A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel
Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 46 of 67
*PAGE 85-86*
Da kallon mamaki Sabeer da Suhaima suka bita dashi kawai kafin kuma Sabeer ya rik'o hannunta yace
"Sorry Baby nah akan abin da Mumy take miki bana jin dad'in haka ko kad'an "
Cikin rarrashi ya k'arasa maganar gashi fuskar shi d'auke da damuwa, d'an murmishin yak'e Suhaima ta saki sannan tace
"Kada ka damu don Allah komai mai wuce wa ne, mu tafi ka ga Baby kada ka makara a office ".
"Thank U Baby nah da yanda kike da fahimta i luv U "
Suhaima na shirin bashi amsa kenan Jiddah ta lek'o da kanta tana cewa
"Don Allah Yah Sabeer mene haka tun d'azu kuna tsaye anan ka hanata shigowa "
Hannun shi ya sanya tare da janyo kunnen ta d'aya yace
"Jiddah kin raina ni da yawa zan miki duka na tsayar da ita d'in mata ta ce ai "
D'an ihu ta saki na jin zafi kafin ta marairaice fuska tace
"Sorry Yah Sabeer na tuba na daina "
Yanda tayi d'in dole yasan ya shi murmishi ya cika mata kunnen, kamo hannun Suhaima tayi suka wuce cikin gidan.
Masha Allah abin da Sabeer ya fad'a lokacin da ya kar6i Babyn fara ce tas har wani ja ja take yi kyakkyawa da ita ta d'ebo kamannin D'an fillo family, wani son yarinyar ne ya shiga zuciyar Sabeer har yana imagine gashi Suhaima ta haifa mishi Baby yana d'auke da shi.
Kallon Suhaima yayi wadda take zaune kusa dashi tana lek'en Babyn don itama kanta tayi mata kyau ba kad'an ba.
"Baby kema kina so koh, ki haifa mana mu ma please "
D'an murmishi tayi kafin tace
"Toh my dear kayi addu'a Allah ya bamu masu albarka "
"Amin Baby "
Jiddah ya mik'awa Babyn don ya makara ma sosai, tashi Suhaima tayi ta rakashi har bakin mota suka yi sallama ta dawo cikin gidan, bayan ta gama ganin Babyn ne sai ta gyarawa Jiddah bedroom nata sannan ta wuce kitchen don shirya abincin rana.
Tana tsaka da girkin 'yan uwan Jiddah suka fara zuwa gidan kasa fita tayi su gaisa tayi don gabanta sai fad'uwa yake, dakyar ta k'arasa girkin ta zuba a foodflaks sai kawai taja kujera a kitchen ta zauna tare da had'a kai da gwiwa tana tunani.
Awannan yanayin Jiddah tazo ta same ta tausayin Suhaima ne ya kamata, dafa kafad'ar ta tayi a tsorace Suhaima ta d'ago kanta ganin Jiddah ce ya sanyata sakin ajiyar zuciya.
"Suhaima ki rage tsoron su fah wallahi, taya zaki zauna a kitchen bazaki fito ba saboda su? "
"Uhmmm Jiddah wallahi bana son kallon wulak'anci da k'ask'ancin da suke min, ina jin tsoron fita mu gaisa dasu kada su gwasale ni kamar yanda suke yi min "
"Kada ki damu Suhaima komai zai wuce amman baza ki tak'ura kanki ba saboda su don haka ki fito daga kitchen "
Babu yanda zatayi haka ta fito hannunta rik'e dana Jiddah, wani kallo na wulak'anci suka bita dashi kamar yanda Suhaima ta tsani ayi mata, babu wanda ya amsa gaisuwar ta sai ta6e baki da suke Jiddah ma sai da ta samu alakoran harara a wajen su.
Bedroom d'in ta Jiddah ta kaita ta zauna amman duk da haka a tak'ure take har so take lokacin tashin Sabeer daga office yayi yazo su wuce gida, duk da ya kirawo ta awaya amman ba'a kwanciyar hankali ta amsa ba mishi ba, har tunanin ranar suna take batasan irin wulak'ancin da zasu yi mata cikin mutane ba.
Atak'ure take har zuwa bayan mangarib sannan Sabeer yazo suka tafi gida, kallo d'aya yayi mata ya fuskanci tana cikin damuwa girgiza kanshi yayi yana yana sauke numfashi dole ya takawa 'yan uwan shi birki akan abin da suke yiwa Babyn shi bazai jure ba ko kad'an ganin ta cikin damuwa.
Duk damuwar da take tattare da ita sai da Sabeer ya cire mata ita ya mayar da gurbin farinciki a wannan daren sosai Suhaima ta k'ara jin wani son mijinta cikin zuciyar ta yanda yake faranta mata rai itama tana addu'ar Allah ya sanya ta haihu don cika mishi burin shi.
