Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 67

PAGE 40-41

Tafiya suke Suhaima sai wara ido tana kalle kalle sosai taji garin na Kano ya birgeta daman Yaya Aliyu yana bata labarin yanda yanayin garin yake kodayaushe cikin sha'awar zuwa take sai gashi a dalilin Jiddah tazo ta, karatun Qur'an ne yake tashi a motar k'ira'ar Shureim cikin suratul Ma'idah sosai karatun yake ratsa cikin zuciyar Suhaima har wani lumshe ido take tana bin karatun a hankali cikin k'asa k'asa da muryar ta.

Agaban wani k'ayataccen mall driver yayi parking tare da cewa "mun iso ranki ya dad'e"
D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa
"Okay bari na shiga na fito "
"A fito lafiya "
Bud'e k'ofar motar tayi ta fito cikin takun nutsuwa take tafiyar duk da kuwa yanda gaban ta yake fad'uwa don bata ta6a zuwa irin wannan wajen ba, kawai d'auriya tayi kada ta ba da kanta amman zuciyar ta fal tsoro kamar ace kyat ta zura da gudu, har ta k'arasa wajen k'ofar shiga ta shiga ciki.

A hankali Sabeer yayi parking kusa da motar da ta kawo Suhaima, fitowa Sabeer yayi sannan ya k'arasa wajen motar tun kafin ya k'araso drive ya ganshi don haka da sauri ya fito daga motar yana cewa
"Yalla6ai barka da rana"
Sabeer bai tsaya bawa driven amsa ba yace
"Salisu me kake anan? "
"Yalla6ai na kawo k'awar Jiddah nan zata yi shopping "
"Okay zaka iya tafiya gida "
D'an shiru Salisu yayi kafin yace "Yalla6ai Jiddah tace na jirata ta gama na mayar da ita gida don bak'uwace anan "

D'an shan mur Sabeer yayi kafin yace "Oh baza kayi abin da na saka ba? "
Cikin d'an tsoro da biyayya Salisu yace
"Ayi min afuwa Yalla6ai yanzu zan tafi "
Yana gama fad'in haka ya shiga mota yaja ya bar wajen zuciyar shi cike da d'an tsoro yanzu idan ya koma gida me zai cewa Jiddah idan ta tambaye shi ina k'awar ta, gashi bazai iya musu da Sabeer ba don kada ya rasa aikin shi don dashi ya dogara.

Salisu driver na tafiya Sabeer ya saki wani murmishi dani kaina bansan ma'anar shi ba kafin ya shiga cikin mall d'in cikin takun shi na k'asaita, zuciyar shi cike da tunanin yanda yarinyar da ko sunan ta baisani ba zai tunkare ta da magana mafi daraja a wajen shi wanda babu 'ya macen da ta6a furtawa.

Bayan Suhaima ta gama duk siyayyan gift's d'in da zata bawa Jiddah ne ta nufi wajen biyan kud'i, ga mamakin ta akace an biya mata cikin mamaki take kallon matar da ta fad'a mata da gani yare ce don hausan ta baya fitowa sosai.
"Wane ya biya min anya nice?"
Suhaima ta tambayi matar, d'an murmishi tayi tare da cewa
"Yes kene aka biyawa ba ke da mijin ka bane? "
Ad'an tsorace Suhaima tace
" A'a ba mijina ba ne ko zanyi iya sanin wanda ya biya min?" Da mamakin abin da Suhaima ta fad'i tace mata "Yawwa ga Yalla6an can wanda ya biya miki "
Matar ta nuna wajen da d'an yatsanta, bin d'an yatsan matar Suhaima tayi kallo zuwa inda take nuna mata wani irin buguwa zuciyar Suhaima tayi sakamakon had'a ido da Sabeer da tayi yana wani kasheta da murmishi zaune yake kan kujera yana kallon ta suna had'a ido ya d'aga mata gira tare da yi mata wink, wayyo Allah nah yanzu wannan mutumin duk inda nayi sai ya biyo ni yanzu ya zanyi na guje mishi?, fad'in haka cikin zuciyar ta.

A sace ta k'ara kallon matar inda Sabeer yake sai taga ya tashi tsaye yana gyara rigar dake jikin shi, da sauri ta fara tafiya zuwa hanyar da zai kaita ta fita sauri kawai take tana fatan ta ganta a cikin mota ta shiga ciki ta zauna sun bar wajen.

