Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 41

***

Mujahid na shiri kunna Motarsa yaga Junai ta fito da saurin ta sanye da Uniform, tuna abunda ya faru jiya yayi, da sauri ya karasa inda take tahowa.
Murmushi ya sakar mata yace "autar mu ya kike..
Bata rai tayi zata wuce ya kuma jan motar gabanta, "Junai am sorry nasan namaki laifi jiya".
Sai sannan ta kalleshi, turo baki tayi tace naji"
"Zona kaiki skull".
"Banso" ta fada.
"Baki hakura ba kenan, toh bara na fito nayi kneel down n seek for your forgiveness" shirin bude motar yayi tayi saurin dakatar dashi, "yaya unless kai zakazo kayi picking dinta"
Murmushi yayi yace "i promise"
Itama murmushin tayi sannan ta shiga motar yaja.

***
Salma kam tunanin abunda zata wa Mujahid take dan huce haushi, tana isawo Traffic light ta tsaya jiran Green light, tagumi tayi tahau saka da warwara, kaman ance juya ta juya left hand side dinta, Mujahid tagani zaune da wata mai Uniform suna hira shi kuma yanai sakar mata murmushi.
Haushi ne yakamata yadda ta ganshi cikin nishadi meanwhile gata nan kaman ta mutu, saidai tasan abunda xatayi.
Grean light na nunawa Mujahid yaja yayi gaba, lane dinsa ta koma tafara binsa a baya har suka isa makaranta junaina, tana ganin Junaina tamai nuni da 12 xai dawo daukan ta sannan yamata bye yaja yabar gurin.

Dariyan Mugunta Salma tayi, tun bata aiwatar da kudirin taba taji farin ciki ya mamaye ta, reverse tayi ta koma baya inda taga wani Toy Store, shiga tayi ta siyi Bindigar wasa ta yara wanda idan ka ganta zaka dauka ta gaske ce, can gefe tayi parking zaman jiran 12 yayi.
12 nayi taga anfara fitowa, wasu anxo daukan su, daga can nesa ta hangi Junaina tsaye da kawayanta, sundan jima tare sannan suka mata bye suka wuce.
Kunna motar Salma tayi ta karasa daidai Inda Junaina take tayi wining glass, Kallon ta Junaina tayi tana Murmushi.

Murmushi Salma tayi ta fiddo takarda a Jarkata tace "you are...".
Katse ta Junaina tayi tace "am Naina, nyc meeting you" Hannu Junaina ta mika mata zuciya daya, harga Allah taji Salma ta kwanta mata arai.
"Shigo mu tafi, Officer mujahid ya aikoni kaiki office dinsa daga nan ku tafi gida..". Acewar Salma batare data mika mata hannu ba.
Junaina baki har kunne ta zagaya ta shiga gaba ta zauna Salma taja motar, adaidai lokaci shi kuma Mujahid yayo kwanar Makarantar.

Sun glasses dinta Salma tadau ta saka a fuska hade da kara daure fuska tamau, Junai kam banda murmushi ba abunda take.
Wayar Salma ce tayi ringing, daukar tayi tasa a kunne suka fara magana da wani, can kuma tace "Tk hop dai kazo da igiyoyin ".
Daga can yace eh.
Tace na kusa karasowa, katse wayan tayi.

Junaina taso tagano wani abu saidai bata fahimci komai ba saida taga sai tafiya suke ba alamun tsayawa, gabanta ne ya fadi, nan take ta gano sumtin is not right.
"Sister kince office din Yaya zaki kaini" junai ta fadi.
Banxa da ita Salma tayi, kara tambaya Junai tayi, afusace Salma ta fiddo Bindigar, cikin tsawa tace "zakimin shuru ko saina harbeki...
Jiki na rawa Junai tayi shuru, Suna zuwa Dutsen Alhaji suka doshi wani daji, Salma ta sayar da motar hade da nuna mata bindigar.
Jiki na rawa Junai ta sauka, ganin maza biyu tayi gabanta rike da igiyoyi, "ku daure ta " Salma ta fada.
Ihu Junaina tayi cike da tsoro tace "baiwar Allah mina yi miki, wace ce ke?
Dariya Salma tayi tace "Mujahid bai taba baki labari na ba.
Cikin muryan kuka junaina tace "karya kikema yayana nasan baisan ki ba, kuma baya harka da Karuwai, kidnappers irin ku....
Wani wawan Mari Salma takai mata, nan Take kan Junaina ya juye, star, moon harma da rainbows ta fara gani saidai ta kasa tantance wanne ne wanne......

Tofah......
Muje zuwa.......

