Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 67

PAGE 38-39

Babu wanda ya sake magana a cikin su kowannen su da tunanin da yake cikin zuciyar shi, amman Suhaima har yanzu hankalin tashe yake ganin har yanzu basu zo gidan ba ta sadaukar sace ta ma yayi tuni wasu sababbin waye sun cigaba da zuba saman fuskar ta, d'an kallon ta Sabeer yayi kad'an yana girgiza kai cike da mamakin ta ko wahalar kuka bata yi. Da haka suka k'arasa gidan Suhaima tana ganin an shiga cikin gidan ta tabbatar shine sai da ta saki ajiyar zuciya na kwanciyar hankali kafin ta sanya hannun ta saman face nata da niyyar goge hawaye sai taga an mik'a mata tissue kar6a tayi ta goge tukunna ta fara kok'arin bud'e kofar motar, kamar ance ta jiyo ta kalli side d'in su Jiddah aikuwa ta hango Jiddah tana tafiya cikin sauri tana goge fuska, da sauri Suhaima ta k'arasa fita kamar abin arzik'i ta rufe kofar motar sai ta zuro kanta ta jikin window da yake ya sauke glass d'in.

Sabeer har zai yi wuce zuwa parking lot sai yaga ta zuro kanta sai ya tsaya ya d'auka godiya zata yi mishi sai hasashen shi yasha banban da na Suhaima don cikin tsiwa ta fara cewa
"Uhm Malam ka d'auka godiya zan maka da ka zuba ido kana kallona har da bud'e kunnuwa don jin abin da zance, to ban gode ba kuma hak'urin da na baka d'azu in mistake ne, me yasa ma ka tausaya min ka d'auko ni da ka barni acan ma da nafi jin dad'i... "

Da sauri Suhaima ta fitar da kanta tare da zurawa da gudu zuwa inda ta hango Jiddah a tsaye sai safa da marwa take, sakamakon wata cafka da Sabeer ya kawo mata ganin ta gudu ne yasa shi dunk'ule hannun shi ya naushi d'aya hannun kafin ya jingina kanshi jikin kujera yace
"Hmmm lallai babe d'in nan da na kama ki yau a hannuna da sai gane kuren ki sai tsiwa da shegen tsoro fal ciki"

Shi mamakin ta ma yake tun da suka taho take kuka jiki yana rawar tsoro, amman wai har ta samu bakin tsiwa da taga ya kawo ta inda take buk'ata, kwafa yayi tare da k'arasa wa parking lot yayi parking tukunna ya nufi part d'in su yana cilla key yana cafewa zuciyar shi yau cike take da farinciki da nishad'i ya ganta a inda bai ta6a zaton zai ganta ba kuma yana kyautata zaton dalilin Jiddah tazo tun da yasan itace mai shige shigen talakawa sosai a cikin families d'in su yayi mamakin yanda Jiddah har tasan k'auyen su Suhaima ta ganta suka fara k'awance. Da wannan tunanin ya k'arasa cikin part d'in su kai tsaye bedroom nashi ya wuce yayi wanka sannan ya sanya wasu fararen sleeping dress ya kwanta amman ya kasa bacci sai tunanin abin da ya faru tsakanin shi da Suhaima yake yana zuba murmishi shi kad'ai.

Da gudu Jiddah ta k'araso wajen Suhaima a lokacin da ta hango ta rungume ta tayi tana kuka tace
"Suhaima don Allah kiyi hak'uri wallahi na d'auka kin biyo wasu ne sai da na neme ki na rasa na d'auka kina gida sai da na dawo na neme ki na rasa, hankali na ya tashi sosai yanzu haka da kika ga na fito komawa zanyi na duba ki sai na hango ki... Waya kawo ki? Naga kamar motar Yah Sabeer kika fito ko shine ya dawo da ke? "

