A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 38 of 67
*PAGE 71-72*
Sai bayan mangarib su Sabeer suka k'arasa gida, yana shiga part d'in su ya hango Mumy kusa da dining table tana shirya abincin dare fuskarta d'auke da damuwa wanda mutum kallo d'aya zai mata ya karanci hakan.
Yana zuwa ya rungume ta tare da bata peck a cheek d'in ta cikin farinciki yace
"Mumy yau ina cikin farinciki sosai na kusan mallakar Suhaima ki tayani murna "
Wani abu ne ya tokare mak'oshin Mumy wanda ya sanya ta d'an jimawa kafin ta bud'e bakinta tace
"Son nasan ka gaji da yawa kaje kayi wanka da sallah tukunna "
Ta k'arasa maganar cikin murmishin yak'en da yafi mata kuka ciwo, da yake Sabeer na cikin farinciki shi ya hanashi fahimtar yanayin Mumy, don haka kawai sai ya wuce up stairs.
Bin bayanshi da kallo Mumy tayi kafin ta zauna saman kujerar dining table ta zabga uban tagumi, duk wannan abin da suke Daddy yana kofar shigowa parlourn yana kallon su.
Ganin Mumy ta zauna ta zuba tagumi ya sanya shi k'arasa wa cikin parlourn hannun shi ya sanya ya janye tagumin da tayi kafin yace
"Haba sweetie nah me yasa kike son shiga tsakanin farincikin d'anki, kinsani Suhaima itace farincikin Sabeer yana sonta rabuwa da ita ba k'aramin wani hali zai shiga ba, a matsayin ki na uwa kina mishi addu'ar fatan Alkhairi a wannan auren nashi, ni kaina da fari ban yarda ba da hakan ba, zama nayi tare da yin nazari kafin na amince mishi sannan da naje yau naga gidan da Son yake neman aure sai naji hankalina ya sake kwanciya da wannan auren don kuwa gidan gidan mutunci ne sosai, ina son ki kwantar da hankali kada wani ciwo ya shige ki matar mutum kabarin shi Allah yayi Suhaima ce zata kasance matar d'anki don haka kawai ki bisu da fatan alkhairi "
Yana gama fad'in haka ya tashi ya wuce side d'in shi don kada a kirawo sallahr ishsha bai yi ko mangarib ba, Mumy tasan Daddy gaskiya ya fad'a mata but zuciyar ta tak'i amincewa da hakan.
Bayan Sabeer yayi wanka tare da yin sallahr mangarib da ishsha ne, ya zauna saman sofa yana kok'arin kiran Suhaima hannun shi d'aya kuma yana rik'e da cup aciki fresh milk ce don baya jin zai iya cin abincin dare cikin shi a k'oshe yake ji Babyn shi ta cika mishi ciki.
Lumshe idanun shi yayi jin sanyayyar murya Suhaima tana tambayar shi sun je gida lafiya, sake gyara kishingid'a yayi tare da cewa
"Alhamdullilah Baby mun isa gida lafiya yanzu kin ganni a d'aki ni d'aya duk nagaji "
"Ayyah sannu "
Cewar Suhaima cikin tausayin shi.
"Da munyi aure Baby nasan da ban da matsala zaki min tausa har na warware bama iya tausa ba har irin wanka da....... "
Bata bari ya k'arasa maganar ba da sauri cikin jin kunya tace
"Kaiii Sabeer baka jin kunyar fad'in wannan maganar? "
"Keee Baby bana jin kunya indai da ke zanyi irin wannan maganar"
Ya fad'i hakan cikin kwaikwayar maganar ta, dariya suka d'an yi kafin yace
"Baby ina son ki da yawa kada ki wahalar da rayuwa, kada kiyi amfani da son da nake miki ki wahalar dani please "
Ya k'arasa maganar kamar zai fashe mata da kuka, wani tausayin shine ya rufe Suhaima tare da wani irin son da yake k'ara shiga cikin zuciyar ta.
"Sabeer don me zan wahalar da rayuwa bana fatan na kasance daga irin wadannan mutanen masu amfani da son da ake musu suke wulak'anta mai son su, ina maka son da bazan jure ganin ka cikin wahala ba balle ni na wahalar da kai, daga lokacin da ka zama mijina zan kasance mai yi maka biyayya dai dai iyawata"
Wata ajiyar zuciya ya sauke wadda har sai da Suhaima ta jiyo shi kafin yace
"Naji dad'in abin da kika ce Baby nah thank U very much"
"Uhmmm "
Abin da tace kenan, d'an murmishi yayi yana cewa
"Baby ya neh koh bacci ya fara zuwa ne? "
"A'a me kagani? "
"Just naji kin ce uhmm"
"Ba komai "
"Okay bari na barki ki huta gud night and sweet dreams "
"Same 2 U"
A haka suka yi sallama kowa ya ajiye waya.
Soyayya mai zafi suke nuna wa junan su tsakanin Sabeer da Babyn shi, duk wata kulawa wanda ya kamata suna bawa junan su, soyayya mai tsafta suke nunawa junan su, yayin da Daddy ya matsantawa Mumy da dole ita zata had'a lefen Sabeer saboda da fari da yayi mata maganar k'in amincewa tayi sai da yayi da gaske sannan ta yarda dakyar, ta 6angaren su Suhaima ma Yaya Aliyu da Aunty Aliya sai shirye shirye suke yi sosai na hidimar biki.
Sabeer sai da ya nunawa Aliyu kada ya sha wahalar yi mata kayan d'aki zuwa kitchen don shi tuni ya gama shirya musu gidan su shi da Babyn shi, amman sam Yah Aliyu yak'i yarda ya kafe sai yayi dole tasa Sabeer hak'ura tunda baisan dalilin shi ba.
*** **** ***
*_After 2 week's_*
"Hello Suhaima kina jina? "
"Ehh Jiddah ina sauraren ki "
"Yawwa Babyn Yah Sabeer gobe ina son zuwa zamu tattauna akan maganar bikin fah"
Cikin rashin fahimta Suhaima tace
"Kamar wanne shiri? "
Hararar ta Jiddah tayi duk da tasan ba gani zata yi ba tun da a waya suke magana tace
"Har kinsa na harare ki wallahi, da kin d'auka zamu yi biki lami ne kamar bikin Yah Sabeer da Besty na ai dole mu kwashi shoki "
Dariya Suhaima ta tuntsire da ita kafin tace
"Kinyi nauyin zaki kwaso shokin a haka? "
"Dallah malama ina ruwan ki sai fah anyi duk wani zagaye zagayen ki yarinya "
Suhaima na dariya tace
"Toh sarkin masifa naji na yarda "
"Yawwa ko kefa, kin ga zan d'auko mai gyaran jikin da zata yi miki ke dai kawai sai nazo don my dear ya dawo gud night "
"Okay Allah ya kaimu "
"Amin kiyi min d'an wake don Allah "
"Zanyi miki kodan Babyn mu "
Dariya suka yi kafin su yi sallama, sauke numfashi Suhaima tayi tare da gyara kwanciyar ta, wayar ta ne ya sake k'ara nan ta d'auka da sauri ganin Sabeer ne, hirar su ta soyayya suka sha sosai kafin su yi sallama, addu'ar bacci Suhaima tayi babu dad'e wa bacci mai dad'i ya d'auke ta..........
_Fan's kuyi hak'uri da page's d'in nan don ban samu damar yin editing ba dafatan za'a yi min afuwa duk inda aka ga error typing_
Aishat A Muh'd âœðŸ»
[3/17, 8:53 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.