Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 23 of 41

****
Har gari Allah ya waye zuwa rana Salma bata motsa ba, da yamma Auntu Bilki tazo takara mata allura sannan ta tafi. Duk shige da ficen da ake akan idon Junaina, tanason Sanin maike faruwa adakin Hajiya, takawa tayi sadaf ta leka ta hangi Hajiya zaune tana jan carbi, Jaafar zauna gefe gado iya abunda ta hanga takoma palo ta zauna.
Kallon Salam jaafar yake cike da tausayinta, fuskarta fayau kaman ka kirata ta amsa, Hannuta ya riko hade da daurawa bisa fukarsa yanai shakar dumi da kamshin hannuta, idonsa sa cike da kwalla, hannusa yakai kan kyakyawan fuskarta yanai shafawa, aransa yace "i'll protect you, til my last breath" baisan maganar ta fito fili ba, Hajiya na jinsa ta mike ta fice daga dakin..
Junai tagani palo bata iya ce mata komai ta wuce kitchen.
Kaman wasa jaafar yaji ta rike mai Hannu da hannuta dayake rike dashi, kura mata ido yayi yaga babu alamun motsi fuskan ta, da sauri ya mike, wayarsa yahau neman dan kira Aunty Bilki, bai ganta ba, ya tuna ya barta a daki, da sauri ya fito dakin Hajiya ya haura sama.
Mikewa Junaina tayi, da gudu ta shiga dakin kafin ya dawo, wata tagani kwance kan gano, karasawa tayi hade da kare mata kallo, tsaf tagane Salma ce data sace ta, "kutumar Uba, yar iskan nan ce a gidan nan" ta fada da karfin gaske, saurin kama bakin ta tayi hade da ficewa daga dakin, dakinta ta koma tahau lalubar Nambar Mujahid awayanta, sai cewa take "tab, wlh bazai yuyuba"
Dailing no din tayi.

Mujahid na zaune office da wusu yan sanda suna bashi feedback akan nemo Salma basu ganta ba, zaginsu yahau akan basu iya aikin su ba, ganin call din Junai yasashi Jan dogon tsaki, "yarinyar nan saina ji ubanta zata kyalleni" ya fada, dauka call din yayi da niyya zazzaga masifa,
"Yaya kasan wana gani adakin Hajiya, yar daban nan data sace ni kwanaki..."..
Azabure ya mike tsaya, "Uwar mi takeyi adakin Hajiyar, how comes taje Gidan...?
"Yaya nima ban sani ba, kaman dai bata da lapia, naga su hajiya sunyi jugum sai kace wata yar uwarsu.."
Katse call din yayi bai tsaya sauraran surutun taba, kallan yan sanda yayi yace ku hada motoci goma da ambulance daya kuje inda zan baku address ku daukon min ita"
Address din gidan yabasu, ya kuma cewa suje yanxu batare da bata lokaci ba yana biye dasu abaya.

Tsaki Junaina taja, tayi kwanciyar ta aranta sai tsinewa Salma take, Jaafar na daukan Wayarsa Dakin Hajiya ya koma, nan ya iske Salma na jijiga tana aman wani bakin jinin, idanuwan ta rufe, tsorata yayi ya kira Aunty Biliki ya shaida mata..
Akidmi tace "jaafar ka kawo ta asibiti, she need blood, idan ba hakaba zata iya mutuwa saboda tayi loosing alot of blood".
"Aunty yan sanda zasu iya kamamu, bakiga duk asibiti ansa securities neman taba"..
Aunty B tace "kazo da ita, zan san dabarar da zamuyi mu shigar da ita."
Hankali tashe Jaafar ya kashe Wayan, Hajiya ce ta shigo dakin, fadamata yadda sukayi yayi.
Tace "dauketa muje mota bamuga ta zama ba" da sauri ya dauki salma suka fice, haraban gidan suka fita suka ga an wangale gate, motar yan sanda mai siren suka gani suna shigowa tare da ambulance.

