Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 67

PAGE 36-37

Suhaima ta d'auki wajen 5 minutes kafin ta d'an nutsu ajiyar zuciya ta sake saukewa a karo na ba adadi tace
"Alhmdllh Allah nagode ma da wannan mutumin bai kamani ba da yau nasan zai ya rama abin da nayi mishi"
Suhaima ta furta hakan a sarari, wayar hannun ta ne ya cigaba da ringing dole ta dai daita nutsuwar ta tayi picking ganin sunan Yaya Aliyu ne akai.

Bayan sun gaisa ta tambaye shi jikin Aunty Aliyah daga nan shima ya tambaye ta yanayin zaman nata don tun da ya tafi hankalin shi yak'i kwanciya sam ga jikin Aliyah sai a hankali, boye mishi gaskiya Suhaima tayi tace tana nan lafiya yanzu ma suna wajen party dinner d'in Jiddah, daga k'arshe yayi mata nasiha sosai tukunna suka yi sallama ta ajiye phone d'in saman k'afarta tare da rafka tagumi tana tunanin yanda za'a yi ta koma cikin hall d'in bayan taga Sabeer ya shiga ciki, nan take zuciyarta ta bata shawarar zaman ta anan waje har a tashi nan take ta aminta da shawarar zuciyar ta sake gyara zama tayi tana jiyo sautin kid'an da yake tashi a wajen partyn.

Sai wurin 11 na dare aka tashi lokacin Suhaima har ta fara gajiya da zaman jiran Jiddah ta fara gyangyad'i a wurin, sam Suhaima batasan har an tashi ba gyangyad'in ta kawai take sabida ta gaji gashi bata saba kaiwa wannan lokacin ba batayi bacci ba gashi ba'a saitin k'ofar shiga hall d'in take ba balle a taji fitowar mutane.

Sai da aka watse a wurin bai fi mutane d'ai d'aiku ba Suhaima ta farka daga gyangyad'in da take tamkar wadda aka tasa haka ta bud'e ido firgigit, ganin yanda duhu yayi sosai yasa Suhaima rarumo wayar Jiddah dake saman k'afarta ta duba time, wani zabura tayi ta mik'e tsaye cikin tashin hankali ganin har k'arfe 11:30 tayi na dare, ai d'ora hannun ta tayi dukka biyun a saman kanta tace
"Wayyo Allahna na shiga uku ni Suhaima yau nice a waje har k'arfe goma sha d'aya da rabi innalillahi "

Lokaci d'aya hawaye suka fara zubo mata ga wani mugun tsoro da sanyi da take ji, tafiya ta fara yi ta nufi k'ofar hall d'in taga duk yawan mutanen nan wayam sai wasu d'ai d'aiku wanda batasan fuskar su ba, tuni Suhaima ta samu waje d'aya ta raku6e ta fara rasgar kuka kamar wadda akai mata dukan tsiya.

Kuka sosai take har da majina ta rasa mafita don duk a rud'e take ta kasa dai daita nutsuwar ta balle ta sami mafita gashi phone d'in Jiddah a hannun ta wa zata kirawo acikin familyn ta mutanen da basu yi maraba da zuwan ta cikin su ba matsayin bak'unta na kwanaki biyu, balle ta samu damar kiran wani daga ciki ya taimaka mata, gashi idan ma ta kirawo Yaya Aliyu d'aga musu hankali kafin ma yazo ma koma mai ne ya cinye ta kuma bata yi wa Jiddah adalci ba idan ta fad'a mishi yanzu ya zata yi wayyo Allah na, sake rushe wa da kuka Suhaima tayi sosai tana nan a raku6e taji an dafa mata kafad'a tare da cewa
"Hey what are you doing here? "
Wata irin firgita Suhaima tayi tare da jiyowa a tsorace had'a ido tayi da wannan guy d'in na d'azu yana tsaye daf da ita ya hard'e hannun shi a kirji, wani k'ugi cikin ta yayi wanda tana tunanin ma Sabeer yaji k'arar da cikin nata yayi matse k'afafun ta ta fara yi saboda daf take da sakin fitsari a tsaye jikin ta kuwa sai rawa yake wanda ya sanya wayar Jiddah ta fad'i a k'asa da bag d'in ta.