Labari don start ooooo
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA

27 - 30

Zaman minti biyar Mujahid yayi ba alamun fitowar ta. Wani guard dake guri ya tambaya yacemai ta jima da tafiyA. Bai damu ba yaja motarsa yayi gaba, atunaninsa tabi motan friends dinta, office ya wuce abunshi.
Dakyar junaina ta dawo hayyacinta bayan wasu tsuntsaye data ga suna lilo bisa kanta tsabar rad'ad'in marin, nan take tsoron ta yadawo sabo sai sannan ta ankara da tuni sun daure ta da igiyar ajiki wata bishiyar kwakwa dake gurin.
"Welcom back" Salma ta fad'a daga inda take hakinci kan dutse dake gurin, maza biyun na tsaye bayanta rike da hangbag dinta, fuskar ta daure tamau babu annuri.
Kuka sosai Junaina ta fashe dashi, farar fuskar tuni ya sauya launi zuwa ja, ga wata uwar yunwa dake addabarta ko breakfast batai ba tafita skull..
Gyara zama Salam tayi tace "gwara ma kibar kuka, cox i wont spare you, ina da Unfinished business da yayan ki"
Cikin shesheka Junaina tace,
"koma miye kuyi settling tsakanin ku, dan Allah ki barni na tafi gida, ina da exam gobe"
"Okay, lemme c if yayanki zai dau call dina" jakar dake hannu guy ta amsa ta ciro wayarta sannan tahau dailing no din Mujahid.

Yana ganin Call din Salma tsaki yayi, bai dauka ba yacigaba da aikin gabansa, saida ta kira sau kusan hudu ba respond sannan ta kalli Junaina, dariya tayi tace "it seems today isn't your lucky day"
Adan tsoro junai ta ware ido, Salma ta cigaba "nan da 3 hours idan baiyi picking call dinaa ba i won't hesitate blowing your brains out" karashe maganar tayi tanai mata nuni da bindigar.
Junai kam ta gama firgita, kuka sosai take, tashi Salma tayi ta koma mota ta zauna zuciyarta na radadi, tana ji ajikinta sumtin is not right saidai bata san miye ba, ayanxu burin ta kawai ta rama abunda Mujahid yayi mata, kwantar da Sit tayi ta kwanta hade da sanya earpiece kunne tahau sauraran wakar freedom ta Akon.

****

Shuru har karfe hud'u Junaina bata dawo ba, shiga dakin ta Hajiya tayi taga wayam.
"Ikon Allah, har yanxu bata dawo ba" ta fada, nambar junai ta kira taji ta ajiye kan dressing mirror tanai ringing. Daya daga cikin mai aikknsu kande ta kwalawa kira, tana zuwa tace "kikace da mujahid junaina ta bar gida da safe"
"Eh" kande tace.
"shuru dai bata dawo ba, bari na kira mujahid"
Kira nambasa tayi, shikam alokacin ma ya fito masallaci sallah la'asar, office xai koma yaga call din hajiya, dauka yayi tace
"kuna tare da Junaina ?
Cikin rashin fahimta yace
"Yaushe?
Hajiya tace "bata dawo gida ba, tun bayan daka fita da ita"
Bata rai yayi. "nifah dropping dinta kawai nayi a skull...
"Toh kaje ka dauko ta" kaste call din tayi batare data jiran cewar saba.
Guntun tsaki yaja, aransha shi yana fadin yaran biyun nan fitinar su bata karewa, i dont have time for their nonsense" wucewa office yayi.

Ta bangaran Salma kuwa bata kuma trying no din Mujahid ba, haka tayi ta zamanta a mota daga bisani ne ta fito gurin Junai, ganin yadda ta galabaita yasa ta tura Tk cikin gari siyo mata abinci take away da drink, bayan ya dawo ba yadda batayi ta bawa Junaina abincin, fir taki karba taci banda tsine mata data dunga yi tana kuka.
Yammace ta doso, hakalin Salma yafara tashi, tunanin kar dare yayi masu gurin, uwa uban idan mujahid bai dau call dinta ba batasan ya zatayi da Junaina ba, tsoro ne yakamata kar yarinyar mutane ta mutu a hannu ta...wayarta ta kalla ta hau turama Mujahid Text msg.
Kaman bazai duba ba sai kuma yafasa ya bude sakon "pick d damm call before i murder your stupid crying sister".
Gabansa ne ya fadi, hankali tashe ya mike tsaye cikin rawar jiki yafara neman nambar ta, saida tayi ringing sau biyar sannan ta dauka..
Cikin fusata yace "dont tell me dagaske kike
Tsaki taja.
"do you take me as a joke" kusa da Junai ta karasa hade da riko gashin kanta, ihu junai tayi cike da azaban rikon da tai mata, wayar Salma ta dasa mata akunne, muryar Mujahid taji akid'ime yana cewa "Auta ki kwantar da hankalin yanxu zanzo..."..
Maida wayar salma tayi kunnan ta sanna tace "kaji ai da kunnan ka".
Ran sa yagama baci, cikin daga murya yace "What did you want, say your price ?
Harara tayi kaman tana ganinshi, tace
"If you keep yelling at me i wont negotiate, so better calm yourself muyi magana like gentle people".
Kaman ya shaketa yakeji, kwantar da murya yayi.
"Duk abunda kikeso xan maki kuma zan baki ko miye, but plz leave my sister out of this"
Shuru tayi tana tunanin mai takeso gareshi, can ta tuna da abunda ya faru a Qrand Square, k'ala mata satan 50k da yayi saita tatikeshi hamsin sau goma.
Murmushi tayi tace "500k nakeso,
Iya k'uluwa yakai yace "aini ba ubanki bane dazan dauki 500k na baki, su kananan kwari da kike bi miye amfanin su"
Dariya rainin wayo tayi sannan ta bata rai tace "idan banga alert nan da 10 minti ba, forget you i have a sister" dif ta kashe call din.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.