Ranar suna tun safe Sabeer ya kaita don yak'i barin ta ta kwana ko komawa bata sake yi ba sabida yana gudun kada a sake 6ata mata rai duk da kuwa nacin da tayi mishi, sosai Sabeer da Suhaima suka kashe kud'i wajen had'a wa Babyn kaya da kuma ita kanta Jiddah don duk abin da suka yi mata baza su biyata abin da tayi musu ba ita kadai ce mai kaunar ganin su tare sai Daddy adukkan familyn Sabeer.
Sosai Jiddah taji dad'i abubuwan da suka kai mata tayi musu godiya tare da addu'ar Allah ya basu suma yaran masu albarka, Sabeer yaji dad'in addu'ar da tayi musu sosai duk cikin 'yan uwanshi yafison Jiddah fiye da kowa don itace mai kaunar abin da yake so.
Baby taci sunan Babar Khaleel wato Khadijah suna ce mata Islam, ansha suna sosai don har walima da yamma sai da aka shirya an kashe kud'i sosai, amman duk wannan abun Suhaima bata shigaba tana zaune waje d'aya kanta ma yake masifar ciwo sosai, gashi tasha kukan habaici da wulak'ancin da su kayi mata.
Sai bayan mangarib 'yan uwa suka fara tafiya, zaune Suhaima take kan abin sallah idar da sallahr ishsha da tayi kenan tana addu'a cikin zuciyar ta tana mai tunanin inda Sabeer ya tsaya baizo sun tafi ba don kanta sosa yake ciwo kamar ya cire ga idanun ta da suka kumbura saboda kuka, ta kirawo phones nashi basa shiga dukka, gashi hadari ya had'u sosai sai walk'iya ake.
"Munafuka har yanzu zaman me kike da baki tafi ba, mun gaji da ganin fah ya kamata kisan nayi "
Cewar Aunty Fadilah 'yar autar su Daddy kenan tana wani hararar Suhaima, sunkuyar da kanta Suhaima kawai tayi idanun ta suna zubar da hawaye.
"Wallahi na tsani yarinyar nan kyau kamar aljanna duk tabi ta asirce mana Sabeer sai yanda tayi dashi daman 'yan kauyen nan da shegen yin asiri"
Dariya aka kwashe da ita irin mai k'ulawar nan suna cewa
"Sai Auntyn mu fad'a mata dai munsan asiri tayi ta mallake mana d'an uwa don Yah Sabeer bazai ta6a son wannan talakar ba yana cikin hayyacin shi"
Cewar Zahra kenan, bak'inciki da takaici ya ishe Jiddah cikin d'aga murya tace
"Ke Zahra wallahi ki kiyayi kanki Allah zan fad'awa Yah Sabeer yaci uban ki matar shi kike fad'awa haka "
Make mata bakinta Aunty Fadilah tayi tana cewa
"Ta fad'a d'in ya kashe ta idan ya isa "
Kuka Jiddah ta sanya saboda make mata bakin da tayi don da ba k'aramin zafi taji ba, yayi da Zahra take danna mata harara.
"Ni na rasa abin da zamu yiwa wannan mayyar yarinyar ta rabu da Sabeer ba irin wulak'anci da bamu yi mata ba amman ta lik'e mishi "
Dariya aka sake kwashewa da ita, sannan Khairat tace
"Ina fah zata rabu dashi Aunty taga kyakkyawan saurayi sabon jini ga kud'i da ilimi inace ko aji ma ta ta6a shiga wannan shegiyar Jiddah ce ta wayar da ita "
Wani irin kuka mai tattare da bak'inciki Suhaima ta saki saboda ta kasa rik'e kukan nata, aikuwa ganin haka suka kwashe da dariya tare da tafawa, sannan Aunty Fadilah ta bud'e bottle d'in faro da yake hannun ta sai kawai Suhaima jin saukar ruwa mai sanyi da taji ajikinta har sai da ta saki ajiyar zuciya mai karfin gaske.
"Shegiya mara zuciya idan kin cika ke mai zuciya ce kare bai d'auke ba ki rabu da Sabeer daga yau "
"Aunty mu taya ki "
Cewar Zahra da Khairat sarakan tsiwa.
"Ku taho mana 'yan 'ya'yana masu kishin 'yan uwan su "
"Don Allah Aunty kuyi hak'uri kada ku min haka "
Cewar Jiddah tana kuka da karfi tana kare Suhaima, ture ta Aunty Fadilah tayi nan Zahra da Khairat suka dunga bud'e bottles na faro suna shek'a mata a jikinta suna zaginta da yi mata rashin mutunci duk gaba d'aya sun jik'e jikinta jagab da ruwa gashi don mugunta da ruwan sanyi suke amfani.
Yusrah yayar Jiddah da batason hayaniya tabar dakin bata jin dad'in abin da suke mata ba amman da yake miskilace sai kawai ta bar wajen.
