A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 29 of 67
PAGE 53-54
Bud'e labulen d'akin Aliyah tayi tare da shigowa zama tayi kusa da Suhaim wadda ta kwanta rub da ciki a saman gadon ta, dafa bayan ta tayi kafin tace
"Suhaima tashi mu yi magana "
Tashi Suhaima tayi zaune tana goge hawayen fuskar ta da hannunta, kallon mamaki Aliyah take mata kafin tace
"Me yasa kika yi mishi haka Suhaima?, haba Suhaima bansan ki da halayyar wulak'anta mutane ba, ki tuna saboda sanadin son ki fah ya bar gatan shi da komai nashi na jin dad'i ya dawo nan k'auye wanda bai ta6a rayuwa acikin irin wannan yankin ba ya aminta zai jure kowacce wahala indai zai same ki, koda da iya abincin mu ma kafin ya saba aiki ne zai hak'ura ya jure duk don A SANADIN SON KI, haba Suhaima ki tausaya mishi kada ki bashi wahala don na tabbatar Sabeer son ki yake tsakani da Allah ba yaudarar ki yake, idan yaudara ce ma bazai zo har nan ba don haka kiyi tunanin kafin ki yanke hukunci tukunna "
Zum6ura baki Suhaima tayi tare da cewa
"Ni gaskiya Aunty bana son Sabeer hasalima kinsan na tsani auren mai kud'i saboda gujewa wulak'anci, musamman gidan su Sabeer tunda na baki labarin abin da suka yi min"
D'an shiru Aliyah tayi tana d'an tunani kafin tace
"Kina da gaskiya don wannan amman ni ina mai baki shawara kiyi tunani sosai kafin ki yanke hukunci,tare da addu'ar neman za6in Allah kada ki yanke hukunci da gaggawa"
Gid'a kai Suhaima tayi kawai tare da cewa
"Ni bama zan so shi ba"
"Hmmm na dai ji ki Suhaima kawai amman wannan zakad'ed'en sauryin ne kece bakya sonshi kawai ra'ayin ki ne ya hana ki tsayawa kiyi tunanin kin fad'a son Sabeer daga irin kallon da kike mishi d'azu "
Wayyo aikuwa Suhaima ji take kamar ta rusa kuka jin abin da Aunty Aliyah ta fad'a mata, zum6arar baki tayi tare da kwanciya ta juyawa Aliyah baya, abin ya bata dariya tashi tsaye tayi tare da cewa
"Abincin ki yana kitchen fah kije ki ci kada ya huce "
Tana gama fad'in haka ta fito daga d'akin, nan ta tarar da Sabeer da Aliyu sun dawo bayan tayi musu sannu da dawowa ta yiwa Sabeer sai da safe ta wuce cikin d'aki.
Sun d'an jima suna hira kafin Sabeer ya wuce d'akin da aka sauke shi bayan yayi wa Aliyu sai da safe, yana tafiya yana waiwayar d'akin Suhaima ko Allah zai sanya ya hango ta don kuwa yana son sake sakata cikin idanun shi kafin yayi bacci, Aliyu yana kallon yanda yake kallon d'akin Suhaima nan ya sake tabbatar wa Sabeer yana son Suhaima bana wasa ba, amman mene dalilin k'in amincewar Suhaima na ta kar6i soyayyar Sabeer?.
Sabeer yana shiga d'akin sai yaji shi kamar wanda aka sanya shi a akurki duk da d'akin yana da d'an girma kuwa hakan bai hana sa Sabeer ganin k'ank'antar shi ba irin wanda ya saba kwanciya da shi ba.
Zama yayi gefen katifar yaji ta tik'irk'ir tauri sosai, ga wani hucin zafi da d'akin yake fitarwa alamar dai ba'a yin amfani dashi a rufe yake sai shegen kukan sauro da ya addabi kunnen shi, ga ba wadataccen haske wata 'yar k'aramar fitila ce kawai a rataye jikin k'usa a bango mai irin mai batir d'in nan, zabga tagumi Sabeer yayi yana tunanin yanda ya tsinci kanshi inda bai ta6a tsammanin ganin a haka ba koda a mafarki sai gashi kwatsam lokaci d'aya ya tsinci kanshi aciki ikon Allah kenan.
