A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 15 of 67
PAGE 26-27
Yana k'arasa wa part d'in su bedroom nashi ya shiga yayi wanka tare da shirya cikin wani blue jeans da T-shirt red yayi kyau cikin sauri sauri ya fesa perfumes tare da d'aukan phone's nashi ya fito zuwa parlour.
Akan dinning table ya hango Mumy, Daddy da Fadilah suna yin lunch abin su, ganin shi da Mumy tayi yasa ta cewa
"Son k'araso kaci abinci "
Yana nufar hanyar fita a parlourn yake cewa
"Mumy sauri nake zan fita sai na dawo "
Kafin wani ya k'ara magana ya fice da sauri, da ido suka raka shi cikin zuciyar Mumy tana mai mamakin abin da ya canja mata yaro lokaci d'aya don da ba haka Sabeer yake mata ba.
Yana fitowa harabar gidan ya hango driver da hannu yayi mishi alamar yazo da sauri driver ya k'araso inda Sabeer yake tsaye, key d'in motar dake hannun shi ya mik'a mishi hannu ya sanya ya kar6a tare da nufar inda motar take ya shiga key yayi mata tare da jan ta zuwa gaban Sabeer, kafin driver ya fito ya bud'e mishi k'ofa tuni Sabeer ya shiga cikin motar, don haka kawai driver tuk'i ya fara gate man ya bud'e musu gate suka fita.
"Yalla6ai ina zamu je? "
Driver ya tambaya, ba tare da Sabeer ya kalli inda yake ba yace
"D'an k'auyen nan da muka je zaka mayar da ni "
"Toh Yalla6ai "
Driver ya fad'a cikin mamakin mai Sabeer zai je yayi a wannan k'auyen kuma, gashi babu fuskar tambaya sai kawai yaja bakin shi yayi shiru ya mayar da hankalin shi kan tuk'in da yake.
Bayan sun isa k'auyen ne inda Sabeer ya had'u da Suhaima nan driver yayi parking a wurin, fitowa Sabeer yayi daga motar yana faman kalle kallen wajen da kuma hanyar da Suhaima tabi ranar ko zai ganta, amman har ya gama wurwurga idanun shi baiga ko mai kama da Suahima ko wannan yaron, gajiya yayi da tsayuwa ya shige mota ya zauna but still eyes nashi na jikin window yana kallon waje, driver dai kawai ido ne nashi.
Tun rana wajen k'arfe 2 suke wajen har yammaci wajen 5 na yammaci Sabeer bai ga mai kama da Suhaima ba, sosai abun ya dame shi ya rasa yanda zai yi yana son sake ganin yarinyar ne, sallahr la'asar anan suka yi ta cin abinci ne babu batun yin shi, Sabeer ko yunwar baya ji ma rabon shi da abinci tun breakfast na safe driver kuwa daurewa kawai yake don kuwa yunwa ce take kwakwalar 'ya'yan cikin shi, yana tunanin abin da ya tsayar dasu anan waje tsaya wajen awa 4, addu'a yake cikin zuciyar shi Allaj yasa Sabeer yace su tafi gida.
"Driver mu tafi gida "
Abin da Ado driver ya ji kenan wani sanyi dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi ko ba komai yasan nan ba da dad'e wa ba zai samu abinci ya ci, key yayi motar suka bar wajen amman idanun Sabeer akan hanyar da Suhaima ta wuce da gudu gaba d'aya wata damuwa ce cikin zuciyar shi, jinshi yake wani iri daban yaso sake ganin beautiful face nata a yau, haka suka k'arasa gida jiki ba k'arfi Sabeer ya shige bedroom nashi ya kwanta kan bed zuciyar shi cike da tunani kala kala duk akan Suhaima.
**** ****** *******
Aunty Aliyah ce durk'urshe a bakin makwarara tana faman kelaya amai sosai hannun ta dafe da da cikin ta d'ayan kuma dafe da k'asa, Suhaima da Yaya Aliyu sai sannu suke mata tamkar zasu yi kuka yanda fuskokin su ya nuna musamman ma Suhaima ganin yanda take shan wahala, sai da ta gama aman tsaf Yaya Aliyu ya wanke mata bakin ta tare da kamata suka wuce rumfar ya zaunar da ita kan tabarma, yayin da Suhaima kuma take gyara wajen da aka 6ata.
"Sannu Aliyah bari na fito da machine mu tafi asibiti tun jiya da yamma kike aman nan gashi har gari ya waye kina yi duk abin da kika ci sai ya fito koda ruwa ne ya kamata mu je kiga likita "
Yaya Aliyu ya fad'i hakan yana mik'a mata hijab d'in ta, bata yi musu ba ta sanya hannu ta kar6a tare da sanya wa, daidai lokacin Suhaima ta gama gyaran wajen ta k'araso rumfar, kallon ta Aliyu yayi tare da cewa
"Ki tafi gidan Babaa Lantana ki zauna zamu je asibiti ne "
Fuskar Suhaima d'auke da tsantsar damuwa tace
"Toh Yaya Allah ya dawo daku lafiya, Aunty Aliyah sannu Allah ya baki lafiya "
"Amin ya rabbi "
Cewar Aliyu don Aliyah bata iya magana saboda jin jikin da take yi, d'aki Suhaima ta shiga ta d'auko hijab d'in ta sannan ta fito hannu Aliyah ta rik'e suka fito zuwa kofar gida, inda Yaya Aliyu ya fito da machine d'in, sai da ya kulle gidan tukunna ya hau machine d'in dakyar Aliyah ta iya hawa saboda rashin jin dad'in jikin ta, sai da Suhaima ta ga tafiyar su sannna ta k'arasa gidan Babaa Lantana.