Tana fitowa ta k'arasa inda suka yi parking amman wayam bata ga motar ba nan ta sake dudduba wa ko ba wurin ba ne taga dai still anan suka yi parking, toh ina motar da driven? Zuciyar Suhaima ta ambata.

"Ni nace ya tafi "
Fad'in Sabeer kenan wanda ke tsaye a bayan ta tamkar yasan abin da zuciyar ta take sak'amata, bata kula shi ba ta fara tafiya a wajen don bata da abin cewa tun da driven su ne d'auko shi suka yi yana musu aiki su biyashi dole yaji maganar shi tun da ita ba komai bace.

Ganin tana tafiya yasa Sabeer bin bayan ta yasha gabanta yana cewa
"Hey beauty kizo nayi dropping naki zuwa gida "
Ja Suhaima tayi ta tsaya tare da d'an kallon shi gaban ta na fad'uwa ta daure tace
"Bana so zan kai kaina inda nake buk'ata "
Tana gama fad'i haka ta kauce tare da zagaye shi zata wuce da sauri ya rik'o hannun ta, tsayawa Suhaima tayi tare da jiyowa ta kalli tsintsiyar hannun ta inda ya rik'e mata wani bak'inciki ne ya kamata ganin namijin da ba mijin ta ba muharraminta ba ya rik'e mata hannu a cikin bayyanar jama'a, ko jiya ma da ya rik'e mata hannu ba cikin nutsuwar ta take ba.

Wasu hawaye ne suka hau zubo mata a idanun ta kallon shi tayi tare da cewa
"Ka cika ni "
Muryar ta can k'asan mak'oshi ta furta hakan, ganin babu wasa a fuskar ta ya sanya shi cikata tana ganin haka yasa Suhaima juyawa zata cigaba da tafiya, cikin wata irin murya Sabeer yace
"Banason ki k'ara tafiya ba tare da na fad'a miki wani abu ba ina son kizo ki shiga mota akwai maganar da zan fad'a miki please "
D'an jim Suhaima tayi daman ko da zai barta ta tafi batasan inda zata nufa ba gashi ta bar wayar Jiddah a cikin mota.
"Na rok'e ki please "
Sabeer ya furta hakan yana kallon ta, juyawa tayi ta fara tafiya kawai shima bin ta yake a baya har suka k'arasa inda yayi parking motar shi ya bud'e mata seat na gaba ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya koma ya shiga mazaunin driver ya zauna yana nai mamakin kanshi yau wai shine yake bud'e wa wata mace k'ofar mota ta zauna lallai so ya canja shi daga d'abi'un halayyar shi na da zuwa wasu daban.

"Suna na Sabeer Hussein d'an fillo, ke mene sunan ki? "
Shiru Suhaima tayi bata yi mishi magana ba shima bai k'ara cewa komai sai da suka yi nisa da tafiya ta bud'e baki tamkar batason magana tace
"Suhaima "
A hankali ta furta hakan bata d'auka yaji ba sai da taji yace
"Nice name "
Jingina kanta tayi jikin kujerar da take zaune ta lumshe idanun ta, dan kallon ta Sabeer yayi ganin ta rufe idon ta ne yasa shi jan wani birki, a rikice Suhaima ta bud'e idon ta har ta buge kanta ta kalli gaban su ta d'auka wani abin ya faru sai taga ya cigaba da tuk'in shi ko kallo inda take bai yi ba, hararar shi tayi ta gefen ido tare da murgud'a bakin ta kad'an kafin ta koma ta sake lumshe idon ta.

Dariya ce taso kubce mishi amman ya danne cikin zuciyar shi yana cewa wanna yarinyar akwai tsiwa huh, gaban wani gida yayi parking mai kyau da gani gidan kasan sabo ne tun daga wajen kasan an kashe kud'i sosai idan ka kalla.

Jin an tsaya da motar yasa Suhaima bud'e idon ta ganin ba irin yanayin unguwar gidan su Jiddah ba ne yasa jiyowa ta kalle shi na alamr tambaya nan ina ne. Bai ce mata komai ba ya fito daga cikin motar ya bud'e mata ita ma sai tak'i fitowa tace
"Nan ba gidan su Jiddah ba ne don Allah ni ka kai ni gidan su... "
"Zan mayar da ke gida Suhaima but ina son ki bani wasu minute's akwai maganar da zamu yi "

D'an kallon shi tayi sai taga babu wasa saman fuskar shi duk da a tsorace take dashi haka ta fito daga motar ya rufe sannan suka nufi cikin gidan duk takun d'aya da Suhaima zata yi gaban ta fad'uwa yake.