Cirko cirko Su hajiya sukayi suna kallon Yan sandan da already sun fito, daya daga cikin su ya nuna yace fito da gadon, ba masu aka bude ambulance aka fito da gado, inda Jafar ke rike da Salma suka nufa da niyyan karban ta, hade rai yayi hade da ja dabaya, Hajiya kuwa tsoro ne yaka mata, tahau rokonsu Allah da Annabi, ko ajikinsu, ganin Jaafar sai bata basu lokaci yasa suka nunasa da bindinga, ko gezau bashi da niyyan sakin Salma.
Gefe Oga gurin yayi ya kira Mujahid ya fadamai abunda ake ciki. Daga can karshe layin Gidan Mujahid ke zaune a motarsa yana jiran fitowar su.
Cikin fada yace "you guys are dumb, i dont care koma uban miye zakuyi agidan nidai kawai i want her out of that house dead or alive"..
"Yes sir" dan sandan yace hade da katse wayan...
Kallon sauran yayi yace, ku kwato ta da karfi da yaji...
"A"a hajiya ta fada akidime, mi yayi zafi haka kukeson karasar da ita da ranta, kaga Mujahid basu ita tunda ga ambulance samun lafiyar ta shi yafi komai yanxu. Dakyar da rokon Hajiya jaafar yabar Salma suka daurata gadon suka ja suka bar gidan.
Hajiya kaman zatayi kuka tace "jaafar ya akai suka san tana gidan nan, ina Mujahid kirashi awaya..."
Ran Jaafar ya baci ba kadan ba, sai yanxu ma ya tuna da Mujahid Police ne, magana zaiyi yaga Junaina ta fito tana kyalkyalewa da dariya.
Afusace ya karasa hade da damko wuyar ta, yace "mai kika cewa Mujahid..
Ware ido tayi atsorace, tace babu"
Yace "kin dauka bansan kina min bincike kina kaimai rahoto ba, ki gayamin abunda kika fadamai kafin nagama dake.."
Hajiya ce tayi saurin shiga tsakanin su, "miye haka jaafar, zaka kashe tane.."
"Hajiya ki tambaye ta kiji, bakin su daya da Mujahid, how comes suka san Ummi na gidan nan..".
Kallon ta Hajiya tayi tana cira amsa daga gareta.
Gunguni Junaina tahau yi tace "nifa bansan meke faruwa ba, kawai na kira ya Mujahid na fadimai yarinyar data sace ce ita"
Hannu Jaafar ya daura akai yace "ya salam, amma kin zalince ta, baki ga condition da take cika.."
"Inna ruwana" junaina tafada, wani mugun Mari Hajiya takai mata had'e da nunata da yatsa tace "son zuciya kikayi ko adalci, idan har wani abu ya samu Ummi ki tabbata gidan ubanki zaki koma.." Fuuu hajiya tayi gaba ta koma ciki.
Ihu Junaina tayi tace "na shiga uku, badai Abbana dabaya kaunata ba, wace ce Ummi ? Ta tambayi Jaafar dake tsaye, banza da ita yayi ya shiga motar sa yaja yabar Gidan.

Direct central Hospital suka wuce da Salma aka bata gado, da sauri Mujahid ya karaso gurin ganin Doctor ya fito daga dakin.
Doctor yace "tana bukatar jini, saidai bamu da type dinta, nan da 30min xaa kawo ledar type dinta"
Ahasale Mujahid yace "Kaga Doc bana son wasting tym, muje adibi nawa asamata"
Doc yace "ba matsala, inda jinin ku yazo daya muje a diba"
Da sauri suka shiga lab akayi yan aune aune jini yaxo daya aka diba sannan aka karawa Salma, bayan Doctor ya fito daga dakin yace da Mujahid suna sa ran farfadowar ta nan da awanni takwas.
Farin ciki sosai Mujahid yayi ya k"usa kai cikin dakin, kusa da ita ya tsaya yana kalon yadda ta rame farat daya, sonta sosai ke ratsa mai zuciyar saurin kawar da sonta yayi a zuciyar sa sannan ya cire handcuffs a aljihun sa ya sak'ala hannuta daya da karfan gadon, fuska ba annuri yakai hannun sa kan fuskar ta yana shafawa yace "bazaki mutu ba, bazaki gudu ba sai kin gane kuran ki......
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)

54

Yafi minti goma tsaye kanta yana taunting dinta da mugayan kalamansa marasa dad'i sannan ya zura mukullin cuffs din a aljihu ya fito daga dakin, fuska daure ya dubi yan sanda uku dake gurin sannan ya gargad'esu da karsu bar kowa shiga dakin idan ba Doctor ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.