Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 14 of 67

PAGE 24-25

Bayan kwanaki 2 kamar yau ranar laraba da yammaci wajen 4:30,Suhaima tana zaune a bedroom nata gyaran wardrobe d'in ta take gefe d'aya kuma Aunty Aliyah zaune gefen gadon tana mik'o wa Suhaima kayan da ta linke ita kuma tana jera su a wardrobe sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali.

"Assalamu Alaikum "
Kamar a mafarki Suhaima ta jiyo sallamar Jiddah, aikuwa da sauri ta wullar da kayan hannun ta da Aunty Aliyah ta mik'o mata, da gudu ta fita waje zuwa tsakar gidan cikin farinciki.

Jiddah tana tsaye a tsakar gidan sai murmishi take tana rarraba ido don hango ta inda Suhaima zata fito, tana hango fitowar ta a d'aki aikuwa da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su suna dariya cikin tsantsar farinciki na jin dad'in ganin juna don anjima ba'a had'u ba.

Cika junan su suka yi cikin murmishi Suhaima tace
"My besty sannun ki da zuwa"

Kunshe da marmishi kan face d'in Jiddah tace
"Yawwa tawan kwana da yawa "
Ta fad'i hakan suna kok'arin k'arasa shiga d'akin Suhaima, cikin fara'a Aunty Aliyah tace
"Lale maraba da mutanen birni Jiddah kece tafe yanzu da yamma? "

Zama Jiddah tayi akan sallayar da Suhaima ta shimfid'a mata a k'asa ganin kan gadon kaya ne akai, sannan Suhaima ta fita zuwa kitchen don samo wa Jiddah abin motsa baki.
"Aunty kam nice tafe yanzu, ina yini? "
"Lafiya qlau Jiddah, ya gida da iyayen ki? "
"Duk suna nan lafiya Aunty suna gaida ku "
(Hmmm Jiddah ta fad'i hakan ne kawai, amman gaskiyar zance iyayen ta basu san wasu su Aunty Aliyah ba, kawai suna jin tana basu labarin Suhaima duk a zaton su friend nata ne na schl, ko zuwa nan gidan nasu da take basu san da zuwan ba).

"Muna amsa wa, ya fama da hidimar biki don nasan satin da zamu shiga shine na bikin koh? "
Aunty Aliyah ta tambaye ta tana mik'ewa tsaye, cikin d'an jin kunya Jiddah tace
"Ehh Aunty haka ne, ina Yaya Aliyu? "
"Ya zagaya cikin gona ne amman yanzu zaki ga ya shigo "

Har Aunty Aliyah zata fita daga d'akin da sauri Jiddah ta tsayar da ita tare da sanya hannu cikin hang bag nata ta d'auko wani kyakkyawan invitation card guda biyar ta mik'awa Aunty Aliyah tare da cewa

"Aunty wannan card d'in d'aurin aure ne na Yaya Aliyu da na Baba Adamu ne "
"To shikenan zan bashi idan ya shigo "
D'an marairaice fuska Jiddah tayi tare da cewa
"Amman Aunty zaku je ai? "
D'an murmishi tayi tare da cewa
"Me zai hana Jiddah insha Allah zamu je, Allah ya kaimu dai lokacin da rai da lafiya "
"Amin Aunty, sannan don Allah ki dad'a tunawa Yaya Aliyu sauran kwanaki 2 d'aurin aure zan zo na tafi da Suhaima "
"Zan fad'a mishi Jiddah kuma zai barta insha Allah "
'Yar dariyar farinciki Jiddah tayi tare da cewa
"Yawwa Auntyn mu ngde "

Daidai lokacin Suhaima ta shigo d'akin hannun ta d'auke da k'aramin tire wanda ta sanya abinci aciki da kuma lemon so6o acikin k'aramin jug na roba sai cup d'in shi k'arami, ajiye wa tayi gaba Jiddah Aunty Aliyah kuma ta fita don ta barsu su yi hirar su.

Bud'e plate d'in Jiddah tayi aikuwa ta had'a ido da wani lafiyayyen dambu wanda yasha zogale da gyad'a ga ainahin man k'uli da kuma yajin da aka daka da kayan k'amshi da tafarnuwa, muk'ut Jiddah ta had'iyi yawu saboda tana son dambu sosai, dariya ce ta kubce wa Suhaima ganin yanda Jiddah take had'iyar yawu don kawai taga dambu.

Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa
"Tun da dariya kike min na fasa baki cup cakes d'in da nayi miki Aunty Aliyah da Yaya Aliyu zan bawa "

Danne dariyar ta Suhaima tayi tare da rik'o hannun Jiddah tana cewa
"Haba tawan just kin ban dariya ne ganin yanda kike had'iyar yawu but na daina"

Gid'a kai Jiddah tayi kawai saboda ta cika bakin ta da dambu ba damar tayi magana har wani lumshe ido take saboda dad'in da yayi mata, hannu Suhaima takai kan jug ta zuba mata so6on a cikin cup ta ajiye mata kusa da ita, sannan ta koma wajen wardrobe tana cigaba da gyaran kayan suna d'an hira da Jiddah jefe jefe har ta kammala cin abincin ta taya Suhaima k'arasa gyaran kayan, bayan sun gama suka fita zuwa tsakar gidan inda Aunty Aliyah da Yaya Aliyu suke zaune a saman tabarma shigowar shi kenan babu dad'e wa, nan suka gaisa da Jiddah tare da yi mata fatan alkhairin auren da zatayi tare da 'yar nasiha, sosai Jiddah taji dad'in haka tare da yi mishi godiya duk jikin ta yayi sanyi.

Suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib nan Yaya Aliyu yayi alwala ya wuce masjid, yayin da Suhaima, Jiddah da Aunty Aliyah suka yi nasu alwalan tare da gabatar da tasu sallahn.

Bayan sun idar ne da sallahr Jiddah tayi wa driver d'in ta waya, babu dad'e wa yayi sallama a kofar gidan Jiddah ta tashi taje inda yake tsaye kofar gida ta kar6i abin da ta buk'aci ya kawo mata wata 'yar bag ce black mai kyau madaidaiciya wadda zata cinye kayan mutum set 5 a ciki.

Shigowa gidan tayi tare da ajiye bag d'in gaban Suhaima tace
"Besty ga ankon ki fah ki duba ki ga yayi miki "

Sakin baki Aunty Aliyah da Suhaima suka yi suna kallon ta cike da mamaki, bayan d'azu da safe Yaya Aliyu yace gobe zai bata kud'in ankon da na gifts d'in da zata siya mata sai gashi kuma Jiddah ta zo mata dasu.

Murmishi Jiddah tayi ganin yanda suke kallon ta kafin tace
"Aunty wannan kallon fah, ni ku duba kuga yayi? "
Ta k'arasa magana cikin shagwa6a ganin sun k'i bud'e bag d'in tamkar masu jin tsoron akwai wani mugun abun aciki, ya sanya Jiddah ta janyo bag d'in kusa da ita ta bud'e, sai ga wasu tsadaddun kaya kala hud'u ta fito dasu masu matuk'ar kyau da tsada, swiss atampha, lace guda biyu da kuma wa wani material Light pink mai haske da abin nad'in kai pink shima amman mai duhu, anyi d'inkin gown ajiki yayi masifar yin kyau, sai shoes and hang bag set d'aya da su watch k'irar gucci na mata da kuma abin hannu, sark'a d'an kunne kai abubuwan kyalakyale sosai Jiddah ta zuba wa Suhaima.

Rasa bakin godiya Suhaima da Aunty Aliyah suka yi har sun bud'e baki zasu fara godiya Jiddah ta hana su dole suka hak'ura amman gaskiya Jiddah mutum ce tayi musu hallaci tayi musu abin da baza su ta6a mance wa da ita ba har abada, abun kyautata wa take musu tamkar wasu shak'ik'an 'yan uwanta na jini, babu tsangwama ko kyankyamin su da take duba daga inda ta fito, su kansu sun san Jiddah iyayen ta masu kud'i ne sosai bana wasa ba.

A haka Yaya Aliyu ya shigo ya same su sam ya nuna wa Jiddah bai ji dad'in abin da tayi ba da ta bari shi zai bata kud'i taje ta siyowa Suhaima kayayyakin ko nawa ne, nan Jiddah ta nuna mishi ita fah yanda ta d'auki Suhaima tamkar 'yar uwarta ta jini zata iya yi mata komai har idan tana dashi dole yasa Yaya Aliyu hak'ura yayi mata godiya daga k'arshe kuma ta tashi zata tafi har bakin motar su Suhaima da Yaya Aliyu suka rakata suna godiya tana nuna musu batasan godiyar nan, anan Aliyu yayi mata alk'awarin zuwa ta tafi da Suhaima idan ta dawo sosai Jiddah da Suhaima suka ji dad'in hakan, Kafin suyi sallama kuma ta shiga motar driver yaja suka tafi suna masu d'agawa junan su hannu har sai da motar ta k'ule tukunna Yaya Aliyu ya rik'o hannun Suhaima suka wuce gida.

****** ********** ********

Kwance yake saman kujera cikin garden ya zurfafa a cikin tunanin yarinyar da suka had'u, tsawon wajen kwanaki 5 da had'uwar su amman ya kasa manta ta koyaushe cikin tuna beautiful Face nata yake, cikin mafarkin shi da farke yake tunanin yarinyar da baisan sunan ta had'uwar su ta farko da junan su.

Shi yasan ba sonta yake ba duk da bai ta6a son wata mace ba, but why ya damu da ita har haka, duk san da ya tuna ta yana jin bugun heart nashi na k'ara k'arfi yana son tunano muryar ta da kyakkyawar surar ta yana son Allah ya k'ara had'a su koda sau d'aya ne ya ganta ya sake jin daddad'ar muryar ta.

Sake gyara kwanciyar yayi yana mai lumshe ido hango kyakkyawar face nata yayi lokacin da take mishi tsiwa tare da yanda cute lips nata suke motsawa kamar a lokacin take mishi tsiwar haka yake ji.

Ji yake bazai iya jure ba zumbur ya mik'e tsaye tare da nufar side d'in su da saurin shi kamar ba Sabeer ba, yana tashi a wajen Fadilah ta fito daga ma6oyarta ta zauna kan kujerar da ya tashi tana mai shinshina kan kujarer tamkar Sabeer ne zaune a wajen tsabar fitinar ta, d'ago eye's nata tayi wanda suka yi ja cikin wata irin murya tace
"I luv U Sabeer, ina maka son da bazan iya zuba ido ka so wata mace a rayuwar ka ba dole nasan ta yanda zanyi na karkato hankalin ka gare ni "
Tana gama fad'in haka ta tashi tare da wuce wa side d'in su Sabeer...

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝

Written by
Aishat A Muh'd

â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.