Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 67

PAGE 34-35

Hannun ta d'auke da cup wanda coffee ne aciki ta shigo cikin bedroom d'in turus ta tsaya ganin shi a zaune ya zabga tagumi, ta rasa abin da yake damun d'an nata gaba d'aya ya canja tun ranar da ya doki Fadilah, ajiye cup d'in tayi saman center table d'in k'arasa wa inda yake tayi har zuwa lokacin Sabeer baisan da zuwan Mumyn nashi kusa dashi ba, girgiza kawai tayi tana kallon shi kafin ta sanya hannun ta d'ora shi tayi saman kafad'ar shi tace

"Son tunanin me kake? Me yake damun ka ne kwananan "
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Nothing Mumy "
Zama tayi kusa dashi tana mai kamo hannun shi cikin nata kallon shi take cikin kulawa tace
"Son baka da wanda zaka fad'a wa damuwar ka duk duniyar nan sama da ni, ka sanar dani ko zan iya baka shawara please "

Cikin gajiya da maganar Mumy yace
"Nace miki babu komai ki rabu da ni please "
Ya k'arasa maganar da d'an tsawa kad'an.
"Shikenan Son koma mene Allah ya yaye maka "
Cikin zuciyar shi ya amsa da Amin.
"Ga coffee kasa na lura tun breakfast baka k'ara cin wani abin ba, idan ka gama ka shirya ka kayan ka saman bed kasan yau ne dinner na sister d'in ka Jiddah kuma kowa na family zai je don haka ina buk'atar ganin ka please Son "

Shiru yayi mata bai kulata ba itama bata sake bi ta kanshi ba ta wuce ta fita don idan da sabo ta saba da shariyar Sabeer wani lokacin musamman idan yana cikin damuwa bai fiye son magana ba.

Mumy tana fita ya zame ya kwanta kan sofa yayi matashin kai da hannayen shi, idanun shi lumshe su yana tunanin Suhaima sosai yake mamakin yanda yarinyar ta tsaya mishi cikin zuciyar shi, shi baisan so ba amman da alama ya fad'a son wannan yarinyar, dummm gaban shi ya fad'i da ya tuna yanda 'yan uwanshi da iyayen shi suka tsani talaka balle ita a k'auye ma take, yanzu shi ya zai yi zuwan shi wajen uku k'auyen ko mai kama da ita bai gani ba ya rasa yanda zai yi.

Son da yake mata bazai iya hak'ura da ita dole ne yasan yanda zai 6ullowa al'amarin, bayan bikin Jiddah dole ya koma k'auyen ya neme ta, zai nuna mata so sannan zai bawa iyayen ta kud'i sosai ya basu gida da mota da jari sosai yanda bazai samu matsala ba ta 6angaren iyayen shi idan suka ga iyayen ta masu kud'i ne, wani murmishi ya saki na kamar wanda ya samu nasara ma sai lokacin hankalin shi ya kwanta, kiran sallahr mangarib ne ya katse mishi tunani, toilet ya shiga yayi alwala ya fito kai tsaye masallaci ya wuce.

Babban hall ne wanda ya k'ayatu da decorations masu kyau da k'ayatuwa wajen ya tsaru yayi kyau sosai, ga haske tamkar ba dare ba sanyi Ac ta ko'ina ban da k'amshin tsadaddun turaren jikin manyan masu kud'in da suke zaune a wajen kamar anyi 6arin turare a wajen.

Manyan hamshak'an mutane ne masu kud'i sosai a wajen ansha kwalliya ta kece raini ga tsadaddun sutturu da aka sanya mutane suna zazzaune a wajen da aka tanadar musu, slow music ne ke tashi kawai a wajen duk mutane an hallara, family d'in Jiddah gasu nan ga friends na iyaye dana amarya sai na yayyanin amarya dana k'anen ta abin dai ya tsaru gwanin sha'awa kowanne da kalar ankwan su, haka 6angaren dangin ango gasu nan da nasu ankon daban suma sunyi kyau sosai.

Amarya da ango ake jiran shigowar su babu dad'e wa mc ya fara sanar wa shigowar ango da amarya kowa ya nutsu ya zubawa kofar shigowa kallo don ganin shigowar amarya da ango.

Cikin takun k'asaita da nutsuwa Jiddah da angon ta khaleel suka shigo hannun su sark'e da junan su, Jiddah tana sanye da wata farar gown har tana jan k'asa sai ash head da ta sanya yana da kwalliyar flowers silver ajiki pose da hill nata dukka ash ne masu kwalliyar silver ajiki tayi kyau sosai abin ta, haka angon ma Khaleel yasha shadda ash colour sun yi matukar kyau da dacewa da junan su, sai watsa musu wasu fararen furanni da red ake yi.

Bayan su kuma Suhaima ce tasha light pink na gown sai head nata pink mai d'an duhu tasha makeup tayi matukar kyau tamkar ba Suhaima ba, ba wanda zai ganta ya zaci daga k'auye ta fito tama fi 'yan birnin kyau a wajen don ba k'aramin haskawa tayi ba tamkar itace ma amaryar ba Jiddah, don kallo dawowa yayi kanta abin da yasa duk ta dibirbice ta rasa inda zata yi saboda idanun mutanen da suke kanta sai murmishin yak'e take.