Zumbur ya mik'e kamar wanda aka tsikara sakamakon wani fitsari da ya matse shi, wayyo Allah nah yanzu ta ina zan fara shiga toilet d'in su, fad'in haka cikin zuciyar Sabeer yana faman matse k'afa, fuskar nan tashi tayi kalar tausayi tamkar wanda zai fashe da kuka kasa jurewa yayi kawai ya tashi da sauri ya fito daga d'akin zuwa tsakar gidan.
Ba kowa a tsakar gidan ga duhu yayi tsit kake ji, yana nan tsaye sai ga Suhaima ta fito a d'aki zata shiga kitchen d'ebo ruwa suka kusan cin karo da Sabeer saboda duhu gashi babu wadataccen hasken farin wata, ba k'aramin tsorata tayi ba ta d'auka ko wani aljanin ne amman lokacin da ta fuskanci Sabeer ne sai kawai ta dake tare da d'aure fuska zata wuce daga sauri yasha gabanta ya tsaya
"Malam lafiya? "
"Uhm ina son ki nuna min toilet "
Da hannu ta nuna mishi ba tare da tayi magana ba ta wuce shi ta d'auko ruwan ta shige d'aki ko kallon inda yake bata sake yi ba, buta ya d'auka ya wuce cikin toilet d'in a d'an tsorace, duk da a duhu ne hakan bai sanya shi gane tsabtar da band'akin yake dashi ba a tsorace yayi abin da zai yi ya fito yana share gumi sai kace wanda yayi tseren gudu duk gumin tsoro ne, da sauri ya wuce d'akin ya rufe kafin ya kwanta saman katifar.
A cikin wannan daren ya zame wa Sabeer daren da bai ta6a tsammanin zai irin shi a wannan duniyar ba saboda yanda zafi da sauro suka hanashi runtsawa, idan zafin ya isheshi sai ya cire kayan jikin shi iya vest da 3quater ne kawai a jikin shi sai buge bugen sauro yake yi ko baccin kirki ya kasa samu ga wani tsananin ciwon kai da ya kamashi saboda gajiya ga rashin bacci.
Washe gari kuwa jikin Sabeer yayi luhu luhu da cizon sauro abin ka da d'an hutu kuma farar fata duk tayi ja tundaga fuskarshi kuwa har jikin shi inda kaya bai rufe ba, idanun shi sun yi ja sosai ga wani zazza6i da ciwon kan ya saukar mishi dashi wajen asubah, har gari ya waye yana kwance a d'aki bai iya fitowa ba sai da Aliyu ya shiga ya ganshi kwance sai rawar sanyi yake ya tukunkune waje d'aya.
Cikin tashin hankali Aliyu ya k'arasa tare da cewa
"Subhanallah! Sabeer baka da lafiya ne? "
D'an murmishin yak'e yayi hawaye na zuba a idanun shi na zafin ciwo yace
"Zazza6i ne yake damuna da ciwon kai ko zaka taimaka min da paracetamol? "
"Sannu Allah ya baka lafiya, bari na d'auko maka amman ka d'aure ka fito sai kayi brush kaci wani abin kafin ka sha maganin "
D'aga kai kawai Sabeer ya iya yi sannan Aliyu ya taimaka mishi suka fito tsakar gidan bayan ya d'auko mishi maclean da brush nashi cikin bag d'in da ya taho da ita.
Aunty Aliya da Suhaima suna zaune a kan tabarma ga breakfast a saman tabarmar da yake tare suke karyawa, Aunty Aliya batasan sand ta mik'e tsaye ba tana zaro ido tare da cewa
"Innallilahi Aliyu mai ya cije haka "
Zaunar da Sabeer yayi saman kujera kafin yace
"Cizon sauro ne wallahi"
"Allah sarki sannu Sabeer Allah ya baka lafiya "
D'an murmishin yak'e yayi mata yana d'aga kanshi alamar amsawa, tun lokacin da Aunty Aliyah ta fara magana Suhaima ta d'ora idanun ta kan Sabeer ta k'ura mishi ido cikin wani yanayi wanda ni kaina na kasa tantancewa, sai da suka had'a ido tukunna ta janye nata idon daga kallon shi ta sunkuyar da kanta.
"Suhaima zo ki samo ruwan d'umi a kitchen yayi brush dashi "
Tashi tayi ta d'auki buta ta d'ebo ruwan d'umin ta kawo maimakon ta sirka shi sai kawai ta dire a gaban shi a haka gaba d'aya jinta take wata iri kamar ba ita ba.
