Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 44 of 67

*PAGE 82-83*

Tana nan kwance ta kudundune cikin bargo tana rawar zazza6i ga hawayen da suke zuba a idanunta, kanta ciwo yake mata kamar ya cire duk eye's nata sunyi ja sun kumbura, tana cikin wannan halin Sabeer ya shigo bedroom d'in nata.

"Baby baccin yamma kike me yasa Jiddah bata zauna da ke ba har na dawo? "
Yana maganar yana hawa kan bed d'in, yaye blanket d'in yayi tare da sanya hannun shi zai d'ago ta jikin shi, sai yaji zafi sosai jikinta da ya ta6a jikinta, a rikice da kallo ta sai yaga hawayen da take nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi har ya rasa me zaice yana tsoron kada ya kasance ya illata 'yar mutane, jiki na rawa ya d'auke ta ya shimfid'e ta saman k'afafun shi cikin tashin hankali yace

"Baby nah me ya same ki, ina ne yake miki ciwo, me yasa baki kirawo ni kin fad'a min na kirawo doctor ya duba ki ba, tun yaushe wannan zazza6in ya rufe ki haka? "

Muryar shi da d'an rawa yake maganar, kasa magana Suhaima tayi sai hawayen da suke zuba kawai ita abin da yake sake firgitata da tsorata ta kada 'yan uwan Sabeer su rabasu, tabbas ta kamu da son Sabeer wanda tasan idan suka rabu su ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba.

"Kiyi min magana Baby please, ki daina kuka kin ga yanda idanun ki suka koma kuwa? "

Ganin yanda ya d'aga hankalin shi ya sanya bud'e idanun ta dakyar ta kalle shi kafin tace
"Zazza6i da ciwon kai ne kawai suke damu na"
"Sai me kuma? "
"Shikenan "
D'an kallon ta yayi sannan yace
"Baby fad'a min gaskiya abin da su Mumy suka yi muku shi ya sanya ki kuka ko? "
Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi cikin mamakin a inda yasan me akayi musu, d'an girgiza kai na takaici yayi then yace
"Nasan komai Baby, idan don wannan kike damuwa don Allah ki daina sanya shi cikin zuciyar ki kada ya janyo miki wani ciwon please, sannan zan d'auki mataki "

"Amman dai bai ka......."
Hannun shi ya sanya saman bakin ta ya rufe tare da cewa
"Baby kiyi shiru kawai, bari na kirawo doctor ya duba min ke "

Langa6e kanta tayi cikin yanayin shagwa6a tace
"Ni Allah bana son allura ne da shan magani, zan warke a hakan kawai "

"Ke kinma isa amarya fah kike taya ciwo yazo bazan d'auki matakin gaggawa akanshi ba sai yayi k'arfi ya hanani cin amarci nah tabbb yarinya naki wasa ne "

Sanya face nata tayi cikin kirjin shi tana d'an murmishi don ya bata kunya, tana ji ya kirawo Doctor Aishat wadda take babbar likitace ta gynecologist ce tana aiki a hospital d'in Dr Faridah wato Mumy.

Tsayin 5 minutes suka d'auka suna waya kafin ya kashe ya kalli Suhaima wadda ta lafe ajikin shi dauriya kawai take amman kanta ciwo yake sosai, shafa kanta yayi da hannun shi yana cewa
"Sannu Baby nah yanzu Doctor Aishat zata zo ta duba ki "

"Amman bazata yi min allura ba koh? "
"Eh zance kada tayi miki tunda bakya so"
D'aga kanta tayi kawai.
"Baby jikin ki yayi zafi sosai sannu dama zan iya dawo da ciwon jikina dana dawo dashi"

Hannunta ta d'ora saman face d'in shi tana shafa kwantaccen gashin sajen shi zuwa gefen bakin shi, lumshe eyes nashi yayi yana jin wani abu na ratsa shi kai hannun ta yayi bakin shi yayi kissing d'in tsakiyar tafin hannun ta, wanda daga shi har ita da bata jin dad'i sai suka ji wani yanayi atattare dasu.

"Kada ka damu zan samu sauk'i insha Allah"
"Amin Baby nah "

Sunan zaune suka ji door bell kafin ya tashi kuma ya bud'e yaji phone nashi na ringing, bayan ya d'auka ne Doctor Aishat take mishi bayanin gata a k'ofar parlour a tsaye.

"Baby bari naje na bud'e mata door ta k'araso "
Yana gama fad'in hakan ya fita daga bedroom d'in, yana shigo da ita ya koma bedroom ya d'auko Suhaima cak kamar wata Baby ya kawo ta parlour duk kunya ta kama Suhaima sosai sai wani sunkuyar da kai take shi kuwa gogan ko ajikin shi sai ma kok'arin had'a ta da jikin shi yake, yayi da Suhaima sai nok'ewa take.

"Yalla6ai me yake damun amaryar taka? "
Cewar Dr Aishat kenan ganin idan ta cigaba da shiru Sabeer zai bata kunya yanzu.

