A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 56 of 67
*PAGE 104-105*
Cikin wannan daren Suhaima bacci kasa d'aukan ta yayi ta rasa abin da yake damunta tun da Sabeer yazo ta rasa nutsuwar ta wanda har takai da yiwa kanta tambayoyi tana son Sabeer ne har yanzu, tausayin shi take ji ko kuma har yanzu zuciyar ta na son sake zama da shi a matsayin mijinta.
Ta 6angaren Sabeer kuwa kusan kwanan zaune yayi saboda zafi da cizon sauro ga duhu dulum ko'ina sai buge bugen sauro yake ya rasa inda zai sanya kanshi yaji dad'i, yayi dana sanin abin da yayiwa Suhaima sau ba iyaka yayi nadama sosai akan tsayawa binciken da bai yi ba gashi ya janyo kanshi shiga cikin tashin hankali.
Wajen k'arfe 3:25 ne gari hadari ya had'o sosai sai walk'iya da cida wato tsawa ake yi ga wata irin iska mai k'arfi da take kad'awa sosai, nan Sabeer ya shiga mugun tashin hankali sosai don yasan idan ruwa ya tsinke babu shakka sai yayi mishi jagab musamman idan mai feshi ne, kawai sai ya fashe da wani irin kukan tausayin kanshi, yana cikin kukan ne ruwa ya zuge kamar da bakin kwarya kafin Sabeer ya ankare ruwa ya jik'e shi jagab tunda kanshi har k'afafun shi.
Tak'urewa yayi waje d'aya ya had'a kai da gwiwa yana faman shashshak'ar kuka da rawar sanyi, ga ruwan sai zubo mishi yake jikin shi amman ya kasa tashi daga wajen toh idan ma ya tashi ina zai je bashi da wajen zuwa a yanzu wanda ya shige inda yake zaune.
Tun da aka fara walk'iya Suhaima ta farka tana zaune tsakiyar gado ta zabga tagumi duk ta rasa abin da yake mata dad'i, don tasan irin yanayin zauren gidan nasu ruwa zai jik'a mutum Yah Aliyu yana da niyyar gyaran shi cikin satin nan, amman tasan halin Yayanta sai yak'i gyara shi saboda Sabeer, kasa jurewa tayi ta sakko daga kan gadon ta nufi bakin window wanda za'a iya hango filin tsakar gidan zuwa cikin zaure.
Hannu ta sanya ta yaye labulen window wani irin mugun sanyi tare da feshin ruwa ne ya ratsa ta, bata hango Sabeer sosai ba saboda duhu sai kyallin farin kayanshi da ta hango, sakin labulen tayi tare da dawowa ta zauna kan gado kusan har aka gama ruwan gabannin asubah Suhaima na zaune ta kasa komawa bacci, da yake tana da toilet aciki ya sanya ta yin alwala tayi sallah tana idarwa ta fara addu'a tana cikin yi ne wani bacci mai k'arfi ya d'auke ta.
"Suhaima! Suhaima!! Ki tashi haka baccin ya isa "
Cewar Aunty Aliyah tana bubbuga k'afar ta, cikin nutsuwa take bud'e idanunta akan agogo ta d'ora eyes nata taga har 10:40 da sauri ta mik'e zaune daman haka lokaci yaja lallai tayi bacci mai nauyi.
"Aunty gaskiya nayi bacci mai nauyi haka lokaci yaja "
"Naji shirun yayi yawa har mun karya shine nazo duba ki ko lafiya?"
D'an murmishi tayi sannan tace
"Lafiya qlau Aunty kawai bacci ne "
"Kiyi sauri ki shirya kizo ki karya don ina son mu gama aiki da wuri zan fita suna da yamma "
"Laaa Aunty zan raka ki don Allah "
Cewar Suhaima cikin shagwa6a, 'yar dariya tayi kan tace
"Waiii rufa min asiri sai dai ki tambayi mijin ki tukunna "
Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin.
Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin.
Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su.
"Lek'en me kike har kina yin tuntu6e "
Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen da d'auko abin karyar ta tana cewa
"Ni babu abin da nake kallo fah Aunty "
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»
[4/18, 10:27 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
â™» *єχ¢ℓυѕινє ωÑιтєÑ'Ñ• fσÑυм*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.