Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 67

PAGE 30-31

Tashi Jiddah tayi tsaye tare da d'aukan bag d'in ta gida take son tafiya saboda yau ne ranar kamu sai faman kiran ta ake a waya ana tambayar ta inda take, kallon ta Aliyu da Suhaima suka yi, ita ma kallon su tayi tare da cewa

"Yaya Aliyu zan tafi gida ana nema na, zan dawo gobe da safe na mayar da ku gida Allah ya bawa Aunty Aliyah lafiya "

Kallon ta Aliyu yake gaba d'aya ya rasa ma mai zai ce mata dakyar ya iya bud'e bakin shi yace
"Amin Jiddah nagode sosai da karamcin ki gare mu, nasan kina son tafiya da Suhaima koh? "

D'an murmishi tayi tare da cewa
"Haba Yaya Aliyu taya zan tafi da ita bayan itace ke kula da Aunty babu komai wlh nasan lalura ce taja hakan "

Girgiza Aliyu yayi kafin yace
"Idan lokaci bai k'ure ba ki d'auki Suhaima kuje gida ta d'ebi kayan da zata yi amfani dasu, sai ku taho da Babaa Lantana ta zauna da mu anan zuwa gobe "

Duk da Jiddah taji dad'in abin da Aliyu yace mata amman sai da ta sake cewa
"Ka barshi Yaya yanzu babu lokaci sauri nake sai kirana ake lokacin kamu yayi amman insha Allah gobe zan dawo sai mu tafi tare "

"Shikenan Jiddah Allah ya biya ki, Allah ya sanya alkhairi "
"Amin Yaya, amman godiyar ta isa haka "

Murmishi suka yiwa junan su kafin Suhaima da Aliyu su tashi rakiyar Jiddah har zuwa compound d'in hospital d'in suka sake yin sallama kafin ta shiga mota driver yaja motar su tafi, Aliyu da Suhaima suka dawo cikin room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah har yanzu dai bacci take bata farka ba zama suka yi jigum jigum, sai jefi jefi suke d'an ta6a hira sannan nurses suna shigowa duba Aliyah, da dare sai da Jiddah ta aiko driven da suka zo tare da takeaway na abinci sai kayan tea acikin leda bak'a 'yar babba, sosai Aliyu da Suhaima suka ji dad'in haka daman a lokacin yake tunanin fita neman masu abin da zasu ci sai gashi, nan Aliyu ya sake jinjina k'aunar da Jiddah take yiwa Suhaima dasu kansu basu da abin da zasu biyata abin da tayi musu sai dai addu'ar fatan alkhairi.

Washe gari da safe Aliyah ta tashi jikin ta da sauk'i sosai ta samu k'arfin jikin ta, tana cin abinci sai dai wani ya zauna wani ya fito amman sosai sun ga sauk'i fiye da lokacin da suka zo jiya tun da tana tashi da kanta ba tare da an taimaka mata ba.

Ganin haka ya sanya likita basu sallama tare da rubuta mata maganin da zata nayin amfani dashi, sannan ya fad'a musu idan taji wani canjin yanayi a jikinta ta dawo hospital d'in tun da file Jiddah ta sanya aka bud'e mata.

K'arfe 11:25 na safe sai ga Jiddah ta shigo room d'in sosai taji dad'in ganin Aunty Aliyah jikin da sauk'i, bayan an gaisa kuma suka fito daga cikin asibitin zuwa inda motar da Jiddah tazo da ita, yau babu driver ita d'aya tazo da kanta tayi driving, bayan sun shiga motar ne suka d'auki hanyar zuwa k'auyen nasu.

Bayan sun isa gida ne a gurguje Suhaima ta gyara gidan tsaf tana kok'arin d'ora girki Babaa Lantana ta shigo gidan ta kar6in aikin tare da ce mata ta shirya su tafi, aikuwa nan ta shiga wanka bayan ta fito ne ta shirya jikin ta a lokacin Jiddah har ta gama had'a mata kaya a cikin bag d'in da ta bata suka fito zuwa tsakar gidan.

Inda Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suke zaune zama suka yi suma a k'asan tabarmar da suke kai, nasiha sosai mai ratsa jiki Yaya Aliyu yayi wa Jiddah na irin rayuwar da zata shiga nan da kwana d'aya, haka Babaa Lantana ma tayi mata nasiha sosai Aunty Aliyah ce babu k'arfin yin magana sai murmishi da take mata cikin zuciyar ta tana mata addu'a.

Daga k'arshe Jiddah ta fito daga gidan da bag d'in Suhaima a hannun ta, saboda taga alamar kamar akwai abin da suke son fad'a wa Suhaima, aikuwa tana fita Yaya Aliyu da Babaa Lantana suka yi mata nasiha na ta tsare mutunci kanta ban da kula samari da rawar kai komai ta gani ta kawar da kai tana yin alkunya kodan saboda Jiddah sannan Yaya Aliyu daga k'arshe ya gargad'i ta da babbar murya kada tayi shiga matsatstsiya na sutura, ta suturce jikin ta matsayin ta na 'ya mace.

Bayan sun gama mata nasihar ne Yaya Aliyu ya bawa Suhaima kud'i masu dama sannan yace
"Wannan kud'in ki nemi abin da zaki siyawa Jiddah gift's dashi ki rage wasu kuma don ki rik'e a hannun ki "

Aunty Aliyah cikin muryar marasa lafiya tayi wa Suhaima magana da ta shiga d'akin ta ta d'auko mata wani box cikin drower d'in gadon ta, nan Suhaima taje ta d'auko ta mik'a mata kar6a tayi ta bud'e sai ga wata sark'a, d'an kunne, zobe da warwaro guda uku sai sark'ar k'afa masu kyau sai kyalli suke da d'aukan ido farare ne.

