Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 47 of 67

*PAGE 87-88*

Shiga cikin bedroom d'in da take a kwance yayi hawa kan bed d'in yayi yana kok'arin had'a ta da jikin shi duk da jikinta ba kwari sai da tayi kok'arin matsawa da sauri, cikin marairaicewa Sabeer yace
"Baby please kada ki hora ni akan abin da akayi miki, bazan jure hakan ba "
Kamar zai yi kuka yake maganar, cikin muryar ta wadda ta dushashe tace
"Mu hakura da junan mu Sabeer 'yan uwanka basa sona sun tsaneni"

"Nooo! Baby ki daina fad'in haka bazan iya rabuwa dake ba, ni ina sonki kuma ni zan zauna dake basu ba "

Duk yanda yaso yanda yaso ya had'a ta da jikin shi don ya rarrashe ta tak'i yarda, gashi kukan ta yana ta6a mishi zuciya, bata ankara ba taji Sabeer yana fitar da hawaye.

Kallon shi ta tsaya yi kawai ana cikin haka Jiddah ta shigo da sauri ya goge hawayen shi don bayason ta gani, cikin sanyin murya yace
"Jiddah ki tayani rarrashin Baby tace bazata koma gidana ba"
Cikin jin tausayin su ta zauna tana kama hannun Suhaima tace
"Haba Suhaima mene hakan idan kika yi hakan ai abin da suke so kenan, taya zaki zalunci kanku bayan kuna son junan su kice zaku rabu, kiyi hak'uri don Allah kada ki rabu da Yah Sabeer yana son ki "

Rarrashin ta sosai Jiddah take dakyar ta ciyo kanta ta amince, rungume ta Sabeer yayi don jin dad'in abin da ta fad'a.

Har an fara yayyafi suka tafi gida, bayan sun je gida Suhaima tana yin wanka wani zazza6i mai zafi ya rufe ta sosai da ciwon kai sai kuma amai sosai ranar basu iyayin baccin kirki ba saboda yanda jikinta ya rikice sosai don Sabeer ba k'aramin tsorata yayi da jikin ba.

Washe gari da safe ya kirawo Dr Aishat don ta dubata, babu jimawa tazo tayi mata gwaje gwaje nan ta hango ciki d'an wata 2 ajikin Suhaima sai kuma damuwar da ta saukar mata da zazza6i, ganin yanda ta gala6aita ne ya sanyata sa mata drip don taji kwarin jikinta sannan tayi mata allurar bacci.

Nan tayiwa Sabeer albishir d'in cikin jikin Suhaima, dad'i da farinciki ne ya rufe Sabeer saboda tsakanin murna sai da yayiwa Dr Aishat kyautar mota, dad'i ya ishe shi Dr Aishat nan tayi ta zuba godiya da addu'a sannan tace da zarar Suhaima ta farka ya kirawo ta awaya tukunna ta tafi, Sabeer ya koma d'akin Suhaima kallon ta yake kawai wata zazzafar kaunar Suhaima take sake mamaye cikin zuciyar shi sai shafa cikinta yake Daddy ya iya kira yayi mishi albishir sosai Daddy ya nuna murnar shi.

*** **** ****

Dr Faridah ce zaune a katafaren office d'in ta sai jujjuyawa take cikin kujera idanun ta a lumshe, turo kofar akayi tare da shigowa.

Bata bud'e ido ba taba da umarnin azauna, wadda ta shigo ce ta zauna kan kujera kanta sunkuye tana jiran abin da Dr Faridah zata ce.

"Dr Aishat ina kika je bakizo office akan time ba? "
Cikin girmama wa tace
"Ranki ya dad'e naji gidan Yalla6ai Sabeer ne duba matar shi bata jin dad'i "
"Okay me ya same ta "
Cikin fara'a Dr Aishat tace
"Ai abin farinciki ne ya same mu Doctor don Matar shi ciki ne da ita har tsayin 2 months "

Wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki mutum ya zaci murmishin farinciki ta saki har da wani cewa
"Masha Allah Dr Aishat naji dad'i sosai da wannan albishir d'in "
Bud'e bag nata tayi ta d'auko kud'in da batasan adadin su ba ta mik'awa Dr Aishat tace
"Ga nawa tukuicin "
Kar6a Dr Aishat tayi cikin fara'a tace
"Kaiii wannan d'a da farinjini yake tun kafin yazo duniya nake samu alkhairi yanzu Yalla6ai fah ya bani kyautar mota "
"Babu komai zaki iya tafiya "
Tashi tayi tana godiya ta fice daga office d'in, wata shegiyar dariya Dr Faridah ta saki tare da cewa
"Lokaci na yayi dole cikin nan ya zube ta kowanne hali "

*** **** ****

Bayan ta tashi daga bacci ne Sabeer yayi mata wanka tare da bata tea ta d'an sha kad'an da maganin da Dr Aishat ta bata, sannan ya kirawo Dr Aishat ya fad'a mata ta farka babu 6ata lokaci tazo ta sake dubata tare da bata shawarwarin yanda zata kula da kanta daga nan tayi musu sallama ta tafi.

