Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 67

Cigaba tayi da tafiyar ta abin ta har ta k'araso inda motar tayi parking amman babu wanda ya fito daga motar gashi glass d'in motar mai duhu ne ba'a ganin na ciki, sai dai na cikin ya gan ka, ita Suhaima ko alamar tsoro babu a tattare da ita ta wuce motar, baifi taku hud'u tayi ba tsakanin ta da motar taji alamar an bud'e kofar motar amman bata jiyo ba saboda bata da ra'ayin ganin wanda ke cikin motar.

Cikin fusata na cikin motar ya nufi inda Suhaima take tafiyar ta cikin zafin nama ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta na baya, tare da jiyo da Suhaima saitin inda yake ya d'aga hannu zai mare ta cak ya tsayar da hannun shi ya kasa karasar dashi kan fuskar Suhaima kamar yanda yayi niyya, sakamakon had'a ido da yayi da ita duk wani 6acin rai da ya kwaso shi yaji ya tafi a lokaci d'aya.

Kallon kyakkyawar face nata yake da eye's nata masu matuk'ar d'aukan hankali, runtse idon ta Suhaima tayi cikin tsoro jikin ta har ya fara 6ari na tsoro don ta zaci mari zata sha, eyelashes d'in ta yabi da kallo yanda suka bi idon suka kwanta kan beautiful face nata.

Jin bataji saukar mari ba ya sanya ta bud'e idanun ta a hankali ta sauke su kan fuskar kyakkyawan saurayin da yake gaban ta, ganin yanda ya zuba mata ido yana kallon ta ya sanya ta fincike hijab d'in ta da ya rik'e mata tare da gyara taayuwar ta aka wani rik'e kugu cike da tsiwa tace

"Malam lafiya da zaka wani rik'e min hijab? "

Sai da ya guy din ya lumshe idanun shi don jin saukar dadad'ar voice d'in Suhaima kafin ya sake bud'e idon nashi yana cigaba da kallon ta tamkar wadda ya samu wata tv yana kallo ko motsin kirki baya yi, sosai abin ya bawa Suhaima mamaki cikin zuciyar ta take cewa shi wannan baya jin tana magana ne ko kurma ne shi? da alamar ma daga birni yake.

Cikin tsiwa ta sake cewa "wai malam baka ji ina maka magana ko kai kurma ne? "

Ganin again ya kuma share ta sai kallon ta kawai da yake yi ne har da wani hard'e hannaye saman kirjin shi yasa Suhaima juya bayan ta cikin sa'a ta hango wani yaro na kusa da su hannun shi rik'e da robar ruwa a kanshi ya d'auko zai tafi gida.

Dad'i ne ya ishi Suhaima har da d'an murmusawa na mugunta don tasan abin da zata yiwa wannan mayen d'an birnin, yaron yana k'arasowa inda suke zai wuce da sauri Suhaima ta sanya hannunta saman kanshi ta d'auke robar ruwan.

Kafin yaron ya juyo tuni ta watsawa wannan guy d'in ruwan a jikin shi dukka tare da jefar da robar gefe d'aya, lokaci d'aya drivern da yake tsaye jikin motar da wannan yaron da Suhaima ta d'auki ruwan shi suka d'ora hannu a kansu cikin tashin hankalin da abin da Suhaima ta aikata, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya jin wannan ruwan mai shegen sanyi a jikin shi tsikar jikin shine ya tashi kafin ya sanya hannun shi a fuskar shi yana goge ruwan da yake di'gowa daga saman gashin kanshi yana kok'arin bud'e idon shi.

Ganin haka ya sanya Suhaima kwasa da gudu ita da yaron har ma yafi Suhaima gudu tamkar shi yayi laifin daman tuni ya mance da wata robar shi don anashi tunanin aka tashi kama da Suhaima har dashi za'a had'a, sai abin ma ya bawa guy d'in dariya sosai ganin yanda suke gudu kallon su yake fuskar shi d'auke da murmishi har sai da ya daina ganin su....

Ku hak'uri da wannan ban da charge wollah, ku biyo ni next chapter don jin abin da zai faru.

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝

Written by
Aishat A Muh'd

â™»EXCLUSIVE WRITERS FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Ina kike Basmah Er lele wannan shafin naki ne kyauta ina tayaki murnar kammala littafin ki TAURA BIYU Allah ya Kara basirah da k'arfin ido, Allah ya bar zumunci. 👄

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.