Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 22 of 41
Innalilahi wa inna'ilaihi rajun yahau furtawa, Ummi bazaki mutu ba dayardar Ubangiji... Ya kuma fadi, da sauri ya karasa da ita mota yasata abaya sannan ya shiga gaba motan ya zaune hade da cire suit jacket dinsa daya shafi jini ya ajiye gefe sannan yaja motar.....
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
Wattpad @Cutexarah
Blog xarahbukar.wordpress.com
53
Saida Mubarak ya tabbatar Salma ta b'ace agurin sannan ya dakatar da fad'an hade da matsa wa gefen yana cewa "May calm down plz, ka saurare abunda zan fad'a ma"
Iya k'ulewa Mujahid yakai, nunasa yayi da bindigar cike da fusace yace "enough of your nonsense, hand over the d damm keys"
"Easy mehh.." Mubarak ya fad'a had'e dayin surrender, key din ya ciro ya wulla mai ya ceb'e.
Fuska ba annuri Mujahid yahau shi da mugun kallo yana cewa "dont you dare interfere, am warning you, stay out of this"
Kai Mubarak ya daga mai, tausayin Salma sosai yakama shi da takaici duk dalilin sa komai tsakanin su yakara tabarb'arewa, yana gani Mujahid ya juya da sauri yabar gurin.
Titi ya nufa bai ganta ba sai jinin daya gani kwace gurin, hannu yasa yaji jinin fresh ya tabbatar ba tayi nisa ba aduk inda take, Wayarsa ya fiddo ya kira duk polisawa dake check point din hanyoyin fita da shiga ya shaida masu lailai susa ido dakyau akan masu wucewa akwai wata wanted dangerous crimal data gudu kuma suyi making sure sun cafketa, komai na yanayin Salma da kayan jikinta saida ya kwatanta masu yadda zasu ganeta.
Sun Shiga gari, wani mugun Holdup ya tsayar dasu, hankali Jafar ne ya tashi kansancewar garin yad'an soma duhu, sauri kawai yake danya kai Salma asibiti. Wining glass yayi ya leka can gaba ya hango polisawa da sojoji tsaye suna lek'a motocin dake gaba da nashi, gabansa ne ya Fadi, da sauri yadau Jacket dinsa dake gefe ya rufawa Salam dake kwance seat din baya. Dukda baisan make faruwa ba Addua neman tsira yahau yi.
Yana isa gurin su Wani Sojo yace yayi kasa da glass din motar kasancewar sa tinted baa ganin make ciki.
"Ba matsala let him go, dan'uwan Oga ne" Wani babban dan Sanda dake gurin ya fada yana duban Jaafar, yasan shi sosai, gaisawa sukayi, police dun ya fadimai abunda ke faruwa, Tsuru Jaafar yayi danya gano bakin zaran. Hannu police din ya daga ma jaafar yaja motar ya wuce. Ajiyar zuciya ya sauke na relief, fasa kaman hanyar asibiti yayi ya wuce gidansu da ita. Da azama yayi parking ya fito yadauki Salma sukayi ciki, babu kowa palo, hajiya na dakinta, Junaina kuma tun safe taje gidan Aunty Bilki zama da yaranta... Sama ya haura da ita zuwa dakinsa ya kwantar da ita bisa godan sannan yahau kai koman yadda zai taimake ta shiba likita ba. Dabarar Kiran Aunty Bilki yayi, wayarsa yadauka ya danna lambarta...
Bayan Mujahid ya koma office, rundundar yan sanda kusan motoci hudu ya hada suka nufi gidan su Salma, tamkar wani wild vampire yake acting shi adole saiya cafko Salma aduk inda ta boye. Mom na zaune Palo tana trying no din Salma jin shuru bata dawo Shopping ba har dare yayi, kiran nambar take tana ringing baa dauka. Mai gadi ne ya kwankwaso ta mike ta bude, ya shaida mata yan sanda ke neman Salma. Hankalinta ne ya tashi ta zaburi mayafi a daki ta fito nan taga abu kaman yakin dunia..