Duk wannan maganar da Jiddah take da tambaya babu saurarawa tana yi tana kallon Suhaima, abin ma sai ya bawa Suhaima dariya kafin ta bud'e baki tace
"Kaiii Jiddah irin wannan tambayar gashi na dawo sai hankali ya kwanta amman ni bansan sunan wanda ya taimaka min ba naga dai kuna yanayi dashi "
Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke ta kwanciyar hankali kafin ta tace
"Mybe shine tun da naga motar shi ce amman naji dad'in abin da Yah Sabeer yayi dole nayi mishi godiya, gaskiya Suhaima kinci sa'a sosai don Yah Sabeer sai a slow wallahi"
"Koh? "
"Eh mana don baki san halin shi ba ne, gashi da miskilanci da shagwa6a don ko k'aramin yaro bazai nuna mishi shagwa6a ba "

"Hmmm ni bacci nake ji na gaji wallahi "
"Ai dole zo muje kiyi wanka ki kwanta "
Hannun ta Jiddah ta kama suka nufi side d'in shi shiru kake ji ko'ina kowa yayi bacci, don haka d'akin Jiddah suka nufa kai tsaye, bathroom Suhaima ta shiga wanka tayi tare da yin alwala ta fito wata catton sleeping dress dogowa Jiddah ta bata ta sanya da hula sannan ta sanya hijab sallahr isha'i tayi tare da yin shafa'i da wuturi tayi 'yan addu'o'in ta kafin ta tashi ta koma inda ta ajiye bag d'in da ta zo dashi.

D'auko wa tayi ta bud'e gift's d'in da Aunty Aliyah ta bata ta d'auko taso wa tayi ta zo inda Jiddah ta kwanta saman bed tace
"Jiddah ga gift's d'in da Aunty Aliyah ta bani na baki "
Cikin mamaki Jiddah ta tashi zaune tare da kar6ar sarkar tana dubawa, nan take ta fad'ad'a fara'ar ta sannan ta rungume Suhaima tana cewa
"Wayyo dad'i nagode sosai tana da kyau, me yasa baki fad'a min da wuri nayi mata godiya ba "
Suhaima fuskar ta d'auke da murmishi tace
"Itace ta hana na fad'a miki don babu waya tace sai mun tafi na baki "
"Naji dad'i sosai kiyi mata godiya Allah ya bata lafiya ya raba ta da abin da take d'auke dashi lafiya"
"Amin "
Cewar Suhaima kafin ta d'ora da cewa "sai wani godiya kike tamkar wadda aka bata wani babban abu "
D'an hararar ta Jiddah tayi tare da cewa "Hmm ke kika ga haka Suhaima amman tabbas wannan kyautat a wuri na babba ce "

'Yar dariya Suhaima kawai tayi ta kwanta ita ma bayan Jiddah tayi light off ne Suhaima tace
"Jiddah ina son gobe ki had'a ni da driver ya kaini wani mall zan yi siyayya "
"Me zaki siyo? "
"Ina ruwan ki idan na siyo kya gani "
"Alright Allah ya kaimu goben"
"Amin "
Da haka kowannen su yaja blanket ya lullu6a tare da addu'ar bacci babu dad'e wa bacci ya d'auke su mai nauyi da yake an gaji saboda hidima ta biki.

Washe gari da safe wajen k'arfe 11 aka d'aura auren Jiddah da Khaleel wanda d'umbin mutane masu kud'i goggagun 'yan boko tare da 'yan siyasa manyan likitoci da 'yan kasuwa suka halatta bayan d'aurin aure ne suka wuce reception ta maza, cikin gida kuwa matane a ciki taf ana hidimomi irin na biki.

