A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 67
PAGE 32-33
Bayan tafiyar Yaya Aliyu ne Jiddah ta shigo motar tayi mata key maimakon su shiga gidan sai Suhaima taga ta juya sun bar unguwar gaba d'aya, cikin tsokana Jiddah tace
"Baki ji tsoro ba kada na siyar da ke naga baki tambaye mu ina zamu je ba "
D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa
"Na yarda da ke ne sosai Jiddah nasan son da kike min bazai sa ki cutar da ni ba "
"Haka ne tawan Allah ya bar mu tare har 'ya'ya da jikoki, waiii ya kaga Suhaima da jikoki suna cewa goggo Suhaima "
Dariya kawai suka yi adaidai lokacin Jiddah ta k'araso inda zasu je wani katafaren shagon yin gyaran jiki, saloon, manicure and pedicure da kuma make-up sai lalle, parking Jiddah ta samu tayi suka fito zuwa cikin shagon sosai wajen ya burge Suhaima, matar wajen tana ganin Jiddah ta fara washe baki da alama ta saba zuwa wajen.
Babu 6ata lokaci Jiddah ta fad'a wa matar abin da za'a yi wa Suhaima, aikuwa nan suka shigar da Suhaima wani room suka farayi mata gyaran jiki na dilka sosai suka tsaya suka gyara Suhaima sun san zasu samu kudi masu tsoka, bayan an gama gyaran jikin aka yi mata gyaran su farce sannan aka dawo kan lalle daga k'arshe kuma aka gyara mata gashi wanda basu sanya mata relaxer ba cos gashin Suhaima yana da tsantsi irin na asalin fulani sai suka wanke mata kan da kalolin shampoos and conditioner different color's, sannan suka busar mata da dogon gashin ta da hand dryer tukunna suka gyara mata in style.
Kyan da Suhaima tayi 6ata lokaci ne wajen fad'ar shi tayi kyau sosai tamkar ba ita ba, har wasu kayan Jiddah ta bata ta sanya wata milk d'in gown mai adon light green sai veil light green shima nan ta sanya kayan aka yi mata light make up sosai tayi kyau, rolling d'in veil d'in suka yi mata akanta ba k'aramin had'uwa tayi ba idan kaga Suhaima ka d'auka irin mai kud'in nan ce ba daga k'auye ta fito ba.
Ita kanta Jiddah bata zata haka Suhaima take ba sai yanzu hankalin ta ya kwanta tasan dai ba lalle iyayen ta su gane daga inda Suhaima ta fito ba, kuma ba laifi kan Suhaima a waye yake bata da dahun kai, nan Jiddah ta biya kud'in suka fito daga shagon kai tsaye gida suka nufa.
Horn Jiddah tayi gateman ya bud'e mata kofa ta shigo ciki a parking lot tayi parking tukunna suka fito daga motar, sakin baki da hanci Suhaima tayi ganin irin girman gidan su Jiddah gashi part part ne sosai gidan ya birge Suhaima amman bata kuma aha'awar zaman irin cikin gidan nan don tasan dole a samu masu wulak'anta mutane, ta6o ta Jiddah tayi tana murmishi tace
"Alhamdulillah yau Allah ya nufa Suhaima zata zo gidan mu, ina cikin farinciki yau sosai, Suhaima ga gidan mu nan kina ciki yau anan aka haife ni na girma, daman na fad'a miki gidan mu muna da yawa don kakan mu da iyayen mu duk a ciki muke zaune "
Gid'a kai Suhaima tayi tana k'ak'alo murmishin yak'e kafin tace
"Masha Allah wannan gidan naku yayi kyau sosai Jiddah "
Kamo hannun Suhaima tayi tare da cewa
"Thank U my dear "
D'auko bag d'in Suhaima tayi suka nufi wani part, duk taku d'aya da Suhaima take sai gabanta ya fad'i sosai gaba d'aya a tsorace take kamar wadda za'a sace haka take jin ta.
Suna shiga cikin k'aton parlourn wani sanyin Ac da k'amshin turare ya bugi hancin Suhaima ko'ina tsab dashi duk da mutanen da suke zazzaune cikin parlourn kuwa, kusan gaba d'aya mutanen kallon Jiddah da Suhaima suke.