Mujahid na zauna motarsa a gefe yana bada order, yana ganin Mom yama wani police signal ya karasa gurin ta hade da nuna mata takardar mai dauke da arrest warrant din Salma, salati Mom tayi bata gama rufe baki ba, yan sanda suka rab'a gefenta suka shiga gidan neman Salma, basu ganta ba suka fito waje, Salim ne ya iso gurin adan birkice daga inda ya biya bayan ya gama aika aika, kayan jikinsa na dazu basune jikin saba.
nan yahau tambayarsu meke faruwa, bayani suka mai, yahau ware idanu cike da kid'ima, ko Kallansa Mujahid bai ba balle ma yayi smelling rat, orders ya bawa yan Sanda suka bar gurin bayan ya dakatar da yan sanda shida suyi guarding gidan.
Mom kam kuka tafara yi ta kira Daddy a waya ta shaida mai abunda ke faruwa, Salima ma kuka yafara daya shiga dakinsa, baiyi tunanin haka abubuwa zasu kansance ba.
Aunty Bilki na asibiti tana duba patients, taga ga call din Jaafar, dauka tayi, yahau roka da magiyan taxo ta taimake shi yana cikin matsala, batagane inda zancen ya dosa ba tace bazata samu daman zuwa ba saboda dare yayi gida takeson komawa tabar Yaran, kuka jafar ya fashe dashi yanai cigaba da rokonta, ba yadda ta iya ta fito ta shiga motarta taja zuwa gidan, tana shiga sukayi Kicibis da Hajiya ta fito Palo, gaisawa sukayi tafadi ma hajiya kiran da Jaafar yayi mata, hankalin tashe duk su biyu suka haura sama.
Yana zauna kusa da Salma yana kuka suka shigo,
Tsayawa sukayi bakin kofar.
"miya faru haka.." Aunty Bilki tafada a tsorace ganin jini ta ko ina kan bedsheet..
Kasa bayani Jaafar yayi yace "plz help her, she is dieing..."
Hajiya tace "wace ce ka kawo har daki jina jina haka.."
Murya sarke yace "Ummii umman ce..".
What" Aunty Bilki ta fada, da gudu ita da Hajiya suka karasa bakin gadon.
Salati Hajiya tahau tana tab'a fuska Salma, "miya sameta, ina ka ganta.." Akid'ime hajiya ta jero tambayar.
Aunty Bilki tace bamuga ta zama ba, dauke ta muje asibiti. Nan jaafar yahau masu bayanin yadda komai ya faru kuma zuwa asibiti bazai yuyu ba.
Kowa hankalinsa atashe, Aunty Biilki kuka, jaafar kuka, da sauri tafiddo papper da pen ta rubuta mai abubuwa da zata bukata sannan ta aike shi pharmacy suyo wa, da sauri ya fice, baa fi 30 minti ba yadawo da komai, Aunty bilki tahau gyara ta da treating dinta yadda ya kamata, saukin abun Bullet din bai shiga hannu ba, allurai tai mata sannan ta hada mata da drip.
Hajiya kam tarasa shin kuka zatayi ko farin ciki, dukda tasan Ummin ce saida ta duba kirjinta dan tabbatar da Birthmark dinta wanda kowa adangin su yana dauke dashi, saidai kowa da inda aka mai shaidar, farin ciki sosai tayi bayanta gani, daukar Salma tayi ta maidata dakinta hade da kwantar da ita bayan tai mata sauyin kaya.
Palo suka dawo sukayi cirko cirko cike da jimamin abubuwa, Sallamar Junaina ce ta katse masu shuru, ganin yanayin su tahau tambayan make faruwa, babu wanda ya iya amsata, Aunty Bilki tadau jakar ta tayi waje, Jaafar kuwa mikewa yayi ya haura Sama, Hajiya tace "dare yayi, nikam na shiga" mikewa tayi ta shige daki jikin sanyaya.
Tabe baki Junaina tayi ta wuce dakin ta, aranta tana tunanin miya samesu, Wayarta ta dauka dan kaiwa Mujahid Rahoto, sau kusan shida tana kiran sa baya picking haka dai ta hakura.
Lokacin Mujahid na zaune tsakiyar Palonsa, kansa dafe da hannayansa, yana ganin call din Junaina yaki dauka, kuka sosai yake yana tunanin ina Salma ta shiga, babu inda basu bincika ba, babu ita balle labarin ta, fatan sa Allah yasa ba mutuwa tayi ba, idan har ta mutu rayuwar sa naciki hadari.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.