Tura k'ofar gate d'in yayi ya shiga tana biye dashi, gate man na ganin shi ya zube yana gaida su Sabeer ne ya iya amsawa dakyar Suhaima kuwa bakin ta ne yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi, gidan babba ne ya had'u sosai cikin parlourn gidan suka shiga.

Zama yayi akan kujera ya d'ago kanshi yana kallon Suhaima wadda take tsaye k'ik'am tamkar wata soja yace
"Suhaima ki zauna ina son ki ban hankalin shi da nutsuwar ki "
Ba tare da ta kalle shi ba ta zauna don ta k'osa ta ganta a kusa da Jiddah. Shiru suka yi tamkar babu mutane a cikin parlourn har sai da Suhaima ta k'osa da shirun nashi tace
"Kai nake jira fah "
Tashi tsaye yayi ya dawo gaban ta ya zauna akan carpet d'in dake shimfid'e a k'asa, tsugunna wa yayi tamkar mai neman afuwa yace
"Suhaima kin tuna ranar da muka fara had'u wa da ke tun daga lokacin na kasa manta ki zuciya kullum cikin tunanin ki take haka idanuna kullum cikin son sake ganin ki suke, na je wajen sau uku k'auyen ku neman ki but ko mai kama da ke ban sake gani ba sai ajiya Allah ya nufa zan sake ganin ki "
Dan shiru yayi yana kallon Suhaima wadda take kallon shi take kuma sauraren abin da yake cewa cikin mamakin shi, ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa
"Naji dad'i Sosai a lokacin da na ganki a takaice Suhaima zan sanar miki zuciya ta ta kamu da son ki! I luv U Suhaima i really luv U, ban ta6a son wata mace a duniyar nan ba sai ke ina son ki bani had'in kai na nemi soyayyar ki auren ki nake son yi da gaske Suhaim..... "

Kasa k'arasa abin da zai fad'a yayi sakamakon ganin Suhaima da yayi a tsaye tana girgiza kanta cikin wani irin yanayi wanda na kasa banbance na tsoro ne ko na firgita da tayi daga jin abin da Sabeer ya fad'a mata.

Mik'e wa tsaye shima yayi tare da cewa " ina son ki! Ina son ki Suhaima zaki aure ni? "
Toshe kunnen ta Suhaima tayi da dukka hannun ta biyu don batason jin abin da Sabeer yake ce mata tana cewa
"Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka zaka iya neman wata "
Tana gama fad'i haka ta juya zata fita daga parlourn da tasan wannan shirmen maganar zai fad'a mata da bata biyo shi ba balle ta tsaya sauraren shi don ko a mafarki bazata ta6a aminta da abin da Sabeer ya fad'a mata balle ido biyu.

Fisgo hannun ta yayi da k'arfi wanda ya sanya ta fad'a wa cikin jikin shi ta buge kanta da faffad'an k'irjin shi, d'ago kanta yayi da dukka hannun shi biyun ya matse kan nata da k'arfi wanda ya sanya d'an kwalinta ya fad'i lallausan dogon gashin kanta ya bayyana a sarari, kallon shi Suhaima take wanda taga idanun shi sun yi ja sosai idan ba gizo idanun ta suke tamkar ruwan hawaye take hangowa cikin eye's nashi, ko kwakkwaran motsi ta kasa saboda rik'e mata kan da yayi cikin kakkausar murya yace
"K'arya kike Suhaima dole ki soni tun da har na soki, ina son ki fad'a min kina sona? "

Duk da tsoro da fad'uwar gaban da Suhaima take ga kuma zafin matse mata kan da yayi sai da ta bud'e baki tace
"Sabeer na fad'a maka bana son ka ba'a so dole ka rabu da ni please you're hurting me"
Idanun shi na zubar hawaye yace
"Are you sure baki sona? "
"Yes I'm very sure "
Cikin tabbatar wa Suhaima ta fad'a ba tare da shakka ba, a hankali taji ya cika ta ya koma ya zauna jagwab saman kujera kafin ya had'e kan shi da gwiwa hawaye ne masu zafin gaske suna zuba a idon shi yau wai Shi Sabeer Hussein d'an fillo mace yarinya k'arama take cewa bata son shi why? "

Suhaima kuwa ranta a 6ace ta d'auki d'an kwalinta ta daura tana me shafa wuyanta da d'an k'age, ko kallon inda Sabeer yake bata yi ba ta fita daga gidan ta barshi.