"Wash Allah! "
Taji muryar Sabeer ya fad'a da sauri ta kallo inda yake sai taga yana yarfe hannun shi tare da yatsina fuska ga hannun yayi ja sai lokacin hankalin ta ya dawo jikinta ta mance bata surka ruwan da na sanyi ba.
"Suhaima baki da hankali da zaki kawo mishi ruwan zafi ba tare da kin surka ba"
Fad'in Yaya Aliyu kenan yana hararar ta bayan sun had'a ido.
"Laaa Yaya na mance ne Allah kayi hak'uri "
Da sauri ta mik'e ta d'auki butar ta nufi wajen da suke ajiye ruwa ta surka ta kawo mishi tukunna ta koma ta zauna, duk inda tayi idanun Sabeer suna kanta suna shawagi gaba d'aya ta kasa sakewa.
A haka ya lalla6a yayi brush sannan ya dawo saman tabarmar zama yayi kusa da Suhaima sai ya jingina da bango, sannu Aunty Aliya da Yaya Aliyu suka yi mishi ya amsa muryar shi can k'asa, koko ne mai kauri yasha gasara Aliyu ya mik'a wa Sabeer hannun shi yasa ya kar6a tare da kaiwa baki ya kur6a.
Ba shiri ya furzo dashi waje sai a jikin Suhaima ya 6ata mata jiki don duk ya tsatstsalu a jikin ta har da saman fuskarta, sannu suka k'ara yi mishi yayin da Suhaima ta cukune fuska takaici da 6acin rai fal zuciyar ta har a saman fuskar ta ya nuna.
"Am sorry please "
Ya fad'i cikin sanyin murya fuskar shi d'auke da damuwa dagani kasan ba'a son ranshi yayi mata ba.
"Je ki canja kayan ki wanke fuskar ki"
Fad'in Aliyu kenan ganin irin yanda Suhaima take jifan Sabeer da kallon tsiwa.
A fusace kuwa ta mik'e ta wuce d'akin ta bata dad'e ba ta fito d'aure da zanin wanka tare da hijab a jikinta ruwan wanka ta had'a tare da wucewa toilet.
Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta ji yake tamkar ya tashi ya rungume ta cikin jikin shi ya rarrashi ta ya nuna mata hakan da ya faru ba'a son ranshi ba ne tsautsayi ne amman babu damar yin haka.
"Me zaka ci a dafa maka tunda baka son kokon? "
Fad'in Aunty Aliya kenan
"Aunty idan na samu ruwan tea ma ya isheni don bana sha'awar cin komai"
"Haba haba ruwan tea me zai maka ka fad'in abin da kake so kawai nan kamar gida ne "
"Kin ga wuce kitchen mu je "
Cewar Aliyu nan suka tashi suka tafi kitchen suna shiga Aliyu ya fita bai dad'e ba ya dawo, cikin mintuna kad'an Aunty Aliya ta dafawa Sabeer tea da yasha kayan kamshi citta da kaninfari sannan aka soya kwai suka kawo mishi.
"Sannu da kok'ari Auntyn mu"
D'an murmishi kawai tayi. A lokacin Suhaima ta fito daga toilet da harara tabi Sabeer kafin ta wuce d'akin ta.
Nan suka karya har suka gama Suhaima bata fito ba nan Aliyu ya tafi siyowa Sabeer paracetamol, yayin da Aunty Aliyah ta wuce d'akin ta.
Sabeer yana kok'arin mik'ewa don wuce wa d'aki ya kwanta Suhaima ta fito kallon shi tayi tare da cewa
"Malam ba lallai ba dole idan baza ka iya zaman nan ba ka tarkata ka koma inda ka fito tunda babu wanda ya gayyace ka anan don bazai yiwu kana had'a mutane da wahala ba "
Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan gaba d'aya, nan tsaye take Sabeer yaji wani zazza6in yana neman rufe shi dakyar ya iya kai kanshi d'aki ya zube akan katifa yana wani irin numfashi......
Kuyi hak'uri da ni fan's, kun ji ni kwana 2 shiru abubuwa ne sai a slow but insha Allah zan nayi kok'ari wajen typing.
Aishat A Muh'd âœðŸ»
[2/22, 8:55 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
Dis page is dedicated to Faridah Bashir (Ummu Safwan) marubuciyar Tambarin sarautah, wannan shafin naki ne kyauta Allah ya raya mana Safwan ya k'ara zumunci Amin â£
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.