A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 45 of 67
*PAGE 83-84*
Ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tare da juya kanta, rungume ta yayi ta baya ya sanya kanshi cikin gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar kamshin daddad'an perfumes d'in ta saukar d'umin numfashinshi a wuyanta shi ya saukar mata da wani irin kasala, hannun shi ya sanya yana shafa dogon hannun ta daga kafad'a zuwa 'yan yatsun hannun, kasa jure abin da yake mata tayi sai kawai ta juyo tare da fad'awa kan kirjin shi tsam ya rungume ta ajikin shi yana saukar da ajiyar zuciya, suna nan tsaye wajen 5 minutes ahaka kafin kuma ya bud'e baki yace
"Baby muje kici abinci sai kisha magani "
Hannun ta ya rik'o zuwa parlour har kan dinning table ya zaunar da ita kan kujera, sannan shima ya zauna yana zuba musu abinci, kasa barinshi tayi da ya zuba musu ta kar6i serving spoon tana zuba musu.
Abaki suka dunga bawa junan su har suka k'oshe sannan ta tattara kayan ta kai kitchen, ta dawo ta gyara dinning table d'in, zama suka yi a parlour suna kallo tare da ta6a 'yar soyayya.
Sai da Sabeer ya bawa Suhaima hutun kwanaki biyu sannan aka d'ora daga inda aka tsaya, soyayya, kulawa da duk wata kauna suke nuna wa junan su, cikin farinciki da kwanciyar hankali suke abin su, babu mai zuwa gidan sai Jiddah ce ke lek'o su, sai dai waya da take yi dasu Yaya Aliyu kullum Sabeer kuwa yana kok'arin zuwa gida gaida iyayen shi, amarcin su suke sha yanda suke so babu mai tak'ura musu ko house girl basu da ita Suhaima ta hana Jiddah ta kawo mata tace ba yanzu ba.
Akullum cikin nuna wa junan su so suke biyayya sosai da kyautatawa Suhaima ke yiwa Sabeer yayin da shima yana kok'arin wajen sanya ta farinciki koyaushe, idan ka shiga gidan su kuwa sai ya birge ka saboda tsananin yanda suke kula da junan su.
Motarta tuni Jiddah ta aiko mata da ita gashi Sabeer ma ya bata kyauta ta mota mai matuk'ar kyau da tsada da sabuwar tsadaddiyar phone, sosai Suhaima tayi mishi godiya ta nuna mishi dad'in da taji addu'a sosai yasha ta daga bakin ta, gashi yana koya mata driving duk weekend da yamma zasu fita yana koya mata, yanzu matsalar ta d'aya shine ta cigaba da karatu amman tun da tayi mishi maganar sau d'aya ya nuna ba yanzu ta hak'ura duk da tsananin son da take yiwa karatun ta cigaba da farantawa mijinta rai ta barwa Allah za6in alkhairi akan makaranta.
_*After 3 Month's*_
Zuwa wannan lokacin idan kaga Sabeer da Suhaima sai kayi mamaki sun k'ara wani kyau musamman Suhaima ta k'ara cika sosai tayi 'yar kiba kad'an, bata fita ko'ina sai zaman gida kullum sau d'aya ta sake jarraba zuwa gidan su Sabeer amman har ta karaci zaman ta babu wanda yace mata ci kanki har gwara lokacin da Daddy ya dawo ya zauna sun d'an ta6a hira dashi amman ko a fuska bata nunawa Sabeer jin haushin abin da suka yi mata, Sabeer a lokacin tuni ya fara aiki da company d'in shi da Daddy ya bashi kyauta.
Zaune suke a garden da wani yammaci lokacin damina ne garin yayi luf luf dashi sai iska mai dad'i da take kad'awa mai ratsa jiki da sanya mutum nishad'i.
Suhaima tana sanye da wani wandon jeans iyakar shi rabin cinyar ta blue sai half vest white, yayin da Sabeer kuma yake sanye cikin 3quater kawai suna zaune kan wani babban carpet ga kayan fruits da juice da ruwa a gefen su.