Jiddah ce gaban dressing mirror tana sanya sark'ar da Aunty Aliyah ta bata sai da ta gama sanyawa tsaf ta jiyo ta kalli Suhaima wanda taci gayun ta cikin wani lace ash mai touch d'in flowers pink tayi kyau tamkar itace amaryar sai kashe selfie take abin ta.
"Yah babe kin gani koh na had'u? "
Cewar Jiddah kenan tana kallon Suhaima, kallon ta Suhaima tayi a haka sark'ar tayi mata kyau amman bai kamata ta sanya ta yanzu a lokacin bikin ta don tayi arha da yawa tana kallo ta ajiye gold d'in ta a gefe ta d'auki wannan ta sanya. D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa
"Wow amarya a gidan Khaleel kinyi kyau sosai sai dai ki cire sark'ar nan please "
"Because of what? "
"Bata cancanta ki sanya ta ba yanzu "
Har Jiddah ta bud'e baki zata yi magana aka turo k'ofar bedroom d'in aka shigo, Umman Jiddah ce ta shigo tasha kwalliya cikin wata tsadaddiyar shadda an zuba gold's a jiki sai fitar da k'amshin turare take, da sauri Suhaima ta gaida ita ba yabo ba fallasa ta amsa tana nufar Jiddah wadda take tsaye, cikin mamaki tace
"Me zan gani Jiddah, mene haka a wuyan ki? "
"Uhm Umma sark'a ce tayi kyau? "
Wata harara Ummna ta zabga mata tare da cewa
"You're very stupid Jiddah na rasa mene akan ki wallahi ranar bikin ki zaki sanya wannan banzan sark'ar mai araha haka ko 'yan aikin gidan nan zasu sanya sark'ar da suka fi wannan tsada balle ki, wanne stupid ne ya baki ita?"

A hankali cikin sanyi jiki Suhaima ta tashi ta nufi bathroom ta shige idanun ta suna fitar da hawaye yau a gabanta ake kiran Aunty Aliyah stupid wadda ta d'auke ta tamkar mahaifiya a wajenta yau da ace wata ce ba Umman Jiddah ba da sai inda k'arfin ta ya k'are wallahi.

Gaba d'aya ran Jiddah ya 6aci sosai cikin jin haushin abin da Umman ta fad'a, Jiddah ta bud'e baki tace
"Haba Umma me yasa kike haka ne "
"Dalla can rufe min baki kafin ranki ya 6aci kiyi maza ki cire ta sannan ki fito parlour za'a d'auki pic's sauran ki taho mana da yarinyar nan "
Tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata me yasa me yasa iyayen ta suke wannan halin na kyamar talaka me yasa suke abu tamkar basu da ilimi sun san Allah ne mai azurta bawan shi a lokacin da yaso, ba wayon su ko dabarar su ne yasa suke da kud'i ba a yanzu idan Allah yayi sai ya kwace kud'in.

Da sauri ta sanya hannu ta goge hawayen fuskar ta tare da jiyowa jin an dafa kafad'ar ta, Suhaima ta gani tana murmishi itama murmishin yak'e tayi kafin tace
"I'm so sorry Suhaima akan abin da Umma tayi miki"
"Haba Jiddah ni fah babu abin da akayi min "
Ta k'arasa fad'i tana cire sark'ar jikin Jiddah bayan ta gama cirewa ne ta d'auko mata wanda su zata sanya ta d'auko wannan ta sanya.

"Wow kin had'u tawan ni yanzu ki had'a ni da driver na tafi "
"Okay dear "
D'auko phones nata tayi ta kirawo driver magana tayi na tsayin 2 minute's sannan ta mik'a wa Suhaima wayar tace
"Yana waje yana jiran ki driven "
"Okay thank U "
Daga haka ta d'auki bag nata suka fito tare ta kofar baya Jiddah ta nuna wa Suhaima ta fita don batason wani ya sake 6atawa Suhaima rai, bayan Suhaima ta fita driven shi ya hango ta yayi mata magana aikuwa nan ta shiga mota yaja suka bar gidan.

Tun da Suhaima ta fito daga part d'in su Jiddah tazo ta wuce ta shiga mota yana kallon ta, wani mirmishin mugunta ya saki duk gajiyar da yayi dakyar yake d'aga k'afa gudowar shi daga wajen reception ko gamawa ba'a yi ba ya taho don duk ya gaji da hayaniya ganin Suhaima ne yasa duk yaji gajiyar ta wartsake cikin sauri ya shiga mota ya bisu a baya...

Aishat A Muh'd ✍🏻

[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI

Written by
Aishat A Muh'd

â™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.