Complete Hausa Novels

A Sanadin Son Ki Complete Hausa Novel

Reading file: A_Sanadin_Son_Ki_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 50 of 67

*PAGE 93-94*

Suhaima gudu take tana kuka har ta samu ta fito daga gidan, sannan ta d'an tsaya tana yiwa gidan kallon k'arshe don tasan bazata ta6a komawa cikin shi ba har abada kuwa.

Fara tafiya tayi tana goge hawaye da hijab d'in jikinta ko takalmi babu a k'afar ta, wani mai taxi taga ya sauke wata mata bata tsaya tambayar shi ta fad'a cikin motar tana kuka kawai, daga matar har mai taxi d'in suka bita da kallo kowanne fuskar shi ta d'auki alhini suna tunanin ko mutuwa akayi mata mai zafi yasanya ta haka dad'in dad'awa da suka ga ko takalmi babu a k'afar nata, canjin matar mai taxi ya bata sannan ya tada motar suka fara tafiya sai da suka hau kan titi sannan yace
"Baiwar Allah ina zan kai ki? "
Dakyar ta iya tsayar da kukan tayiwa mai taxi bayanin inda zai kaita, mai taxi bai zaci wajen da nisa ba sai da ta fad'a mishi sunan kauyen da zai kaita yaso yi mata maganar ba nan zai je ba but ganin irin halin da take ciki ne kawa yayi niyyar taimaka mata.

*****

"Faridah ina jiye miki duk ranar da gaskiya tayi halinta, idan har da sanya hannun ki cikin wannan abun to kiyi gaggawar warwarewa tun kafin kizo kina nadama "

Turo baki tayi kan tace
"Wai ni duk kun tattara laifi akaina ina ruwana da ita da har zanyi yunkurin zubar mata da ciki kawai ta samu sake ne kasan halin talakan mutum bai iya samun waje ba, kuma nagodewa Allah da ya sanya suka rabu da d'ana yaje ya auri wadda zata haifa min 'yan jikoki na, yanzu kawai saki nake so naji yayi mata yanda zasu rabu har abada"

"Allah ya shirya ki Faridah "
Cikin wani irin murmishi tace
"Amin my Dear "

Tashi Daddy yayi zai fita itama ta mik'e tana cewa
"My Dear ka tsaya mu tafi da Son mana kada mu tafi mu barshi shi d'aya "
Cikin jin haushin abin da Sabeer yayi wa Suhaima tunda bai tsaya yayi bincike ba kawai ya yanke hukunci yace
"Ai ba yaro bane shi kuma yasan hanyar gida "
Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita daga palon, Jiddah ma d'aukan Islam tayi ta wuce da sauri ta bi bayan Daddy da harara Dr Faridah ta bita tukunna ta wuce upstairs inda Sabeer yake.

Agefen gado ta ganshi yayi ruf da jiki rabin jikin shi a saman bed rabin a k'asa sai wani irin shashshak'a yayi na kuka idanun nashi sunyi ja sun kumbura hatta face nashi tayi ja sai maimaita kalmar
"Why! Why! Suhaima zaki yi min haka na tsane ki i hate U "
. wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Dr Faridah jin yanda Sabeer yake furta ya tsani Suhaima kamar tayi tsalle da ihun murna haka take ji amman sai ta danne, zama tayi akan gadon ta tare da d'aukan kanshi ta d'ora kan k'afafun ta shafa mishi gashin kanshi take a hankali tana rarrashin shi but still Sabeer eyes nashi basu bar zubar da tears ba.

"My Son kayi hak'uri mu tafi gida kaji bazan iya barin ka anan kai d'aya ba "
"No! Mumy ki tafi ki barni zuciya ta yana daf da tarwatse wa, ina jin zafi acikin zuciya na idan na tuna Suhaima ta cuce ni taci amanata ta yaudare ni tayi min butulci Mumy! "

Dafe saitin zuciyar shi yayi da hannun shi d'aya yana jan wani irin numfashi, wani irin zabura Dr Faridah tayi ganin yanda eyes d'in Sabeer suka kakkafe.

Hannu ta d'ora saman kanta tana kuka tace
"Wayyo Allah nah na shiga uku zan kashe d'ana da kaina! "

******

Sai bayan sallahr ishsha ne suka k'arasa kauyen su Suhaima har k'ofar gida mai taxi ya kaita har zuwa yanzu Suhaima bata bar kukan bak'inciki da takaicin hukuncin da Sabeer ya yanke ba batare da bincike ba aure ko shekara baiyi ba ace har an rabu daman ashe ba sonta yake tsakani da Allah ba yaudare ce yake mata irin ta mazan yanzu nima na tsane ka kamar yanda ka tsane ni Sabeer!.

Maganar da d'an taxi yake mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani fitowa tayi daga motar cikin dushewar murya tace
"Bari na kar6o maka kud'in ka "

Ko taku uku bata yi ba taji ta bige mutum d'agowar da kanta da zatayi suka had'a ido da Yah Aliyu cikin tsakanin mamaki yace

"Suhaima! "

ai Suhaima batasan lokacin da ta fad'a jikin shi ba ta saki wani irin marayan kuka, wani irin tashin hankali da fad'uwar gaba ne ya ziyarci Yah Aliyu tuni fuskar shi ta fara canja yanayi.

"Yay... Yaya ka biyashi kud.... kud'in shi "
Ta fad'a cikin kuka tana nuna mai taxi da hannun ta, zuciyar Yah Aliyu tana tafasa yace
"Malam nawa ne kud'in ka? "
Nan d'an taxi d'in ya fad'a hannu Yah Aliyu ya zura a aljihu ya d'auko kud'in shi ya bashi yana bashi ya rik'o hannun Suhaima suka shiga cikin gida.

Aunty Aliyah da take zaune tana jijjiga Ameer yayi bacci taga shigowar mijin nata batasan lokacin da ta kwantar da Ameer saman katifa ba ta mik'e a razane tana cewa
"Suhaima kece da daren nan? "
Jikinta Suhaima ta fad'a tare da fashewa da kuka da k'arfi, ruwa Yah Aliyu ya d'ebo mai sanyi a randa zama yayi tare da zaunar da Suhaima akusa da shi ya bata ruwan da hannun shi, bayan ya gama bata ne sannan cikin nutsuwa yace
"Suhaima fad'a min me yafaru kada ki 6oye min komai don baki da kamata a duniyar nan "

Kallon Yah Aliyu tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta fara zayyana mishi abubuwan da suke faruwa gaba d'aya bata 6oye musu komai ba tana gama fad'in ta sake fashewa da kuka, Aunty Aliyah wadda take kukan tausayin Suhaima ta janyo ta jikin ta tana rarrashin ta.

Yah Aliyu kuwa wani zafi zuciyar yake yi sai wani huci mai zafi da yake fitarwa zagaye tsakar gidan yake hannun shi goye a bayan shi ya ma rasa abin cewa can ya bud'e baki cikin kakkausar murya yace

"Yau ni Aliyu za'a wulak'anta aci mana mutunci don kawai muna talaka, abin da Sabeer zai aikata mana kenan lallai yau koda bai sake ki ba ni ni Aliyu na sanya almakashi na datse igiyoyin da suke tsakanin ku dashi bake bashi har abadaaaa..........

Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
[4/12, 10:39 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*

Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ

ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ

♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.