Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 41

****

Cikin light purple arabian gown Salma tayi shirin ta, sauri kadai take ta fita Qrandsquare shopping data sabayi duk bayan sati biyu, agurgurce taje gurin Mom tai mata sallama ta fice waje, nan haraban gida ta iske Salim na waya, ganinta yasa shi katse wayan tamai kyau sosai.
"Salma sai ina, irin kyau haka ? Washe baki yayi.
Yatsine fuska tayi ayayinda take kokarin bude motar, tace "yau Sunday kaima kasan inda xani ?
Riko hannuta yayi "ki tsaya na kaiki
Kallon karfin hali barawo da sallama tamai tace "kabari next tym sai muje" janye hannu ta tayi yayi sauri kara rikota. "Salma nafara gajiya da wulakancin ki, kin dauki ni kamar wani puppy dinki, you keep using me when ever you want people to detest you amma damun keb'e saiki fara yank'wanani kuma am sure kina kaiwa wasu maza kanki cox d first tym dana gankii arayuwata nasan you aint a good person"
Dariyan rainin wayo tayi.
"Ya salim you're funny, ka fiya zalama shiyasa bazan iya baka kaina ba"
Ranshi ya baci matseta yayi gam jikinsa yanai mata mugun kallo itakam banda dariya ba abunda take, shigowar Motar Daddy ne yasa shi sauri sankin ta, amma tuni Daddy ya gansu, da gudu Salma ta karasa gurinsa tamai sannu da zuwa kasancewar yayi bulaguro, sosai yaji dadin ganinta sun dan gaisa tamai bye to koma mota taja tabar gurin.

Sai sannan Salim ya gaida Daddy, Mugun kallo yamai, cikin fada yafara cewa "ban hanaka zuwa inda Salma take,
Shuru salim yayi ran shi na zafi, Daddy ya cigaba "kaga yadda na taimaka na dauko ka harka zama wani abu, i wont hesitate throwing you out of this house if you dare hurt my Precious Daughter, kar kaga duk abunda take bana tankawa ina sane da komai, i trust her kuma nasan bazata bani kunya ba, so you'd better keep your distance".
Kai Salim ya sunkuyar, yagane inda zancen Daddy ya dosa, kar shaye shayan shin yayi effecting Salma, saidai ayadda yakejin son Salma bazai iya barin taba, Wucewar sa Daddy yayi bai jira abunda xai ceba.

***
Hankali kwance Mujahid yake tukin sa, gidan su Faiza zai je wanda ya zame mai jiki duk weekend, saidai baya zuwa hannu empty yakan dan siya mata kayan dadi, yanke shawaran tsayawa Grand square yayi dan siya mata kwamulashe.
Salma na isa Grandsquare parking tayi ta karasa ciki, tsayawa tayi a tsakiyar gurin tanai duban wana direction yaka mata ta fara bi, dan ko wana abu da maajiyar sa.
Gurin kayan kwalliya tayi tunanin bi kafin taje bangaran su Chocolate, hankali kwance tafara takunta mai daukan hankali, daidai kwanar dazai shiga siyan fruit ya hango ta tafe, saurin boyewa yayi gudun karta ganshi har ta iyo ta gabansa ta wuce, gurin kayan kwalliya ta tsaya ta loda iya son ranta sannan ta karasa gurin chocolate ta diba, duk akan idonsa, tafiya tacigaba dayi taji ta gware da mutum Handbag dinta ya subuce kasa kayan ciki kaman su pen da powder suka zubo, cikin sauri ya kwashe ya maida mata cikin jakar yayi gaba.
Bata gane waye ba saidai taji haushi yadda bai tsaya bata hakuri ba alhalin shi ya shigo gabanta, tsaki taja ta karasa counter tayi payment sannan taba security ledar kayan dan rike mata, fitowa taxoyi wani alarm dake kofar tayi kara, Security dake gurin yace Hajiya akwai wani abu ajakanne, harara takai mai
"do i look like a terrorist"
"Ba haka bane hajiya, ina kayan da kike siya"
Da hannu ta nuna security dake tsaye kofar da ake fita da kaya.
Alarm dai sai kara yake gashi kuma baa bari ta fita ba, gabanta ne yafadi ta tabbatar akwai wata kullalliya.
Wata mace ce ta karaso gurin, da alamun itace babban security agurin, warce jakan tayi tana fadin "Madam wetin dey inside d bag.."
Shuru salma tayi dan bata fahimci komai ba,
Zazzazge jakar Matar tayi saiga Gold Ring mai dauke da Tag din kudinsa 50k ya fado.
Ware ido Salma tayi adan tsorace tana tunanin yaushe ma tabi hanya juweries.
Mugun Kallo matar tayi mata sannan ta damko hannunta.
"Thieve, ole, dama sata ke kawo irin ku, toh i don catch you..
Iya tsurewa Salma takai, idan akwai abunda ta tsana bai wuce amata shairi ba, balle Sata da tunga uwarta ta haiheta bata taba iya, wata zuciyar tace kin manta kin sace hoto da agogo da Id, Saurin kawai da Thought din tayi tana fadi aranta "wannan ba sata bane, neman magana ne kuma aina maida komai, hoton ya rage shi kuma nawane" (who dash you)
"Ole muje office" taji muryar matan, kokarin janta take kaman akuya.
Marairace fuska Salma tayi tace "Madam dan Allah kiyi Hakuri, bazan sake ba"karasa maganar tayi kaman xatayi kuka.
Security dake gurinne suka bawa Madam din hakuri sannan ta kyaleta bayan ta gama mata wankin babban bargo, Salma kam tagama kulewa ko takan kayanta bata biba ta rugu waje ta fada cikin motar ta.