Sabeer ne yake danna laptop d'in shi da hannu d'aya, d'ayan hannun kuma yana rungume da Suhaima ta gefen shi, cikin shagwa6a ta bud'e baki tace
"Ni Allah ka bar aikin nan kazo ka goya ni idan ba haka ba zanyi maka kuka "
D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai wani turo baki take murmishi yayi tare da jan hancin ta yace
"Oh Baby rigima naji zan goya ki amman kiyi min afuwa na k'arasa aikin nan please "
D'aga kanta tayi, da sauri ya rik'o d'ayan hannunta yace
"Amman ban da kuka please"
D'an murmishi tayi sannan tace
"Toh bazan yi ba "
"Yawwa 'yammata na "
Cikin 10 minute's ya k'arasa aikin tare da rufe laptop d'in ya kallo ta cikin murmishi sannan ya sunkuya yace
"Baby taho na gama "
Cikin sauri ta taso tare da d'anewa bayan shi, yatsina fuska yayi sannan yace
"Wash! Bayana Baby kin k'ara nauyi zaki karya min baya "
Turo baki tayi cikin shagwa6a tace
"Ni.... Ni Allah ban wani k'ara nauyi ba kai ne ka dad'a zama babba "
"A'a Baby fad'i gaskiya "
"Toh bakai ne kake d'ura min abinci ba da yawa "
Dariya yayi yana cewa "a haba Baby fad'i gaskiya dai "
Hannun ta ta sanya tare da d'an mintsinin shi a damtsen hannun shi, wata 'yar k'ara ya saki
"Laaa Baby kika mintsine ne, aikuwa sai na rama "
Kafin ta ankara ya kwantar da ita akan carpet ya bi jikinta ya kwanta gaba d'aya sai ya saukar mata da nauyin shi , dakyar take jan numfashi tace
"Wayyo don Allah ka d'aga ni dear "
Yana dariya yace
"Nak'i wayon yarinya sai na rama ko kuma yau da dare na hanaki bacci kin yarda "
Da sauri ta d'aga kanta dariya ya sake yi sannan ya d'aga ta, hannun ta ta zube su kan carpet tana sauke numfashi, janyo ta yayi kan k'afafun shi tare da had'e bakin su waje d'aya wani salo na daban yake nuna mata itama babu 6ata lokaci take mayar mishi da martani.
Sunyi nisa cikin wannan yanayin ne yaji wayar shi na k'ara, ba don yaso ba ya d'auki wayar yana jan tsaki don an katse mishi jin dad'in shi.
"Hello Yaya na haihu "
"What! Da gaske kike? "
Cewar Sabeer yana tambayar Jiddah, cikin dariya tace
"Allah Yaya da gaske nake an samu Baby girl"
"Masha Allah na tayaki murna 'yar kanwata Allah ya raya "
"Yaya ka fad'awa Suhaima ita na fara kira wayan ba'a d'auka ba"
"Okay babu damuwa "
"Toh yaushe zaka kawo min Besty tun da kuka yi aure bata zo ba fah?"
"Jiddah surutu huh, yanzu kina buk'atar hutu ne kije ki huta zan kawo ta ne"
Cikin shagwa6a tace
"Yaya ka kawo min ita gobe don Allah idan zaka fita office "
"Okay naji "
Nan ya kashe wayar tashi, kallon Suhaima yayi wadda take kallon shi tun fara wayar shi ya ce
"Albishirin ki Baby "
Matsowa kusa dashi tayi sosai tace
"Goro fari k'al dear "
"Mene tukuici na idan na fad'a "
D'an dariya tayi kad'an sannan tace
"Ka fad'i duk abin da kake so zanyi maka "
"Jiddah ta haihu ansamu Baby girl "
Wani ihun murna ta saki tare da rungume shi tana dariyar farinciki kallonta yake duk tabi ta birkitashi ta kashe mishi jiki.
"Dear ka tashi mu tafi ganin Baby please "
"No Baby yanzu mangarib ta kusa ki bari sai gobe don gaskiya yanzu kin gama birkita ni tashi mu tafi ciki before mangarib tayi "
Sanin halin shi ya sanya ta biye mishi suka tafi, sai da suka sha soyayyar su tukunna sukayi wanka tare da yin alwala ya tafi masjid ita kuma ta shige bedroom nata don yin sallah, bayan ta idar da sallahr ne ta samu damar kiran Jiddah don yi mata barka kafin tazo sunsha hirarar su sosai kafin suyi sallama da juna.
_*Washe gari*_
Tun asuba da tayi sallah take faman gyaran aikin gidan bayan ta gama ta had'a breakfast sannan ta jera saman dining table, bedroom ta wuce ta cire kayanta ta d'aura towel ta shige bathroom don yin wanka, acan Sabeer ya same ta suka sha soyayya then sukayi wanka suka fito shirya junan su suka yi, yana sanye cikin wata blue na suits sai necktie black da black shoes yayi matuk'ar yin kyau.
