auko wayar shi ya kirawo Doctor, Hajjah da Mumy kuma kuka suka sanya tare da zube wa kusa da inda Sabeer yake suna cewa
"Sabeer ka tashi please "

Daddy ne ya d'auke shi ya d'ora kan bed da taimakon Doctor ya shigo don Alhj Ahmad zube wa yayi a k'asa yayi zaman 'yan bori hannun shi yake bi da kallo wanda ya mari Sabeer dashi tamkar wani soko haka yake kallon hannun, wai shi yau ya mari Sabeer mafi soyuwa cikin zuciyar a gaba d'aya cikin jikokin shi, anya shine kuwa da hankalin shi ya aikata wannan abin ko dai mafarki yake yi ba gaske ba ne kamar wani mutum mutumi haka ya koma ya rasa me zaiyi ma.

Dakyar Daddy ya lalla6a su Mumy da Hajjah suka fita don a bawa Doctor damar duba Sabeer haka Daddy yazo ya janye Alhj Ahmad dakyar suka fita tare da jan k'ofar bedroom d'in.

Likita yana cikin duba Sabeer yaga ya bud'e idon shi tare da tashi ya zauna cike da mamaki Doctor yake kallon shi, kamo hannun likitan Sabeer yayi sannan yace
"Doctor ina son abin da zan fad'a maka yanzu ka sanar da iyaye na bana son a samu matsala fah"
Gid'a kai likita yayi kafin yace "Okay baza'a samu matsala ba insha Allah "
A hankali Sabeer ya matso kusa da likitan kafin ya fara yi mishi magana cikin k'asa k'asan murya, bayan ya gama yi mishi maganar ne ya koma ya kwanta tare da rufe idon shi.

Suna zaune jugum jugum a parlour kowannen su ya rafka tagumi suna tunani ba mai yin magana a tsakanin su, k'arar bud'e door suka ji da sauri suka mik'e tsaye tare da nufar Doctor da sauri kowanne na jefo mishi tambayar jikin Sabeer.

D'an share zufa likitan yayi yayi shiru baiyi magana ba, cakumar wuyan shi Alhj Ahmad yayi tare da cewa
"Kai wanne irin wawa ne muna maka magana ya jikin Sabeer zaka zuba mana ido kana kallon mu kamar ka samu tv"

Ba k'aramin shak'a likita yasha ba dakyar Daddy ya cire hannun Alhj Ahmad daga wuyan shi, kafin yace
"Abba mu bi a hankali please "

Zama suka yi sannan likita ya shafa wuyan shi tare da jujjuya shi yace
"A binciken da nayi damuwa ce tayi wa Sabeer yawa sosai wanda a yanzu yana d'auke da hawan jini, idan kuka cigaba da matsanta mishi da 6acin rai ko ku k'i mishi abin da yake so idan ranshi ya 6aci zuciyar shi zata iya bugawa na lokaci d'aya don haka ku kiyaye "

"K'arya kake zuciyar Sabeer bazata ta6a bugawa ba "
Cewar Alhj Ahmad cikin tsawa gaba d'aya hankalin shi a tashe yake, "a cigaba da kwantar mishi da hankali a bashi abin da yake so, zanje na kawo maganin da zai sha yanzu "

Babu wanda ya kula shi haka ya zame ya tafi sannan suka shiga cikin d'akin inda Sabeer yake kwance, nan Alhj Ahmad ya zauna kusa dashi tare da rik'o hannun Sabeer yana mai nadamar abin da yayi mishi, a lokacin Daddy ya kirawo mai gyaran k'afa ya fara gyarawa Sabeer kafar shi kuka sosai Sabeer yasha shi a lokacin haka Hajjah da Mummy tare da Alhj Ahmad sun zubar mishi da hawayen tausayi Daddy ne kawai yayi dauriya ta rik'e Sabeer har aka gama gyara mishi kafin daga k'arshe wani wahalallen bacci ya sake d'aukan shi sai sauke ajiyar zuciya yake.......

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/6, 8:12 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz

Dis page is dedicated to my Biebie dee ina tayaki murnar k'arin shekara Allah ya k'aro shekaru masu albarka Allah ya baki miji nagari wanda zai kular mana dake muzo musha biki 💃🏻😍😅.

_fan's kuyi hak'uri akan rashin yi muku typing kwana 2 akwai uzirin da ya dakatar da ni but yanzu insha Allah zan cigaba da yi muku daidai iyawata, inason ku oll my fan's_❣

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.