Jiddah tana cikin kuka ne d'ago kan da zata yi sukayi 4 eye's da Sabeer tsaye ya hard'e hannun shi a kirjin shi eyes nashi sunyi ja tare da fuskar shi, sai da gaban Jiddah yayi mugun fad'uwa ganin yanda d'an uwan nata ya rikid'a kamar ba Sabeer ba, bata ta6a ganin shi cikin makamancin irin wannan yanayin ba.
Zahra ce ta fara arba da Sabeer ta ankara dashi tuni tayi cilli da bottle d'in hannun ta jikinta ya fara rawa na tsoro, haka ma Khairat itama ta cillar da robar tana rarraba ido Aunty Fadilah kuwa sai da gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Sabeer don bata ta6a ganin shi a haka ba batasan lokacin da ta saki nata robar ba.
Cikin wani irin taku na fusata ya k'arasa shiga d'akin bai kalli inda suke ba ya k'arasa inda Suhaima ke zaune jikin ta jagab da ruwa har tsiyaya yake d'ago ta yayi tare da kallon Jiddah yace
"Kai ta wani bedroom d'in ki bata kaya ta canja "
Muryar shi dakyar take fitowa saboda tsananin 6acin rai jikin shi har wani rawa yake, da sauri Jiddah taja hannun Suhaima wadda take kuka sosai suka fita.
Aunty Fadilah, Zahra da Khairat kuwa suman tsaye suka yi ko motsin kirki sun kasa yi, Zahra bata ankara ba taji saukar wani zazzafan mari mai saurin kurmanta mutum wani ihun k'ara ta saki da karfin gaske ya fara dukanta yana ball da ita cikin zafin nama, Khairat tun kafin azo kanta take rusa kuka sosai tana dana sanin biyewa zuciyarta da Aunty Fadilah.
Bata ankara ba taji saukar nata marin wanda har sai da bakin ta ya fashe, belt d'in jikin shi ya cire ya fara narkar su cikin tsananin 6acin rai har wasu hawaye ne suke zuba a eyes nashi zuciyar shi tana zafi.
"Sabeer mene haka kashe su zaka yi ne akan wannan matsiyaciyar yarinyar ne "
Bata gama rufe bakin ta ba taji saukan mari akan face d'in ta da mamaki ta d'ago kanta ta d'auka Sabeer ne ya mare ta sai taga ashe Daddy ne.
Zaro ido tayi cikin tsorata tace "Yaya! "
Sake kwad'a mata mari yayi tare da cewa
"Rufe min baki mara kunya banza mara kunyar wofi "
Cikin 6acin rai Daddy yake fad'in haka ashe Jiddah ce ta kirawo shi tana kuka tana yi mishi bayanin abin da yake faruwa shine ya taho.
Dakyar aka kwaci Zahra da Khairat a hannun Sabeer aka fita dasu daga d'akin duk ya farfasa musu jikin su ko kuka sun kasa saboda azaba, zubewa yayi kan carpet tare da rik'e kanshi da hannun shi yana sakin wani ajiyar zuciya.
Babu dad'ewa gaba d'aya kusan family suka had'u a gidan Jiddah har da Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa wadda take kuka wiwi Sabeer zai kashe mata 'yan jikoki akan wannan shegiyar yarinyar amman ta kasa yiwa Sabeer fad'a saboda son da take mishi sai hucin da take saki.
Dr Faridah ma ranta a 6ace sosai da kanta tayi treatment d'in su Zahra da Khairat a inda suka ji ciwo dole ta d'auki mataki akan wannan shegiyar, Aunty Fadilah kuwa tayi tsit da ita sai raba ido take saboda ba k'aramin tsoron Daddy take ba.
Suhaima bayan ta canja kaya ne tana kwance wani zazzafan zazza6i ne ya rufe ta kuka take sosai yau taga karshen wulak'anci dole ta rabu da Sabeer duk da kuwa son da take mishi bazata jure wulak'anci da zagan mata da mahaifiya da suke wadda take kwance a kabari.
Dakyar Daddy ya rik'o hannun Sabeer suka fito zuwa parlour kallo d'aya Dr d'an fillo yayi mishi yaji duk haushin dukan da yayiwa su Zahra ya kau hankalin shi ya tashi sosai ganin yanda d'an lelen shi ya koma dole yayi wa su Aunty Fadilah tatas don kawai Sabeer yaji sassauci ya nuna musu abin da suka yi basu kyauta ba daga karshe kuma yayi musu iyaka da matar Sabeer.
Daga karshe tafiya suka yi gaba d'ayan su, Mumy kuwa aranta haka tace kowa ya gama nashi rashin mutuncin akan wannan yarinyar yanzu lokacin ta yayi dole tayi nasarar raba Sabeer da Suhaima rabuwa ta har abadaaa.........
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»
[4/9, 9:15 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'É– âœðŸ»: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.