"Kawo nakai mata" Mujahid ya yace da Security dake baza ido yana neman hanyar da Salma tabi, ba masu ya bashi.
Dariya Mujahid yayi ya nufi inda ya hangi motar ta, aranshi yanai jin dadi yau dolene yaga hawayan da take ikirarin bawanda ya isa yasata zubda shi.

Kan Sitiyari Salma ta daura kanta, kuka takesonyi saida bazata yiba saboda wasu dalilai, sosai Idonta yayi jajir tahau tunanin yadda ring ya shigo jakarta, "kodai wanda ya fadarmin da jaka ne ya...." Knocking din window ne ya katse mata tunani, dagowa tayi sukayi four Eyes yana sakar mata wicked smile, kofar ya bude ya daura mata kayan acinyarta sanan yace "long time no seen"
Kallon shi tayi ta tuna da wanda ya bigita,, aranta tace wato shine yaja mata cin fuska.
Shuru tayi, bazata iya magana ba karya gano yadda ranta ke bace, dan kuwa kiris ya rage tayi kuka.
Hannu motar taja ta rufe ta kunna tayi gaba, sosai Mujahid yaji dadi, koba komai ya ajiyeta in her place, next tym she will learn to respect herself, saidai rashin kukan ta yabashi haushi.
Dariya yayi ya koma motar sa yaja gidan su Faiza, taji dadin ganinsa, sun jima suna hira kafin nan ya gangaro mata wata tambaya.
"Faiza ya student dinki, hop dai yanxu bata miki raini...
"Wa kenan" Faiza ta tambaya, dukda tasan wace yake nufi.
Yace "ko Ummi koya take da suna, yarinyar nan mai harka da area boys"
Tsaki tayi tace "Salma xakace, sam bana kaunar yarinyar nan... "Karashe maganar tayi tanai duban fuskan shi, saidai bata gano komai ba.
Shuru yayi tace "Mjay don't tell me you're fond of that girl ?
Dariya yayi ya share zance yace "ya bazawarai, nifa ke nake jira kiyi aure sai nayi, kinsan friends dont abandon friends.
Harara takai mai cikin salon wasa, azuciyar ta taji haushi abunda yace.
Tace "kamin adduaa Allah ya kawo na gari"
"Okay tam".
Wata hira suka kama sun jima tare daga bisani ya koma gida.

****
Washe gari..
8am Salma ke da Lecture, 7.30 ta fito fuska ba annuri, zuciyan ta na radadin abunda ya faru jiya, Daddy da Momy ta iske zaune a dining, Daddy nasha tea, ciki ciki ta gaida su, daga ganin fuskar ta bata cikin walwala.
Daddy yace "Salma make damun ki ?
Kaman zatayi kuka tace ba komai, juyawa tayi ta fice daga palon, mikewa Mom tayi da sauri zata nufeta, Dad yayi saurin dakatar da ita
Yace "karki damu, indai Salma ce she will over come any obstacle, mu bata time"
Zama Mom tayi jikin ta duk amace, tana son Salma duk wani damuwa ta Salma bataso.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.