Kallon ta Sabeer yake up and down yana sakin wani murmishi wani sanyin dad'i ne yake ratsa cikin zuciyar shi da gangar jikin shi, sauran kad'an dariya ta kubce mishi ganin yanda take matse k'afa tamkar wanda yake jin fitsari ya matse shi irin sosai d'in nan har k'arar da jikin ta yayi sai da yaji sautin.

Ganin murmishin da yake ba k'aramin sake rud'ar da Suhaima yayi ba aikuwa fakar idon shi tayi ta tattara gown d'in ta da hannun ta kafin Sabeer ya ankara yaga Suhaima ta zura da gudu tayi hanyar fita daga gate, ba shiri shima ya d'auki phone d'in da bag nata da suka fad'i ya bita da gudu shima.

Suhaima da ta bud'e kofar gate d'in zata fita da sauri ta dawo baya jin wani irin sanyi da ya busa ta gashi wajen duhu babu wadaccen haske sosai a wurin nan ta tsaya waje d'aya tana rawar jiki, da haka Sabeer ya cimmata tana tsaye sai ruwan hawaye da yake tsere saman kyakkyawar face d'in ta, ganin Sabeer a kusa da ita da sauri Suhaima ta bud'e baki tace
"Don girman Allah kayi hak'uri da abin da nayi maka tsautsayi ni bazan sake ba har abada kayi hak'uri kada kayi min komai bansan kowa anan ba "

Sosai ta bashi tausayi ganin irin rud'ewar da tayi cikin sanyin murya yace
"Hey calm down babe babu abin da zan miki just I'll help you"
Kamo hannun ta yayi ganin har yanzu bata daina rawar jiki ba kuma a rud'e take, jan hannun ta yake har cikin mota ya zaunar da ita tukunna ya zagayo seat d'in driver ya zauna kallon ta ya tsayayi na tsayin wasu minutes, kallon yake cikin wani irin yanayi ita kuwa kanta a sunkuye batasan abin da yake ba tsoro ne fal a tattare da ita addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada ya cutar da ni, kafin yayi wa motar key suka bar wajen sun d'an yi nisa suna tafiya tukunna ya jiyo ya kalle ta still har yanzu kanta a sunkuye.

D'an girgiza kai yayi tare da sakin dan murmishi yace
"Ina zamu je, i mean ina ne gidan da zan kai ki? "

D'an satar kallon shi tayi ta fad'a duniyar tunani ita da take bak'uwa a garin yau ne zuwan ta na farko ina zata gane gidan, don haka sai tayi shiru kawai.

Ganin haka yasa Sabeer yace
"Ina jiran ki fah kinsan dare yayi fah idan baki da wajen zuwa kuma sai mu wuce guest house d'ina mu d'an huta zuwa gobe "

Wani zaro ido Suhaima tayi tamkar idanun ta zasu firfirto wani tsoro da nadamar shiga motar shi ya dirar mata lokaci d'aya ashe d'an iska ma ta shiga motar shi yau na shiga tara ba uku ba, dariya sauran kad'an ta kubce wa Sabeer ganin yanda Suhaima ta koma.

"Don Allah kasan gidan su amaryar Jiddah? "
Suhaima ta fad'a cikin rawar murya, da mamaki ya kalle ta kafin yace
"Oh nan zaki je kenan? "
Da sauri Suhaima ta d'aga kanta alamar eh, mamaki ne sosai ya kama shi ta yanda akayi Suhaima tazo gidan tun da yasan halin 'yan gidan su da basa huld'a da talaka sai mai kud'i d'an uwan su.

Kuyi hak'uri da wannan fan's mu had'u a next page muji ya zata kasance.
Ga Sabeer da Suhaima sun had'u shin komai zai faru kuma?...

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI

Written by
Aishat A Muh'd

â™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.