Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 34 of 67

*PAGE 63-64*

Kasa k'arasa fad'in maganar tayi ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi, jin tayi shiru ne kuma ta sunkuyar da kai yasa shi sanya hannun shi ya d'ago face nata kafin yace

"Uhm ina jin ki Baby kawai dai me ".
Kasa jure kallon cikin idanun shi tayi sai ta lumshe idonta, kallon eye's lashes nata kawai yake cike da sha'awar kissing nasu sai dai ba yanzu yake son aikata hakan ba, d'an bud'e idonta tayi suka had'a eye's nasu kafin cikin d'an jin kunya Suhaima ta janye idanunta saboda ganin har idonshi ya fara canja launi tace
"Ya wuce fah, yanzu ka hak'ura zaka sha kunun ? Kada kace min a'a please "

Mak'e kafad'a yayi cikin shagwa6a da langa6e kai yace
"Nak'i wayon sai kin fad'a min idan ba haka ba bazan sha ba yarinya "

Sam Sabeer ya mance da duk wani shiri da yayi na share Suhaima, lallai ba k'aramin so yake mata ba, maganar tace ta katse mishi tunanin shi da yaji tana cewa
"Haba Yaya nah na zuba maka "
Dariya ta bashi sosai jin sunan da ta kirawo shi.
"Yaya na koma yau kuma?, wannan ai sunan Babban Yaya ne ni miji ne ba Yaya ba "

D'an rufe hannunta tayi da tafin hannunta sai ta d'an wara yatsun tana kallon shi ta haka kafin tace
"Ai kaima kazama Yaya tunda Yayan Jiddah ne kuma ka girme ni"
Tana gama fad'in haka ta janyo cup ta had'a mishi kunun ta ajiye mishi a gefen shi.
"Koh! "
Ya fad'in hakan yana kashe mata ido d'aya wani kunya ne ya sake kama Suhaima sai kawai ta mik'e zata gudu har zata fice daga d'akin taji yace
"Suhaima har zuwa yaushe zaki furta min kina sona ne?, ki tausaya wa rayuwata Suhaima ki amshi soyayyata nayi alkawarin kasancewa dake cikin tsayin rayuwata bazan ta6a wulak'anta ki ba ko na guje miki ina yi miki wani so wanda baki bazai iya kwatanta miki ba "
Cikin sanyin murya ya k'arasa fad'in haka fuskar shi d'auke da damuwa.

Jikinta ne yayi sanyi sosai har ta gaza d'aga k'afanta sai kawai ta tsaya itama zuciyar ta yayi rauni sosai ga wani sabon son Sabeer da ya k'ara shiga cikin zuciyar ta, gashi yanda ya sadaukar da rayuwar shi don ya ceci nata lafiyar da rayuwar koda iya hakan tasan Sabeer ba k'aramin sonta yake ba don haka bazata bar wannan damar ta kubce mata, don haka batasan lokacin da bakin ta ya furta

"Ina sonka Sabeer nima bazan iya rayuwa babu kai ba "
Tana k'arasa fad'in haka ta juya da gudu tabar d'akin cikin jin kunya.

Sabeer kuwa zaune yake kamar mutum mutumi saboda tsabar mamakin abin da ta furta mishi, anya ba mafarki yake ba kamar yanda ya saba tunanin shi da ne ya katse a lokacin da hannun shi ya dangwarar da cup d'in kunun gyadar har yayi nasarar zubo mishi a hannun shi wata 'yar k'ara ya saki kad'an, kafin kuma ya wuntsala kan katifar ya fara juyi na jin dad'i tabbas ba mafarkin da ya saba ba ne, da gaske ne Suhaima tace mishi tana son shi, sai da ya gama juyin murna sannan ya d'auki phone nashi num d'in Daddy ya lalubo ya kira.

Daddy yana picking ko sallama Sabeer bai yi ba saboda tsabar zumud'i cikin murna yace

"Daddy ka tayani murna Suhaima tace tana sona zata aure ni Daddy! "
Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Daddy fuskar shi cike da fara'a yace
"Alhamdullilah congrats son, yaushe zaka dawo don muna kewar ka? "
Yana dariya Sabeer yace
"Very soon Daddy! "
"Okay ya kamata ka dawo sai a fara maganar aure, uhm son za'a zama babba "
"Kaiiii Dad! har da tsokana koh? "
Ya fad'a cikin shagwa6a, dariya Daddy yayi kafin su cigaba da hira har zuwa lokacin da suka yi sallama, kwanciya Sabeer yayi ya lumshe idanun shi yana tuno lokacin da Suhaima take fad'a mishi tana son shi zata aure shi da wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi.

