Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 67

PAGE 44-45

Yana nan kwance kan bed idanun shi a lumshe hawaye ne har yanzu suke zuba gaba d'aya brain nashi ya d'auki zafi har ya kasa tunanin abin yi, banko k'ofar akayi da k'arfi aka shigo Hajjah Hauwaa ce ta shigo a matukar kid'ime bayan ta Alhj Ahmad, Mumy da Daddyn Sabeer ne suka k'arasa shigowa cikin bedroom d'in.

Cikin kuka Hajjah Hauwaa ta k'arasa inda Sabeer yake kwance idanu a lumshe suna zubar da hawaye, fyace hancin ta tayi da hankycif d'in hannun ta kafin ta zauna saman drower na gefen bed, hannun Sabeer ta kamo cikin tashin hankali tace
"Sabeer me yake damun ka?, wane ya 6ata maka rai?, ka sanar damu yanzu kaga irin mataki da zamu d'auka akan kowanne d'an mara mutunci ne, ka sanar da mu yanzu kaji d'an lele na ba wanda zai ta6a min kai ya kwana lafiya kowa ne maza ka sanar da ni...?"

Shiru Sabeer yayi mata tamkar baisan da mutum kusa dashi ba, "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka ba"
Maganar Suhaima ce take ta amsa kuwwa a kunnen shi tamkar yanzu take fad'i, hannu shi yasa ya damk'o zanin gadon da k'arfi tamkar irin mace mai nak'udar nan kafin ya furta
"Suhaima ki so ni bazan iya rayuwa bake ba please idan kika baki soni ba mutuwa zan yi "

Wayyo tashin hankali a wajen iyayen Sabeer da su Hajjah ba kad'an ba najin abin da Sabeer yake fad'a, hannu Hajjah Hauwaa ta d'ora saman kanta ga hawaye kace kace saman fuskar ta tana cewa

"Hussein kuyi wani abin kai na shiga uku Sabeer ya haukace ko wata aljannar ce ta shafe shi "

Abin da Hajjah ta fad'i ne yasa Sabeer bud'e jajayen idanun shi ya watsa mata wani kallo, ai tuni Hajjah tayi wani tsalle ta koma bayan Alhj Ahmad tana rawar jiki tare da zare idanu tana lek'en Sabeer ta d'auka fisgota zai yi ya shak'eta don da gani kasan baya cikin hayyacin shi.

Ganin haka ya sanya Daddy kallon iyayen shi da Mumy wadda take shar6ar kuka yace
"Abba ku d'an bani wuri zanyi magana dashi "
Jikin a sanyaye suka fita daga bedroom d'in kowanne na sak'e sak'e cikin zuciyar shi.

Bayan sun fita ne Daddy ya samu waje kusa da Sabeer ya zauna tare da janyo shi cikin jikin shi yana bubbuga bayan shi na rarrashi, sun d'an dad'e a haka kafin Daddy ya raba jikinshi dana Sabeer kallon shi yayi sannan ya janyo wata bottle d'in faro ya bud'e ya sanya wa Sabeer a bakin shi, ba musu Sabeer ya fara sha kafin ya d'auke bakin shi alamar ya isheshi ajiye bottle d'in yayi, ta6a jikin Sabeer yayi yaji har jikinshi ya d'auki d'umi alamar zazza6i yana son rufe shi.

Cikin nutsuwa Daddy ya kalle shi kafin yace "me yake damun ka Son ka fad'a min damuwar ka ko da abin da zan iya taimaka maka? "

Sai da Sabeer yayi shiru na tsayin lokaci kamar bazai yi magana ba kafin kuma ya bud'e baki yace
"Daddy ko na fad'a maka matsala ta babu abin da zaka iya akai saboda ba irin ra'ayin ku ba ne"
D'an shiru Daddy yayi cikin mamakin abin da Sabeer ya fad'a, kawar da mamakin yayi ta hanyar yin murmishi na kwantar da hankali kafin yace
"Ka sanar da ni Son idan abin da ka fad'a min abin da zai yiwu ne why not mu baka had'in kai "

Kai tsaye Sabeer yace "Daddy aure nake son yi kuma Suhaima nake so Daddy "
Abin ya bawa Daddy dariya sai kawai ya murmusa sannan yace
"Toh Sabeer ban da abin ka mene na damuwa kuma?, wace ce Suhaima?, me akai akayi ta fad'a min sunan Baban ta a fad'in Nigeria a gobe za'a d'aura aure "

Kallon Daddy kawai Sabeer yake cikin zuciyar shi yana cewa lallai Daddy bakasan wace Suhaima ba ita ba 'yar kowa bace amman ta fita daban da sauran mata sannan kud'in bazai iya siyan ra'ayin ta ba.......