Da haka ta samu waje ta zauna bayan ango da amarya sun wuce wajen zaman su, nan aka fara gabatar da dinner cikin nutsuwa da wayewa, gaba d'aya Suhaima a tak'ure take saboda bata saba zuwa irin wad'annan wuraren ba, har zuwa lokacin da amarya da ango suka fito domin taka rawa nan 'yan uwa da abokanan arzik'i suka fito domin yi musu lik'i.

Dr Faridah ce ta fito filin wajen nan mutane suka bata hanya ta wuce zuwa inda su Jiddah suke tsaye ita da angonta suna taka rawa a nutse, bag d'in hannun ta ta bud'e ta fito da bandir d'in 1k ta fara watsa musu tamkar bata san zafin kud'i ba sai da ta gaji tukunna ta bar wajen.

D'ago kan Suhaima yayi dai dai da barin Dr Faridah wajen aikuwa suka had'a ido wani irin bugawa zuciyar Suhaima tayi da k'arfin gaske haka ma a 6angaren Dr Faridah d same abin da Suhaima taji haka taji itama, amman sai ta kawar da kanta daga barin kallon ta cikin zuciyar tana tunanin irin wannan kyan na yarinyar da bata ta6a ganin ta ba sai yau, gashi ta d'an birgeta kad'an da taga duk da kyan da take dashi but bata da rawar kai irin na 'yammatan da suka waye sosai kafin kuma watsar da tunanin ganin Suhaima ta cigaba da sha'anin gaban ta.

Har zuwa lokacin da aka buk'aci amarya da ango su yanka wedding cake nasu, nan 'yan uwan amarya da ango 'yan kad'an suka rakasu wurin cake d'in babu 6ata lokaci suka yanka Khaleel ya bawa Jiddah a baki itama ta yanko tare da d'an tsugunna wa kad'an ta bashi nan aka hau tafi.

Suhaima ba k'aramin birgeta suka yi ba sai sakin murmishi take ita kad'ai, zuwa yanzu ta d'an saki jikin ta da zaman wajen, amman sam duk da haka har yanzu bata ji sha'awar ta auri irin d'aya daga cikin wad'annan masu kud'in ba, tana kallon yanda su Zahra da sauran sisters d'in Jiddah suke wurgo mata harara tsanarta k'arara akan fuskar su, d'aga kafad'ar ta tayi alamar ko a jikin ta, tana fatan jibi iyanzu tana k'auyen su cikin gidan su, sai su harari wata ba ita ba.

Ana gaf da tashi a wurin Sabeer ya shigo cikin hall yana sanye cikin wata light blue sky na shadda tsadaddiya har da hula akanshi, d'inkin shi irin wanda matasan yanzu suke yin shi ba k'aramin kyau yayi ba, a daidai lokacin kuma Suhaima ta taso zata fita daga hall d'in don amsa kiran wayar da Yaya Aliyu yake yiwa Jiddah.

Karo suka yi da junan su inda Suhaima ta bige kanta da kafad'ar shi, dafe goshin tayi tare da yamutsa fuska tace
"Washh Allah na "

D'ago kan da zata yi ta bashi hak'uri suka had'a ido da junan su, kallon second 3 Suhaima tayi mishi ta gane ko wane tuni jikin ta ya fara rawa tsoro ya kamata kada ya d'auki fansar abin da tayi mishi a wajen da batasa kowa ba sai Jiddah, shima Sabeer kallon ta yake cikin mamakin me ya kawo ta nan kuma don ko acikin mafarki ya ganta sai ya gane ta wane ya kawo ta wajen bikin k'anwar shi? Ta dalilin wata zo nan? wad'annan tambayoyin ya yiwa kanshi a lokacin d'aya.

Ganin ya zuba ido yana kallon ta yasa ta saurin fita daga hall d'in, cikin zafin nama ya bita yana cewa
"Hey tsaya mana kece wan...."
Kafin ya k'arasa maganar tashi yaga wayam babu kowa a wajen, ta gudu kenan abin da zuciyar shi ta fad'a ba guduwa tayi ba 6oya tayi, ina ta 6uya kuma?.

Daga d'an nesa kad'an na hango Suhaima tana lek'en shi jikin ta na 6ari zuciyar ta na bugawa da k'arfi, ganin yana dube dube a wurin ya sake fad'ar mata da gaba, bata k'ara rud'ewa ba sai da taga ya nufo inda take.

Yana daf da k'arasa wa inda take ne yaji an rik'o hannun shi da sauri ya juya ga ashe Mumy ce da tarin kannen shi, wayyo Allah ya furta cikin zuciyar shi don yasan yanzu yaran nan zasu sa mishi ciwon kai da hayaniyar su
"Yah Sabeer kazo mu d'auki pic's please "
Cewar wata sistern shi zai yi magana kenan Mumy tayi musu magana da ido, dariya suka yi don su fahimci me take nufi, aikuwa hannun shi suka kama zuwa cikin hall d'in bashi da yanda zaiyi ya bisu yana tafiya yana dube dube har sai da suka wuce ciki sam ranshi babu dad'i ba haka yaso ba yaso ta tsaya su yi magana ta fahimta amman dole ya binciko wanda yayi inviting d'in ta zuwa wajen nan.

Fitowa Suhaima tayi daga inda ta 6uya tana sauke ajiyar zuciya har da gumi ta had'a duk tayi wani iri kallo d'aya mutum zai mata yasan a firgice take, zama tayi a gefen wasu flower's tana sauke numfashi....

Aishat A Muh'd 🤸🏻‍♀
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI

Written by
Aishat A Muh'd

â™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.