Lokacin da Suhaima ta fito da gudu daga d'akin Sabeer sauran kad'an ta bige Aunty Aliya tayi saurin kaucewa tana cewa
"Sorry Aunty nah"

"Lafiyan ki kuwa Suhaima? "
Fad'in Aliyah kenan.
"Aunty lafiya qlau wallahi "
tana gama fad'in haka ta wuce d'akin ta da sauri yayi da tabar Aliyah baki sake tana kallonta.

Kan bed ta fad'a tana murginawa akai tana wani murmishi dagani murmishin farinciki ne take, jinta take sakayau kamar ta sauke wani babban abu akanta.

"Ina son ka Sabeer, i luv U so much "
Fad'in Suhaima a fili tana rufe fuskarta da hannunta kamar mai jin kunya wani na ganin ta.

Tun daga wannan lokacin wata tsaftacacciyar soyayya ake gudanarwa tsakanin Sabeer da Suhaima, bawa junan su kulawa suke tare da tattalin juna, Yaya Aliyu, Aunty Aliya da su Babaa Lantana da Baba Adamu sun yi matuk'ar farinciki da kar6ar soyayyar Sabeer da Suhaima tayi.

Yammaci ne irin na bayan sallahr la'asar Sabeer da Suhaima suna zaune a tsakar gidan saman wata babbar tabarma hira suke yi irin ta masoya.

"Assalamu Alaikum "
Suhaima ta tsinkayi sallama da muryar da bazata ta6a mance ta ba, don haka zumbur ta mik'e da sauri ta nufi k'ofa nan suka had'u da juna, wani ihun murna Suhaima ta saki tare da yin tsalle ta rungume Jiddah cikin tsananin farincikin ganin ta.

Sai dai kuma jin abu ya tokare ta yasa ta sakinta tare da yin baya kad'an tana kallan d'an tudun da cikinta yayi, cikin dariya tace
"Besty kaddai mun samu Baby "

Dariya Jiddah tayi tare da kawo hannu ta d'an bugi kafad'ar Suhaima cikin k'asa k'asa da murya tace
"To sarkin tonon silili kina son ki kunyata ni gaban su Yaya "
Hannunta ta rik'o tare da juyawa da nufin su k'arasa wajen tabarmar su zauna, sai suka had'a ido da Aunty Aliyah wadda ihun Suhaima ya fito da ita daga d'aki ba shiri.

Cikin farinciki Aunty Aliya tace
"Jiddah yau kece a gari"
Cikin dariya Jiddah tace
"Ni ce wallahi Aunty ina Yaya Aliyu da Ameer ne ban gan....... "
Sauran maganar Jiddah ta mak'ale a bakinta saboda had'a ido da Sabeer da tayi.

Cikin mamaki tace
"Yaya Sabeer! "
Da murmishi kan face nashi yace
"Sai yanzu kika kula dani kenan "
Tana dariya tare da rufe bakinta tace
"Yah Sabeer ba haka ba ne wallahi d'okin ganin Besty ne ya sanya ban kula da kai ba "

D'an murmishi kawai yayi kafin ya wuce ya tafi, da mamaki sosai Jiddah take bin shi da kallo ko a mafarki bata zaci Sabeer zai zauna a irin wannan yanayin ba, kuma tayi farinciki da hakan don tun ba yanzu ba take sha'awar wani nata ya auri Suhaima saboda son da take mata, kama hannun ta Suhaima tayi suka zauna nan ta kawo mata ruwa kafin su fara gaisawa da Aunty Aliyah tana yi mata barka da samun Baby sun d'an ta6a hira kafin su wuce cikin d'akin Suhaima.

Nan suna shiga hira ta 6arke tsakanin su Suhaima sai tsokanar Jiddah take yanda tayi k'iba, Jiddah na dariya tace
"Yarinya sai kin yi uku nama don nasan Yah Sabeer zai baki kulawa ba kad'an ba"
"A haba taya zan yi ukun ki da ban ganu ba"
"Babyn kune ya sanya min wannan k'ibar don kiji yana zuwa nan duniya zan koma kamar yanda nake "

Da haka suka cigaba da hirar su inda Jiddah take fad'awa Suhaima abin da ya sanya bata zo ba lokacin da suka dawo daga honeymoon laulayin ciki ne ya sanyata a gaba sai yanzu ta samu dama dama.

Sai wajen mangarib Jiddah ta tafi cike da kewar Suhaima bayan ta ajiye musu tsarabar su har ta tafi dai basu k'ara had'uwa da Sabeer ba.....

Aishat A Muh'd ✍🏻
[3/6, 11:04 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Written by
Aishat A Muh'd

Dedicated to my Sadeey SaNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.