Katse mishi tunani Daddy yayi ta hanyar rik'o hannun shi yace
"Son wace Suhaima tell me? "
Cikin muryar damuwa Sabeer yace "Daddy bata sona bazata iya aure na tace min"
"K'arya take yi Son dole ta soka kuma ta aure ka, fad'a min ita wace zata kalli idon d'ana tace batason shi, fad'a min wane Ubanta? "
Daddy ya k'arasa fad'in haka rai a 6ace.
"Daddy Suhaima ba kowa bace haka iyayenta bakowa bane infact ita a k'auye take renon k'auye ce"
"What! Son me kace, kasan abin da kake fad'a? "

Daddy ya fad'i hakan yana tashi tsaye, tashi Sabeer shima yayi tsaye babu alamar tsoro ko fargaba yace
"Yes! Daddy nasan abin da na fad'a kuma ina cikin hayyaci na "
"Bazai yiwu ba Son ka sake nemo wata amman sam wannan yarinyar bata dace da kai ba 'yar talaka ce kuma 'yar k'auye bata da ilimi ko kad'an bazan iya had'a zuri'a da ita, kai kad'ai Allah ya bani bazan iya zuba ido naga kayan takaicin nan ba don haka ka sake tunani! "

Cikin tsantsar 6acin rai da abin da Daddy ya fad'a yasa Sabeer naushin dressing mirror da k'afar shi da k'arfi wanda sai da tayi k'ara tsabar had'uwar kafar shi da katakon dressing mirror wata k'ara mai razanar wa Sabeer ya saki da sauri Daddy ya juyo a razane da sauri ya k'arasa wajen Sabeer zai rik'e shi
"Don't touch me! "
Ya fad'a cikin wata irin voice, hankalin Daddy ya tashi sosai cikin rarrashi yace
"Saboda na hanaka auren yarinyar nan zaka nakasta kanka Sabeer? "
Idanun shi na tsiyayar hawayen kallon shi yake cikin ido kafin yace
"Idan baku barni na aureta ba zan iya mutuwa ma Daddy!"
A matak'ar razane Daddy yake kallon d'an nashi cikin wani irin yanayi na tsantsar tashin hankali.

Sabeer bai k'ara kallon inda Daddy yake ba ya fara tafiya cikin d'ingisa d'ayan k'afar nashi wanda ya dakidaki dressing mirror da ita, yana runtse ido saboda azaba da haka ya shiga bathroom yana shiga ya kunna shower ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya fashe da wani irin kuka yana bubbuga jikin bango da hannun shi ga ruwa yana zuba a kanshi da jikin shi.

Ya d'auki lokaci mai tsayi kafin ya fito k'afar shi ta isheshi da zugi da azaba ji yake tamkar ya cireta dakyar ya iya sanya kayan shi ya kwanta saman sofa fuskar nan tayi ja da ita saboda tsabar kuka, a haka wani wahalallen bacci yayi awon gaba dashi.

Azabar da k'afar shi ya dame shi da ita ne yasa shi farka wa daga baccin da ba wani jin dad'in shi yake ba, kallon k'afar yayi yaga ta kumbura sosai tamkar ba k'afar shi ba, tsura mata ido kawai yayi yana kallo, yana jin an bud'e k'ofar d'akin an shigo.

"Subhnallah Son haka k'afar ka ta koma? "
Bai kalle shi ba balle yasa ran zai amsa mishi, ganin haka yasa Daddy d'auko wayar shi ya kirawo mai gyaran k'afa tare da kiran family doctor d'in su Kafin ya ajiye wayar ya zubawa Sabeer ido yana kallon shi, ya hana kowa shigowa inda yake amman dukkanin su suna parlour a zaune Mummy da Hajjah sun sha kuka sun more yak'i sanar musu da ainahin abin da Sabeer ya fad'a mishi saboda yasan ba k'aramin ruguntsumi za'a sha ba.

Suna zaune har mai gyaran k'afa yazo bayan ya shigo d'akin sun gaisa da Daddy zai ta6a k'afar Sabeer ya janye ta da sauri tare da cewa
"Bana buk'ata a duba min"
"Haba Son taya ga ciwo a jikin ka kak'i yarda a duba maka, kayi hak'uri a duba maka please "

Duk wani rarrashi da lalla6a Daddy yayi wa Sabeer amman yak'i yarda har Doctor d'in da Daddy ya kirawo yazo amman duk Sabeer yak'i yarda gashi k'afar dad'a kumbura take, Daddy kasa jure ganin tilon d'an shi a haka yayi don haka ya bud'e baki yace......

Mu had'u next page fan's, naga Comment's naku na jiya sosai naji dad'i Allah ya bar k'auna.

Aishat A Muh'd ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI

Written by
Aishat A Muh'd

â™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

Dedicated to my Sadeey saNaz

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.