"Ki bawa Jiddah kice mata ba yawa tayi hak'uri "
Cewar Aunty Aliyah kenan cikin sanyin murya, rik'e hannun ta Suhaima tayi tana murmishi tace
"Toh Aunty zan bata insha Allah "

Daga haka Suhaima ta tashi haka ma Yaya Aliyu suka fito zuwa nan kofar gida inda Jiddah take zaune cikin mota, shiga seat d'in gaba Suhaima tayi tare da rufe k'ofa, nan Jiddah tayi wa motar key suka fara tafiya sannan Yaya Aliyu ya buga machine d'in shi yana binsu a baya don ganin gidan su Jiddah saboda zuwa d'auko Suhaima.

"Malama da haka zamu tafi kina min hawaye salon ace na sato ki "
Fad'in Jiddah cikin sigar tsokana,
"Kewar gida na fara yi Jiddah tun da nake ban ta6a zuwa wani wajen kwana ba sai yau"
Cewar Suhaima tana kwantar da kanta a jikin kujera.
"Lallai da drama duk lokacin da kika yi aure za'a kai ki gidan miji kenan, tun da shi fatan zama na har abada ake "
D'an zaro ido Suhaima tayi tare da cewa
"Tabbb ni fah auren ma baya gaba na Jiddah, har yanzu ban ta6a tsayawa da wani ba da sunan zance ba "
"Lallai yarinya da sauran ki kina tunanin Yaya Aliyu zasu zuba miki ido babu aure? "
D'an marairaice fuska Suhaima tayi tana cewa
"Ni fah da za'a bi tason ra'ayi na karatu zan cigaba da yi wlh tun da gaba d'aya ni yarinya ce nawa na ke "

Hararar wasa Jiddah tayi wa Suhaima kafin tace
"Ai yanzu tsab za'a yi miki aure ki zauna akwai wad'anda basu kai ki ba ake musu su zauna lafiya ma "

D'an shiru suka yi na 'yan minute's kafin Jiddah tace
"Ni kuwa Suhaima wane irin Namiji kike son aura i mean halayyar shi, yanayin shi and everything da kike son mijin ki ya kasance? "

Shiru Suhaima tayi na tunani kafin ta sauke ajiyar numfashi tace
"Ni a tsarin rayuwa ta bana son auren miji mai kudi da yawa nafi son auren talaka dai dai ni wanda bazai wulak'anta ni ba da 'yan uwana ba ko dangin shi su na wulakanta mu ba, kuma bana son auren miji mai irin kyan nan da yawa ina da kishi wallahi bazan iya jure ganin 'yammata suna kai mishi farmaki ba, sannan bana son mai saurin fushi,ina son kuma mijina ya kasance mai ilimi both side addini da boko kuma...... "

"Kaiii Suhaima idan kuma Allah ya baki handsome mai kyau da kudi fah, kamar yanda kike da kyau ke ma? "

"Hmmm bana fatan haka Jiddah na fison talaka d'an uwana, ni koda misali wani mai kud'in zaice yana sona bazan amince mishi ba wulak'anci zan tayi mishi har ya hak'ura ya bar ni, nasan ma bazai jure wulakanci ba zai rabu da ni "

Dariya sosai Jiddah tayi kafin tace
"Koda wanda kika watsa mishi ruwa ne idan ya dawo yace yana son ki fah ya zaki yi? "

"Tabbb ai korar shi zanyi balle nasan bazan sake ganin shi ba har abada ma"

Cikin zolaya Jiddah tace
"Kika sani ko shine mijin naki Allah ya kawo miki "
Dukan wasa Suhaima ta kaiwa Jiddah da sauri ta goce tana dariya tare da cewa
"Haba Besty daga wasa sai duka kin mance ni amarya ce zan had'a ki da my sweet darling fah"

D'an murmishi Suhaima tayi kawai ta d'auki phone d'in Jiddah tana kallon pic's d'in ciki, da haka har suka k'arasa gidan su Jiddah amman daga waje tayi parking bata shiga cikin gidan ba, Wow! abin da Suhaima tace kenan ganin irin unguwar su Jiddah ta manyan masu kud'i ce ganin gidan su Jiddah kuwa sai da gaban Suhaima da na Yaya Aliyu ya fad'i.

Anya basu yi gangancin sake wa da Jiddah ba irin wannan k'aton gidan daga ni Iyayen ta ba k'aramin masu kud'i bane, lokaci d'aya jikin su yayi sanyi sosai, nan Jiddah ta k'arasa wajen Yaya Aliyu suka yi sallama bayan ta tabbatar mishi da jibi da yamma yazo d'aukan Suhaima idan yazo ya kirawo ta a waya daga haka suka yi sallama ya buga machine d'in shi ya tafi jiki a sanyaye yana dana sanin sakewa da Jiddah da suka yi har haka, kada a wulak'anta mishi k'anwa ko kuma su bud'e mata ido da rayuwa amman da ya tuna irin tarbiyyar Jiddah sai ya d'an ji sanyi cikin zuciyar shi but still jikin shi a sanyay dakyar yake tuk'a machine d'in yana addu'a cikin zuciyar shi Allah ya tsare mishi Suhaima har taje ta dawo lafiya...

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝

Written by
Aishat A Muh'd

â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Dis page is dedicated to
Ayusher Ilias my Namecy
Biebie dee tawa
My Zeee yabour
Asy khaleel, kirkin ku daban ne ina yin ku sosai sister's Allah ya bar zumunci a tsakanin mu ❣

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.