Ta d'auki wajen 10 minutes a tsaye ta rasa inda zata nufa sai ta ga motar Sabeer wanda yayi amfani da ita yanzu kauda kanta tayi gefe guda ganin an tsaya.
"Yalla6ai yace ki shigo na mayar da ke gida "
Wata murya ta daban ta furta mata hakan, kallon wajen tayi ta ga wani bak'on fuska ne ba Sabeer ba ne, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shiga motar bayan ya bud'e mata k'ofar motar.

Babu dad'e suna tafiya ba aka suka k'araso gidan su Jiddah bayan yayi parking ta kwashe kayan ta da tayi shopping ta fito daman a motar ta bar su, tana shigowa d'akin Jiddah sak'on harara ne ya fara ziyartar Suhaima a wajen su Zahra da sauran cousin's d'in Jiddah sa'annin ta, bata kula su ba ta k'arasa wajen Jiddah taya zata iya aminta da soyayyar Sabeer alhalin 'yan uwan shi suna kyamatar ta bazata kai kanta cikin matsala ba.

Daga baya ma sai suka zame suka bar musu d'akin daga Jiddah sai Suhaima, nan Suhaima ta bawa Jiddah gift's din da ta siyo mata hannu biyu Jiddah tasa hannu ta kar6a tana yiwa Suhaima godiya, tuni Suhaima ta watsar da abin da ya faru da ita da Sabeer ta fara harhad'a kayanta don gobe ana gama bud'an kai Yaya Aliyu zai zo ya d'auke ta zata koma k'auyen su inda hankalin ta zai fi kwanciya.

Da dare kuma dinner d'in da friends na ango suka had'a aka gabatar wanda iya k'awayen amarya da na ango ne kawai, daga nan kuma aka wuce da amarya gidan ta wanda yake nasarawa GRA gidan ya had'u sosai, nan Suhaima da 'yan uwan amaryar suka kwana.

Washe gari kuma da safe akayi walima anan farfajiyar gidan nata wanda ya had'a manyan malaman addinin musulunci mata suka gabatar da lectures akan rayuwar aure da tarbiyyar yara zuwa 1 aka tashi daga walimar bayan anci an sha.

Sallahr azahar Suhaima tayi bayan ta idar ta ne babu dad'e wa Yaya Aliyu yayi wa Jiddah waya yana k'ofar gidan, nan Jiddah da Suhaima suka rungume junan su suna kuka sosai dakyar dai Suhaima ta zame jikin ta ta d'auki bag nata suka fito babu wanda Suhaima tayi wa sallama cikin families d'in Jiddah don basu yi maraba da bak'unta suka yi ba.

Har compound d'in gidan Yaya Aliyu ya shigo suka gaisa da Jiddah tare da bata hak'urin rashin zuwan su da basu yi ba saboda jikin Aliyah sai a hankali, nan ta nuna ba komai yayi mata fatan alkhairi na zama lafiya, sannan suka yi Jiddah sallama suka tafi bayan kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima sosai, tana tsaye a wurin har suka fita daga gidan kafin ta koma ciki tana zubar hawaye na kewar Suhaima don tasan zasu kwana biyu basu had'u ba sai a waya.

Bayan Yaya Aliyu ya tada machine d'in shi suka fara tafiya Suhaima na bashi labarin yanda bikin ya kasance amman ba komai ta sanar mishi ba don bata sanar shi had'uwar ta da Sabeer ba da kuma yanda 'yan uwan Jiddah suka kar6e ta, murmishi kawai Yaya Aliyu yake na jin dad'in ganin tilon k'anwar tashi cikin koshin lafiya.....

Sai dai kuyi manage da page d'in nan ban samu time d'in da zan yi editing ba, mu had'u a next page don jin ko Sabeer zai hak'ura da Suhaima? Ko mai zai kasance a gaba?...

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI

Written by
Aishat A Muh'd

â™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.