A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 53 of 67
*PAGE 99-100*
Mumy har ta fara gyangyad'in bacci acikin bedroom d'in ta bacci ne take son yi ko hospital bata lek'a ba sai da yamma, kamar cikin mafarki taji Sabeer na kwalla mata kira a firgice ta fito saboda tasan wannan kiran bana lafiya bane.
Cikin sauri take taka steps na bene saboda har yanzu Sabeer bai bar kiranta ba, cikin sauri ta k'arasa wajen shi inda yake tsaye tsakiyar parlour yana faman kiranta ga hawaye da suke zuba a eyes nashi.
"Son lafiya irin wannan kira haka? "
Kallon ta yayi hawaye na kwaranya a idon shi yace
"Mumy ashe bakya son bakya kaunata ko kad'an Mumy kin cuce ni kin cuce ni! "
Gaban Mumy ne yayi wani irin fad'uwa sosai da sauri ta dafe kirjin ta da hannu tare da zaro ido irin na shiga rud'u tace
"Son me kake nufi, me nayi maka har na cuce ka anya kanka d'aya ko wani abun kasha ne, ina matsayin mahaifiyar ka zan cuce ka ne ? "
Idanun shi jawur yace
" Mumy sam baki cika uwa mai bawa d'anta farinciki a rayuwa ba, kin rabani da 'ya'yana har biyu tun kafin su zama mutum kika zubar min dasu bayan haka kin rabani da mata ta Suhaima anya Mumy zan iya yafe miki kuwa? "
Sauran kad'an Mumy ta kife a k'asa tsabar firgita da kalaman Sabeer, amman sai ta wayance da cewa
"Haba Son wanne munafiki ne ya shirya maka wannan zancen kamar a mafarki, kada ka yarda da wannan shirmen zancen"
Kallonta Sabeer yake ba don mahaifiyar shi bace da idan ya shak'eta sai ta kusan daina numfashi, kasa magana ma yayi saboda takaici da bak'inciki sai wani irin kallo da yake mata mai tattare da nuna kin cuce ni, wannan kallon da Sabeer yake yiwa Mumy shi yafi komai d'aga mata hankali.
"Kada ki nemi ki raina mana hankali Faridah daman nasan duk wannan abun da ya faru da sanya hannun ki aciki"
Cewar Daddy a fusace wanda k'arasowar shi palourn kenan.
Kukan kissa da munafurci Mumy ta saki tare da cewa
"Na shiga uku Daddyn Sabeer ni kuke cewa na aikata hakan ta ina, na ta6a zuwa gidan Sabeer ko kuma na ta6a bata wani abun da hannuna taci cikin ya zube? "
Sam Mumy ta d'auka Larai tabar gidan kamar yanda ta umarce ta. Cikin fusata Daddy yace
"Ta dalilin 'yar aikin ki Larai mukasan komai, wadda kika turata gidan Sabeer don tana taimaka wa matar shi ayyukan gida ina fatan ba sai na k'arasa miki maganar ba kinsan komai tunda ke kika shirya hakan"
Da sauri Mumy ta dafa bango don ganin yanda take kok'arin fad'uwa kallon Sabeer da Daddy take tamkar wasu sababbin hallita agabanta yanda suka rikid'e mata kamar wasu zakuna, can kuma ta aro jarumta ita ma afusace tace
"Nayi nayi d'in! Duk abin da kuka fad'a na aikata su saboda bana son yarinyar da Sabeer i hate her bazan iya had'a zuri'a da shegiyar matsiyaciyar yariny..... "
"Stop it Mumy! Kada ki k'ara aibata min mata ta, nagodewa Allah da ban sake ta ba!"
Sabeer ya fad'a cikin hargowa, kallon shi Mumy kawai take cikin mamaki yau Sabeer ne yake mata tsawa.
"Son ni kake yiwa tsawa akan waccan 'yar iskar yarinyar "
Kuka ya fashe dashi kan yace
"Daddy! Daddy ka fad'awa Mumy ta daina danganta Suhaima da wad'annan kalaman"
Hugging nashi Daddy yayi yana bubbuga bayan shi yayin da yake jifan Mumy da wani irin kallo, saboda tsantsar rashin gaskiya Dr Faridah sai wani had'a uban gumi take kamar wadda ta had'iyi kunama abin da bata ta6a zaton zai faru da ita ba ya faru a lokacin da batayi tsammani ba ganin Sabeer d'anta kwaya d'aya tal da masoyin ta kuma mijinta suna kok'arin kubce mata a lokaci d'aya.
"Ni fah Daddy duk abin da zaku yi kuyi min amman gaskiya bazan iya kar6ar yarinyar nan ba matsayin suruka ta "
Cikin dakewa tayi maganar nan, da gudu Sabeer ya haye upstairs yana kuka zuciyar shi tana wani bugawa da k'arfi, cikin tsantsar 6acin rai Daddy yace
"Faridah da bak'incikin ki ya kashe min yaro gwara na rabu da ke! "
"What Daddyn Sabeer! Kana nufin akan waccan 'yar kauyen zaka sake ni? "
"Ofcourse Dr Faridah bazan zuba ido ki kashe min d'a ba wanda ya kasance shi kadai ne d'ana a duniya"
Matse hannun ta yayi da k'arfi tare da murd'asu har sai da tayi k'ara kafin yace
"Kina tantama ne bazan iya ba yanzu zakisan baki da wayo yarinya "
Wani irin lugude kirjin Mumy yake kamar zuciyar ta zata faso kirjinta ta fito, ganin tana daf da rasa mijinta amman duk da haka tana nan kan bakanta tasan Daddy bazai iya rabuwa da ita ba koda ya sake ta sai ya dawo da ita, tunanin ta ne ya katse a lokacin da Daddy yace
"Faridah ki tafi gidan ku na sa....... "
Kafin ya k'arasa fad'a yaji anyi sauri an toshe mishi baki, d'ago kanshi da zai yi suka had'a ido da Dr AhmadAhmad d'an fillo ranshi a 6ace yace
"Haba Hussein kamar baka da hankali taya zaka biyewa zuciyar ka ta aikata abin da zaka zo kana dana sani, ko da wasa kada ka k'ara yunkurin cewa zaka saki Faridah don duk cikin surukaina nafi kaunarta sakinta da zaka yi shine datse duk wani alak'a tsakanin mu da kai "
Sakin baki Daddy yayi yana kallon mahaifin nashi cikin mamaki kafin yace
"Abbah! Yanzu baka ga laifin Faridah anan ba?"
Cikin irin I don't care d'in na yace
"Yo wane baya yin kuskure Hussein tun da abun ya wuce ba shikenan ba a kiyayi gaba kawai "
Haushi ne ya turnik'e Daddy kallon Faridah yayi kafin yace
"Abbah! Duk da ka hanani sakinta amman ta tafi gidan su bazata dawo gidan nan sai Sabeer ya dawo da Suhaima matsayin matar shi "
Yana gama fad'in haka ya wuce fuuuu a fusace zuwa wajen Sabeer don ya rarrashe d'an nashi, yayin da Dr Ahmad d'an fillo da Dr Faridah suka bishi da kallo kafin lokaci d'aya ta fashe da kuka ganin yanda komai ya jagule mata lokaci d'aya ta rasa d'anta da mijinta!........
_kuyi hak'uri da wannan fan's_
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»
[4/16, 10:12 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
â™» *єχ¢ℓυѕινє ωÑιтєÑ'Ñ• fσÑυм*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.