Yayin da Suhaima kuma ta shirya cikin wani swiss lace brown da touch na red d'in flower's tayi kyau sosai, fita suka yi zuwa dinning table agurguje suka yi breakfast, sannan ta wuce d'aki ta d'auko mayafi babba red colour ta yafa sai flat shoes da handbag redred in colour perfumes masu sanyin k'amshi ta sanya sannan ta fito.
"Wow! Baby na kinyi kyau sosai "
Cewar Sabeer yana rungume ta ajikin shi.
"Nagode Dear kai ma kayi min kyau "
Kissing ya bata goshi sannan ya rik'o hannun ta suka fito zuwa compound.
Suna zaune bayan mota driver nayin tuk'i suka fita daga gidan hanyar gidan Jiddah suka nufa.
"Baby nima yaushe zaki haifa mana Baby? "
Ya fad'a yana shafa flat tummy d'in ta, kunya ce ta kama Suhaima dakyar ta iyacewa
"Duk lokacin da Allah ya bani sai na haifa mana "
"Haba Baby ina kula fah dake tun daga kika zo gidan nan baki yi period ba yau 3 Month's har da 'yan kwanaki da auren mu, ai nasan da ajiyata anan shiru kawai nayi miki "
D'an tunani ta fad'a yi tabbas rabon ta da yin period tun lokacin sauran 2 week's bikin su amman koda tana gida sai tayi 2 months bata ga period yazo mata shiyasa idan ta tashi yi take fama da menstruation pain mai tsananin zafi.
"Kinyi shiru Baby ko ba haka bane? "
Tana shirin yin magana suka shiga gidan Jiddah don haka sai ta mayar da bakin ta tayi shiru.
Tare suka fito daga motar hannun su sark'e cikin na junan su, suna kok'arin shiga parlour ne aka bud'e kofa tare da fitowa, sai da gaban Suhaima yayi mugun fad'uwa ganin Mumyn Sabeer ce wadda ta jima da zuwa duba Jiddah da Babyn ta, idanun ta akan hannayen Sabeer da Suhaima fuskar ta sam babu alamar fara'a.
Jikin Suhaima na rawa take kok'arin kwace hannun ta amman Sabeer ya rik'e k'am yak'i ya cikata don haka kawai ta tsugunna tana gaida Mumy, bata amsa ba sai kau da kai da tayi.
Sakin hannun Suhaima yayi bugging d'in Mumy tare da bata peck a cheek nata, cikin sanyin jiki Suhaima ta mik'e daga tsugunnan da tayi.
Kallon ta Mumy take yi sosai wanda ya sanya Suhaima k'ara rikicewa gabanta banda fad'uwa babu abin da yake, wani irin fad'uwa gaban Mumy yayi masifar yi a lokaci d'aya da ta hango wasu canji atattare da Suhaima wanda tasan tabbas sai mace mai ciki ne take canjawa irin haka abin ka da likita, wani mugun gumi taji ya karyo mata tun daga saman gashin kanta zuwa fuskarta da jikinta.
Zame hannun ta tayi daga na Sabeer ta fara tafiya zuwa wajen motar ta hankalin ta a masifar tashe duk yanda zata yi sai tayi don ganin ba'a haifi wannan cikin ba, don bazata ta6a had'a zuri'a da 'yar kauye ba abin da bazai ta6a yiwuwa ba dole tasan yanda zatayi cikin ya fita idan yaso duk lokacin da ta samu ciki sai tana zubar dashi.
Tasan halin Sabeer yanda yake masifar son yara dole ya rabu da ita daga lokacin da ya gane ita take zubar mishi da ciki duk da son da yake mata kuwa a wannan lokacin ne zata aura mishi yarinyar da take son ya aura wannan dabarar ta shine kawai zai kawo k'arshen zaman Sabeer da Suhaima, wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki tare da shiga mota tabar gidan zuciyar ta fes take jin ta gani take kamar ma Sabeer ya rabu da matsiyaciyar yarinyar nan..........
_To fah reader's kunji tunanin Dr Faridah ko zata yi nasara akan Suhaima ta rabata da Sabeer, ina jiran comments naku yanzu labari zai fara, ƙų Â¢Ä±É Ä…áƒªÄ… É–Ä… ცıŋą ɖơŋ Êıŋ ყąŋɖą ʑąɬą ƙąʂąŋ¢ɛ_.
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»
[4/9, 6:30 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.