Da sallama ta shiga gidan Babaa Lantana da take wajen marhu tana soya gyad'a ta siyar wa ta amsawa Suhaima sallamar tana cewa
"Tabbb yau wa nake gani a gidan nan ba dai Suhaima ba?"
Ta fad'a cikin sigar wasa, d'an murmusawa Suhaima tayi tare da cewa
"Ni ce nan Babaa Lantana ina d'an tsohon ki? "
Suhaima ta k'arasa fad'i tana zama kusa da Babaa Lantana.
"D'an tsoho ya fita can gidan mai unguwa zasu tattauna matsalalon mu na garin nan musamman akan al'amarin matasa"
"Yayi kyau hakan "
Cewar Suhaima kenan
"Lafiya dai kike koh? "
Cewar Babaa Lantana tana sauke kaskon suyar gyadar, kallon ta Suhaima tayi tare da cewa
"Me kika gani? "
"Ganin ki nayi kamar fuskar ki da damuwa ne "
"Uhm Babaa Aunty Aliyah ce bata da lafiya yanzu haka sun tafi asibiti da Yaya "
Da sauri Babaa Lantana tace
"Me yasame ta? "
"Tun jiya take kwara amai har yau bai tsaya ba ko ruwa tasha sai ya dawo duk ta rame "
D'an shiru Babaa Lantana tayi kafin kuma ta saki murmishi akan fuskar ta daman tayi hasashen haka don taga alamomi sosai a jikin d'iyar ta ta magana ce bata yi ba.
Kallon mamaki Suhaima take yiwa Babaa Lantana ganin tana murmishi kamar wadda tayi mata wani babban albishir ba lalura ta fad'a mata ba kasa hak'ura tayi Babaa Lantana tayi magana tace
"Wai Babaa lafiyar ki kalau ina fad'a miki rashin lafiyar Aunty kina murmishi? "
"Uhm Suhaima ai abin farinciki ne ya samu shi yasa kika ga ina murmishi "
Cikin rashin fahimta Suhaima tace
"Rashin lafiyar Auntyn ne abin farinciki? "
'Yar dariya Babaa Lantana tayi tare da cewa
"Matsala ta da ke Suhaima rashin gane wa ina nufin Auntyn ki ciki ne da ita wannan lalurar da take yi ta laulayin ciki ne kin fahimta? "
Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Suhaima daman burin Aunty Aliyah ta samu ciki ta haihu kusan kullum sai ta fad'a wa Suhaima ta taya ta da addu'a Allah ya bata 'ya'ya, sai gashi Allah maji rik'on bawan shi ya bata, lallai yau Aunty Aliyah da Yaya Aliyu akwai murna an samu abin da ake so, amman duk da haka sai da Suhaima tace
"Da gaske kike Babaa? "
"Insha Allahu kuwa Suhaima "
Washe baki Suhaima tayi tana mai jin dad'i farinciki fal cikin zuciyar ta tana jiran dawowar su Yaya Aliyu.
Suna nan zaune Suhaima na taya Babaa Lantana d'aurin gyad'ar a leda suka ji tsayuwar machine d'in Aliyu a kofar gida, da gudu Suhaima ta fita har tana wancakali da faratin gyad'ar ya watsowa Babaa Lantana a fuska amman Suhaima bata tsaya ba tayi waje da gudu.
"Oh ni 'yasu Allah ya shiryi Suhaima ji yanda ta zubar min da gyadar nan "
Cewar Babaa Lantana tana tsince gyadar da ta zube a k'asa.
Suhaima tana fitowa kofar gida ta hango su har ma Yaya Aliyu ya bud'e gidan sun shiga, da sauri Suhaima ta k'arasa gidan ta shiga kallon fuskar Yaya Aliyu tayi taga sai washe baki yake haka ma Aunty Aliyah duk da kuwa jin jikin da take hakan bazai sa mutum ya kasa fahimtar farincikin dake shimfid'e a fuskar ta ba, nan Suhaima ta tabbatar da ciki ne dai da ita zancen Babaa Lantana ya zama gaskiya.
"Albishirin ki "
Cewar Yaya Aliyu yana kamo hannun Suhaima, cikin murmishi tace
"Goro fari tas Yaya "
'Yar dariya yayi kafin yace
"Auntyn ki ciki ne da ita zata haifar miki d'a "
Wani tsalle Suhaima ta daka ta rungume Yaya Aliyu tana dariya kafin ta cika shi ta rungume Aunty Aliyah tana cewa
"Wayyo dad'i Allah mun gode maka "
Hannun Yaya Aliyu ta rik'o dana Aunty Aliyah tace
"Yaya Aunty na taya ku murna sosai Allah ya fito mana dashi lafiya "
"Amin Thumma Amin "
Suka fad'i fuskar su k'unshe da murmishin farinciki, ana haka Babaa Lantana ma ta shigo ita da Baba Adamu don dawowar shi kenan Babaa Lantana take sanar mishi shine suka taho duba jikin Aliyah.
Anan Baba Adamu yaji abin farinciki daman Babaa Lantana ta hasaso hakan, nan suka taya juna murnar samun k'aruwar da zasu samu kafin daga baya su yi musu sallama su tafi......
Aishat A Muh'd ðŸÂŒðŸÂ»â€Â♀
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœÂðŸÂ»: 💠A SANADIN SON KI ðŸ’Â
Written by
Aishat A Muh'd
â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.