Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 41
Mikewa Mujahid yayi da axama ya tsaya bakin window kallonta, saida yaga ta shiga mota taja sannan ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira wata namba, bugu daya aka dauka.
Cikin masifar yace " wato kasheni kukai niyyan yi ko ?.
Daga can mutumin daya dauka yace "Oga kayi hakuri, amma ai kai ce muyi making komai ya zama real, thanks goodness yarinyar tayi intervening da wuri.
Dogon tsaki Mujahid yayi ya katse call din.
Typing din yau sai ahankali wlh, kuyi sorry banyi editing ba....
*#ZSAW*☄
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkar
*This page is Dedicated to my Cousin Sisto, Maryam abubakar Lamin (Maryeama Dasoorh), Love you so much, May Allah guide n shower you his blessings*
37 - 40
Bayan Kwana biyu da aukuwan lamarin sannan Mujahid ya fara fita office. Bai kuma bi takan Salma ba. Da azahar bayan ya fito sallah Masallacin su na office ya hadu da Salim tsaye yana waya, cike da farin ciki yake wayan, da alamun kuma da mace yake, Mugun Kallo Mujahid ya watsa mai sannan ya wuce zuwa office dinsa, zama yayi yana tunanin kardai da Salma yake waya, haushi ne sosai ya turnuke shi, Wayarsa ya fiddo ya lalubo lambar salma, son kiranta yake amma baisan abunda zaice ba asalima tun ranar yake saurara kiranta kodan tamai ya jiki, amma shiru. Dabaran Turo mata text msg yayi.
Salma zaune a kan kujerun dake ajiye gefen faculty dinsu tare dasu shehu da wasu yan ajin su suna tattaunawa game da wani course da zasu shiga test, wayarta ke kunnata tana waya da Salim, murya kasa kasa hade da dariya, katse wayan tayi, shehu yace "wannan dariya fah ?.
Tabe baki tayi, tace "yayana ne, lallab'ashi nake yakai min motata gyara ban iya jure shiga taxi"
Yace "kai yaune fah kawai kikazo da taxi, Yayan nan naki kodai dashi zaai ?
Wani mugun kallo takaiwa Shehu, ba shiri yayi azaman kama kanshi, lumshe Ido Salma tayi hade da kallon wayarta wanda tun ranar take tunanin zai kirata amma shuru, tanason sanin ya yanayin jikinsa yake, taso zuwa office din Faiza tambayar ta, saidai ta fasa gudun kar girma ya fadi kasa wanwas.. Karar shigowan sakone ne ya katse mata hanzari, tayi azaman budewa ganin Mujahid.
"Hi, kwana biyu, dafatan kin isa gida Lapia ?
Murmushi ta saki, aranta tace "sai yau ya tuna dani"
Reply ta rubuta mai, "ya jikin ka, kashe maganin?
Dadine sosai ya kamashi, baiyi expecting tamai reply da wuri haka ba.
"Am okay, when are you less busy nazo na maki special godiya for saving my life..
Gabanta ne yafadi, itakam bataso su kuma haduwa da daddare dan kuwa tsoron shi take, saidai kuma tana son ganin kyakyawan fuskan sa, tunani ta hauyi can dai tasamo mafita ta turo mai "ina skull yanxu, zamuyi cA test, kana iya zuwa kasame ni by 4pm"
Yana gani murmushi yayi, Mikewa sukayi suka tafi Hall kasancewar lokacin test din yayi.
***
Hudu nayi Mujahid ya karaso yayi parking can gaba da inda Hall din yake, lumshe idanu yayi yahau zama jiranta.
Cikin nutsuwa Fa'iza ta kankamce office dinta, sannan tadau jakarta ta fito, yau bata zo da motar taba kuma batayi tunanin Mujahid ya fito aiki ba saboda condition dinshi, can gaba da faculty tasamu taxi ta tare shi ta shiga yaja, sun shigo round kenan ta hangi Motarsa, saurin tsayar da taxi din tayi tahau duban motan, saida ta hango fuskan shi ta tabbatar shine.
Murmushi tayi aranta tace "ashe ma yazo daukata" wayarta ta duba bataga call dinsa ba tayi tunanin ko rashin netwrk. Sauka tayi daga taxi din ta nufo motarsa sa cikin sauri.
Shikam Mujahid kallon saitin gaban shi yake dan ganin tahowar Salma bai ankaraba yaji anbude kofar gefe an shigo, kallon ta yayi cike da mamaki.
Gyara zama tayi tace, "Mjay aida security ka tura office ya kirani, instead of kayi ta jirana"
Bata rai yayi yace.
"Aiba wajan ki nazo ba, kuma am not your driver..
Dariya tayi, cikin rashin kula da yanayin sa tace "wasa kake, gurina kazo kawai haushi zaman jiran da kayi kake.."
Mujahid kam bai iya cewa komai ba, hankalinsa tuni ya koma kan Salma dake tahowa tana duban cikin jarkata tana lulube, komi take nema, oho, yafada aransa, takaici ne ya kama Faiza ganin inda idanuwan sa ke kalla.