Kulawa sosai Sabeer yake bawa Suhaima don haka cikin kwana 2 ta d'an warware tunda cikin ba mai laulayi bane, tana cin abinci babu laifi, sai dai baccin da yake damunta don sai ta yini tana bacci ganin haka ya sanya Sabeer tunanin samin 'yar aiki don tana tallafa mata da wasu abubuwan.

Suna zaune da Daddy a parlour yake gaya mishi yana son 'yar aiki da zata na taimaka wa Suhaima saboda yawan baccin da take yi, abin da Mumy ya kamata ya fad'awa hakan amman babu fuskar hakan.

Suna cikin tattauna yanda zasu samu house girl ne can daddy yace
"Sabeer ina tunanin ka nemi Jiddah ta samo mata"
"Yawwa haka za'a yi Daddy "
Yana kok'arin zaro wayan shi ne a aljihu yaji muryar Mumy tana cewa
"Haba Son basai ka kirawo Jiddah ba, zan baka d'aya daga cikin house girl's nawa su taimaka mata "
Kallon ta suke da mamaki sosai ganin yanda take fara'a, duk yanda suka so su fahimci akwai wani nufi cikin zuciyar ta suka kasa gane hakan da yake Mumy 'yar duniya ce baka gane gabanta balle bayanta green snake ce.

Daddy duk da haka sai da yaji shakku da abin da tace bai yarda da ita ba amman sai yabar abin cikin zuciyar shi kawai, sai kuma ta zauna sosai ana hira da ita wanda rabon ta sakewa Sabeer tun lokacin da ya fara son Suhaima.

Da ya tashi tafiya ta had'a shi da house girl d'in yarinya ce bata fi 18yrs ba suka tafi amman bata bi motar Sabeer ba sai drive ne ya kaita, Suhaima taji dad'in zuwan 'yar aikin sosai gashi kuma taga bata da rawar kai.

Cikin kwana 2 ta tsaya tana aikin ta sosai yanda ya kamata gashi bata da k'iwa Suhaima najin dad'in zama da ita.

Da wani yammaci ne Suhaima tana zaune a parlour tana ta6a charting ita da Jiddah ne, sai ga Larai mai aiki ta kawo wa Suhaima wani had'in so6o acikin jug ga cup nan ta ajiye su kan center table tace
"Aunty ga so6o nan na had'a miki "
D'an yatsina fuska Suhaima tayi kan tace
"Anya zan sha so6on nan Larai bana sha'awar shanshi "
Murmishi tayi kan tace
"Haba Aunty ki daure kisha na 6ata lokaci ina shirya miki shi fah "
"To shikenan zuba min "
Cikin rawar jiki ta fara zuba mata har Suhaima taso d'ago wani abun atattare da ita ganin yanda take rawar jiki amman sai ta share zancen ta kar6i glass cup d'in ta fara shan sa6on, bata ji wani canjin wani yanayi aciki ba sai ma kamshin cocomber da kayam kamshi kawai taji sai zak'in sugar, taji dad'in so6on don har cup biyu ta shanye, tana gama sha ne Larai ta tattara ta d'auke gaba d'aya takai kitchen ta zubar cikin sink ragowar ta wanke jug da cup d'in tas ta goge su tare da jera su.

Tana gama wa ta bud'e k'ofar baya ta fita garden, zaro waya tayi cikin zanin ta tare da lalubo wata number ta danna kira, babu dad'e wa aka d'auka.

"Hajiya nayi duk yanda kika umarci ne nayi tasha har cikin so6o biyu "
Daga can akayi mata magana banji dai abin da akace ba sai naga Larai ta washe baki tana zuba godiya tare da kashe wayar cikin tsananin farinciki ta koma cikin gidan.

Suhaima kuwa ko 10 minute's bata yi da shan so6on nan ba taji cikin ta marar ta da bayan ta yana wani irin ciwo na daban tun tana daurewa har ta kasa ta fara kuka sosai tana kiran sunan Allah, zaro ido tayi gabanta yana bugawa mai tsanani ganin jini yana bin k'afar ta da yawan gaske saboda tsabar firgita da razana ga azabar ciwo ta fad'o daga kan kujera kanta ya bugu da center table lokaci d'aya numfashin ta ya d'auke...........

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[4/10, 8:54 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*

Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ

ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ

♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.