"Uhm Dr Aishat zazza6i ne ke damunta da ciwon kai sai kuma..... Uhmmm kin dai gane bansani ba ko taji ciwo? "
Ya k'arasa fad'a yana shafa bayan kanshi, kamar k'asa ta tsage ta shige ciki haka Suhaima taji a lokacin, yayin da Dr Aishat ta maze don tasan tatsuniyar gizo bazata wuce k'ok'i ba.

"Yalla6ai na fahimta inason zan duba don nagane ko taji ciwo "

"Okay ba damuwa "
Kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta sai bedroom ya kwantar da ita saman bed yayi da Dr Aishat take binsu a baya, ganin ya tsaya bashi da alamar fita ya sanya tace
"Yalla6ai ka taimaka ka d'an bamu waje kad'an"

Ba dan yaso ba ya fita daga bedroom d'in, bayan ya fita ne Doctor Aishat ta duba Suhaima nan ta gane bata ji wani ciwo sosai ba idan tana amfani da ruwan d'umi ma zuwa nan da kwanaki biyu zata warke, nan ta fara kok'arin yi mata allura aikuwa Suhaima ta sanya kuka tare da rirrik'e hannun Doctor d'in, sai Sabeer ta kirawo dakyar ta yarda akayi mata da rarrashi da lalla6a tare da sanya ta ajikin shi aka samu akayi guda biyu sannan ta bata magungunan da zata sha, kuma ta basu shawarwari na yanda Suhaima zata kula da kanta har ta samu sauk'i.

Tukunna tayi musu sallama ta tafi bayan Sabeer ya taka mata zuwa bakin k'ofar fita parlour, kitchen ya wuce ya bud'e frige fresh milk ya d'auko tare da cup ya dawo d'akin lalla6a ta yayi har tasha maganin da fresh milk d'in babu dad'e wa bacci ya d'auke ta da yake har da maganin sanya bacci aciki.

Yana zaune kusa da kanta ya rik'e hannun ta yana aikin kallon ta kawai jinshi yake kamar a mafarki yau wai shine da Suhaima a matsayin ma'aurata, sannan abin da su Mumy suka yi yaji haushi sosai Jiddah ce take fad'a mishi a waya bayan tabar gidan Suhaima, da yaso yin magana dasu Mumy but Daddy ya rarrashe shi kan yayi hak'uri komai mai wuce wa ne wataran sai labari ya zuba musu ido kawai, shi ya cigaba da kula da matar shi don bata da kowa a kusa sai shi.

Kiran sallahr mangarib ne ya tashe shi daga zaunen, addu'a yayiwa Suhaima sannan ya tashi ya fita side nashi ya shiga yayi alwala ya wuce masallaci sai after ishsha ya dawo gidan, yana shigowa farfajiyar gidan ya had'u da driven Jiddah bayan ya gaida Sabeer ne ya bashi sak'on Jiddah na basket mai d'auke da foodflaks 3 sai Jug kar6a Sabeer yayi sannan ya d'auko kud'i ya bawa driven, sosai driven yayi godiya kafin ya tafi, shiga cikin gidan yayi hannun shi rik'e da basket d'in cikin zuciyar shi yana jinjinawa Jiddah da matuk'ar kok'arin da take akan su, yaji dad'in kawo abincin nan daman yanzu yake shirin fita yi musu take away sai gashi na kuma ta hutar dashi, addu'a yayi mata cikin zuciyar shi na Allah ya sauke ta lafiya.

Ajiye basket d'in yayi saman dinning table sannan ya wuce bedroom ya tarar har Suhaima ta tashi tana bathroom don yaji k'arar zubar ruwa, don haka sai yawuce nashi side d'in yayi wanka ya shirya cikin wani catton na kayam bacca and sky blue ya fesa different perfumes masu dad'in kamshi, tukunna ya koma bedroom d'in Suhaima ya tarar har ta fito daga bathroom sallah ma take.

Shiga yayi cikin d'akin ya zauna kan sofa ya d'an lumshe idanun shi, bacci ne sosai cikin eyes nashi ga gajiya, tana idar da sallahr mangarib and ishsha ne bayan tayi shafa'i da wutiri tare da addu'o'in ta ne sai ta tashi ta cire hijab d'in jikinta.

Tana sanye da wata sleeping dress white tsayin ta iyakar shi tsakiyar cinyar ta sai zanin da ta d'aura tayi sallah, batasan Sabeer ya shigo ba sai kawai ta warware zanin ta ajiye shi sannan ta k'arasa wajen dressing mirror ta taje gashinta tare da sanya perfumes ajikinta.

Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta yayi luf ne kawai ajikin sofa, tuni ya fara jin wani canjin yanayi a jikinshi don kuwa Babyn shi tayi mishi kyau amman sai dai ya had'iye abin da yake ji dole yabar ta taji sauk'i.

Tashi yayi tsaye yana wani binta da kallon k'asan ido ya k'arasa inda take tana d'aure kanta da ribbon hannun shi ya sanya ya cikin gashin kan nata yana wani yamutsa shi, a d'an tsorace ta jiyo ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya........

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ✍🏻
[4/9, 5:00 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*

Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ

ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.