ID card dinta take tunanin kota manta a Hall yasata alube, tana gani ta zuge jakar ta maida hankalinta kan tafiyar ta, murmushi tahau yi ganin motar sa, kadan ya rage ta isa gurin ta lura da Faiza dake hakince kan sit tanai kai mata mugun kallo, gaban Salma ne yafadi, saurin shanye murmushi tayi hade da bata rai, kaman ta fasa karasawa gurin sai kuma ta dake ta karasa saitin gurin da Mujahid ke zaune, kawar dakai tayi gefe tace "sannu"
Kallon ta yayi tamai kyau, kwana biyu nan ya lura ta daina shigar banxa data saba, jallabiya ce baka jikinta tayi rolling da veil din, kallon Faiza yayi da gefen Ido kaman yahau ta da duka, yace "ya test din ?
Haushi ne yakama Salma, "wato bazai ce shigo motar ba nice sanda mai jure tsayuwa, wlh kunyi kadan" aranta tayi magana, Afili tace "Nina tafi sai anjima" kaman zatayi kuka tayi maganar, tafiyar ta tayi bata jira cewar saba.
Tsaki Yaja ya kalli Faiza dake cika tana batsewa yace
"Miyasa kike son janyowa kanki raini, gurinta fah nazo bake ba, anjima kuma idan ta hukuntaki kihau kuka".
Kallon takaici tamai
"Ai tare ta ganmu, kuma ma aina fita matsayi agurinka"
Kasa tankata yayi dan haushi, kunna motar yayi yaga Salma na kokarin Tsayar da Taxi, dasauri yaja inda take yace "Kizo nayi dropping dinki
Sai sannan ta dubeshi, Murmushi tayi hade da ciro 1k dake jakarta sannan ta nuna mai tace ina da kudin motar haya basai an lab'a niba" karawa gaba tayi abunta.
Kulewa Faiza tayi tace "kaga ja'ira ni take gayawa maganar banza baka ce komai ba"
Dogon tsaki Mujahid yaja hade da watsa mata Harara, yace "ki tafi da motar gida zanzo na dauka" bai jira cewarta ba ya bude murfin ya fita, Sakin baki Faiza tayi cike da Mamaki rashin M irin nasa, k'wafa tayi cikin tsananin haushin Salma sannan ta fito ta zagaya gurinsa ta zauna hade da data motar.
Salma na shiga taxi data tsayar, taji an bude kofar baya inda take zaune an shigo, adan tsorace ta kalleshi, magana zatayi taji yacewa mai taxi su tafi, mamaki ne yakamata, "ina ta sa motar" ta fada aranta, batasan ya fito fili ba..
Lafewa yayi kan sit din hade da fuskan tarta sanan yace "nabarwa Auntyn ki ta tafi gida dashi tunda kinki shigowa.."
Kunyace ta kamata, aranta taji dadin abunda yayi tasan kam Faiza taji haushi, matsawa kadan tayi tahau bude wani handout tada ciro ajakar, Murya kasa kasa tace "ya jikin ?
Shuru yayi baice komai ba, dagowa tayi suka hada ido ta wayance da cewa "ba lafi, bruises dinma sun warke," dauke kai tayi tahau bude pages din handout din.
Dogon ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe ido yace, "Miyasa baki kirani awaya ba ?
"Hmm, nayi bizy ne, soon zamu fara exams"
Magana zaiyi Wayarsa tahau ringing, dubawa yayi yaga hajiya, gabansa ne ya fadi, yaushe rabo dayaji motsin su Hajiya tun randa yabar gida, gyara zama yayi sannan ya dauka, gaidata yayi ta amsa ciki ciki, sannan tace "kazo gida kasameni ina da magana da kai ."
Dafe kai yayi kaman yayi ihu, sanin maganarta batada nasaba da wacce take kusa dashi, murya kasa kasa yace "Hajiya yamma tayi, gobe insha Allahu zan shigo"
"Allah ya kaimu" ta fada hade da katse wayan.
Satar Kallon shi Salma tayi tace "wace ce ?
Yak'e yayi yace "mama nace"
Cike da fara'a ta dubeshi tace "i would like to meet her, wana unguwa take ?
Tashin hankali ne ya diran mai, dakyar yace "ba anan take ba, can Sokoto suke zama"
Harara takai mai cikin salon wasa tace "kodai bakaso nasanta ne, naga ai sister dinka anan take skull.."
Dariya yayi wanda da gangan ya tsiro shi gudun karta dago shi, yace "Amina wai, ai sunyi hutu tama koma gida can sokoto.."
Murmushi Salma tayi tace "ayyo" aranta kuma tana tunanin Amina dayace dan kuwa ba Amina sister dinshi tace sunanta ba, bata damu ba ta kawar da tunanin kasancewar taje gidan shi kuma bata ga alamu yana da yan'uwa ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.