Tuni Suhaima ta fara tsarguwa da kallon, wata matashiyar budurwa ce kamar sa'ar Jiddah ta taso da gudu ta rungume Jiddah tana cewa
"Ga amarya ga amarya nan ta dawo, ina kika shige muna ta neman ki? "
D'an murmishi Jiddah tayi tare da cewa
"Na d'an fita ne wani wajen "
Kallon budurwar tayi tare da cewa
"Zahra meet my friend Suhaima Omar, Suhaima meet my sister Zahra 'yar gidan K'anin Abban mu ce "
Cikin murmishi Suhaima tace
"Ina yini? "
Wani banzan kallo da Zahra tayi wa Suhaima sai da ta kusan zubewa a k'asa saboda rawar da jikin ta ya fara, wani banzan tsaki Zahra ta saki tare da hararar Jiddah tace
"Kefa tsiyata kwashe kwashe ne dake ina kuma kika samo wannan villagers girl d'in? "
Dumm gaban Suhaima da Jiddah ya fad'i, duk gyaran da ta kashe kudi tayiwa Suhaima don kada su gane daga inda ta fito sai da Zahra ta gane, wannan maganar a cikin zuciyar ta Jiddah tayi bayan ta gama k'arewa Suhaima kallo inda taga ita bata hango makusa ba sai ma kyan da Suhaima tayi, amman sai ta dake ta harari Zahra tare da cewa
"Ni fah bana son iskanci Zahra wannan fa friend d'ina ce tare muka yi schl itace fa Suhaiman da nake baku labari"
Wata shegiyar dariya Zahra ta saki tare da nuna Suhaima da d'an yatsa tace
"Dis villagers girl ce kuka yi schl tare kin ma raina min hankali nafa sanki da kwashe kwashe "
Haushi ne ya turnik'e Jiddah a fusace taja hannun Suhaima wanda idanun ta sun ciko da kwalla taf suka nufi hanyar da zata kai Jiddah part d'in Umman ta yayin da Zahra da sauran mutane wanda suka karkata hankalin su da jin hirar tasu tuntsire wa da wata irin dariyar ta rainin hankali.
Wani parlour suka dad'a shiga tsayawa Jiddah tayi tare da jiyowa ta kalli Suhaima tace
"Don Allah Suhaima kiyi hak'uri da abin da Zahra tayi miki bata kirki ne "
Mayar da kwallar Suhaima tayi tare da kwakwalo murmishi yak'e tace
"Kada ki damu Jiddah duk abin da akayi min zan d'auke kai saboda ke "
Rungume ta Jiddah tayi cikin farinciki da jin abin da Suhaima tace mata
"Thank U so much dear "
"Jiddah ke da wane? "
Da sauri Jidd ta saki Suhaima jin maganar Umman ta wani kallo Umman take yiwa Suhaima kamar irin kallon da Zahra tayi mata.
Da murmishi akan fuskar Jiddah taja hannun Suhaima zuwa kusa da Umma tace
"Umma ni da Suhaima ne, itace wadda nake baki labari, Suhaima wannan ce Ummana"
Da sauri Suhaima ta durk'usa k'asa cikin girmama wa tace
"Umma ina yini? "
"Lafiya "
Cewar Umma cikin halin ko inkula daga k'arshe ma cewa tayi
"Jiddah kiyi sauri ki wanka yanzu mai makeup zata zo kinsan yau ne dinner wadda Hajia Faridah ta shirya na family koh"
Tana gama fad'in haka ta wuce ko kallon inda Suhaima take bata sake yi ba ta wuc abinta cikin tak'aici Jiddah tabi bayan Umma da kallo kafin ta dawo hankalin ta kan Suhaima da har yanzu take durk'ushe ta kasa tashi saboda mugun sanyin da jikinta yayi na abin da ta fara cin karo dashi tun shigowar ta gidan su k'awarta Jiddah.
A lokacin hankalin Suhaima ya tashi sosai ta d'auka Umman Jiddah zata kar6e ta da fara'a ba kamar Zahra ba, shi yasa tayi wa Jiddah alk'awarin kauda kai daga abin da akayi mata, amman fah Jiddah tayi mata abubuwan da zata iya jure duk wani cin kashin su akanta na tsayin kwana biyu daga lokacin da tafi gidan su babu wanda zai sake ganin ta balle har yayi mata kallon banza.
"Kiyi hakur..... "
Jiddah ta fad'i hakan tana d'ago Suhaima fuskar ta da tarin damuwa sosai, da sauri Suhaima ta toshe mata baki da tafin hannun ta tare da k'ak'alo murmishin dole tace
"Kada ki bani hak'uri Jiddah me akayi min babu komai kada ki damu please "
Girgiza kai Jiddah kawai tayi tare da rik'o hannun ta tana cewa
"Mu tafi bedroom d'ina ki huta kiyi hak'uri da halin 'yan gidan mu kusan haka suke "
Gaban Suhaima ya sake fad'uwa da jin abin da Jiddah ta fad'a anya zata iya zaman gidan nan kuwa...
Aishat A Muh'd ðŸÂŒðŸÂ»â€Â♀
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœÂðŸÂ»: 💠A SANADIN SON KI ðŸ’Â
Written by
Aishat A Muh'd
â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.