Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 37 of 41
Gidan su Salma Mujahid ya nufa, dakyar ya iya samun ganin Mom a haraban gidan saboda yawan mutanen dake cikin gidan, fuska daure tamai iso saboda haushin su Hajiya da Annah da takeji.
Hankali tashe yahau tambayar ta ko Salma na gidan, ranta ne yakuma bacci da sabon rainin wayon da takeji, banza tayi dashi saida yace mata Annah tacemai batasan Inda Salma take ba sannan Mom ta saurare shi, mamaki ne yakamasu, Mom ta kwalla kiran maigadi ta tambayase ko yaga fitar Salma, yace tunda ta dawo baiga fitar taba. Hakalin sune ya kara tashi Mom ta kira Salim awaya, koda ya iso tsaye yaga Mujahid da Mom akidemi, cike da tashin sense Mom ta tambayashi koya ga Salma, ware ido yayi kamar gaske yace bai ganta. Salati Mom tahauyi. Mujahid kam kallon banxa ya aikawa Salim dan kuwa bai yadda dashi ba, karasawa kusa dashi yayi da niyyan mai magana yaji kamshi Salma ya ajikinsa, kaman jira yake ya damko wuyan sa, cikin huci da haushi yace "ina ka kaimin Salma ?
Bata rai salim yayi ya turesa, Mujahid yakai mai naushi, nan dambe ya chakwade, Hankalin Mom ne yatashi gudu kar yan ciki su fito, mai gadi ta kuma kwallawa kira, yazo ya shiga tsakanin su dakyar.
Saurin jan Salim tayi gefe ta kalli Mujahid, tace "yanzu ba lokacin fada bane, nemo inda ta shiga yakama ta kayi, tun kafin Daddy yasan cewa b'ata tayi, kuma kai kasan Hajiyar ku bazata so jin wannan mugun labari ba, duk inda aka shiga kaine main suspect saboda dakai tayi waya last kafin na nemeta na rasa" tana gama maganar taja Salim sukabar gurin tanai bashi hakuri.
Fuzgar da Iska Mujahid yayi ya juya ya fice daga gidan ya tsaya nan waje bakin motar sa, yasan cewa indai Salma is missing bashi da haufin cewa babu hannu Salim ciki, amma yazai yi bashi da evidence da zaa yadda dashi, duk Annah ta kara wuta cikin lamarin, inda tun asali batai karya ba da tuni ya binciko inda Salma take.
Haushi ne yakamasa baima san ta ina zai fara ba, wayarsa ya ciro a aljihu ya kira Mubarak, sun jima suna waya sannan ya katse ya shiga motar sa yaja yabar gurin.
Masoyana kuyi hakuri da typing din yau sai ahankali...bana jin dadin jikina kwana biu, yanxu haka am on medication.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
62
Gabad'aya Mujahid ya gama birkicewa, cike da kid'ima yahau laluban mukullin motar sa dake aljihun wandon sa.
Saurin rik'osa Abdul yayi yace,
"kabar tayar da hankalin ka, koka nufeta ba sauraran ka zatayi ba ayadda ka mugun b'ata mata rai"
Dafe kai Mujahid yayi cike da tsantsan tashin hankali, duban Abdul yayi da rinannun idanuwan sa da suka sauya launi zuwa ja.
"Ya kakeso nayi, dole naje na fahimtar da ita".
Hannu Abdul ya daura bisa kafadar sa.
"ka bari ba yanzu ba, she need some time"
Shuru Mujahid yayi batare daya iya cewa uffan ba, sun d'an jima nan tsaye kaman sanduna daga bisani suka koma ciki. Wayarsa dake ajiye kan kujerar palon yadauka ya kira Salma, saidai ba bugun duniyar dabai yiba fir taki dauka.
Akan titi kuwa wuta sosai Salma take bawa motar ayayinda take zubar da hawayan bak'in ciki, dakyar ta iya karaso da kanta gida, Afusace ta bude motar ta fito batare da ta tsaya bi takan wayarta ba, wani mugun juwa da azababban ciwon kai ke barazanar barar da gabobin jikinta.
Adaddafe tafara takawa zuwa bangaran Salim wanda ayanzu ta tabbatar shi daya ke mata son gaskia, sab'anin da datake mai kallon wawa, soko marar hankali, yaudai gashi wanda take ma kallon zinare yazame mata bak'in gwarwashi.
Kuka take sosai ta k'usa kai cikin palon, kwance ta iske shi bisa doguwar kujera duk jikinsa mace, da alamun ma cikin zufin tunanin yake, sunansa ta kira cikin sheshek'a tare da fad'awa jikinsa, Atsorace ya dagota ya yunkuro zaune yana kallon ta, duk ta gama birkice sa da kamshin jikinta, tunda suke gidan bai taba ganin ta cikin mugun yanayi aka ba.
Cike da firgita yahau tambayan ba'isin kukan ta, kasa magana tayi saima sautin kukan ta daya tsanan ta, hankalin Salim ne yatashi, dakyar ta iya cewa
"Yaya kaina ke ciwo"
Janyota yayi ta kwanta bisa kirjinsa yanai mata sannu hade da bubbuga mata baya cike da lallami, sosai yaji dadin yadda suke makale da juya, aransa sai aiyanawa yake dama tazo mai yanzu yakamata ya mayar da Salma tashi ta har abada.
Salma kam kukan ta take, ko tuna abunda ya faru bata sanyi, yadda zata gayawa Daddy ta fasa auran Mujahid kadai ne matsalan ta, tunda tun farko ita tace tagani tanaso bawai tursasa ta akayi ba.
Dagota yayi ahankali ya jingine ta jikin kujerar, cikin sanyi murya yace
"bari nadauko miki maganin ciwon kan"
Kai kawai ta daga mai, ya wuce dakin sa, side drawer ya bude ya dauko wani magani dani kaina bansan na miye ba sannan ya fito yadauki bottle water dake ajiye center table ya karasa gareta..
Salma kam bata kaunar magani, dakyar da lallami ta yadda tasha pills guda biyu daya dauko, ubansa tayi ido jajir tace, "nagode"
Aranta kuwa danasani take dama tun farko shi ta baiwa soyayyan ta, koda yake bai baci ba zata fadi ma Daddy shi takeson aura ba Mujahid ba. Shingid'e kanta tayi kan kujerar, Murmushi Salim yayi yahau goge mata hawayan fuskar ta, bayan kaman minti biyar tafara ji nauyin jiki da kasala, mikewa tayi tace
"yaya sai da safe"
Yace "Allah ya kaimu" aranshi kuwa yace keda ganin safiya badai a gidan nan ba.
Taku tafarayi ahankali taji mugun hajijiya, abubuwan dake palon biyu uku tafara ganin su, bata aune ba taji ta ta fadi kasa wanwas.
Farin cike ne yakama Salim, mikewa yayi ya tako inda take ya tsugunna yanai mata shuumin kallo sannan ya mike ya leka waje ta window, shuru babu kowa, daukar ta yayi suka fito haraban gidan ya nufi inda motarsa ya bude yasata sannan ya shiga yaja yabar gidan @ 360... Ba zaice ko ina ba sai Badoo Quarter, agaban wani gidan mai kyau madaidai ci yayi parking ya fito ya kuma daukar ta suka shiga ciki, palon mai shima mai kyau yasha kayan alatu, dakin ya bude yashiga ya ajiyeta kan gado sannan ya fito ahankali ya kulle gidan, Ajiyar zuciya ya sauke ya koma motar sa yaja ya koma gida.
[9/7, 12:38 AM] Xarah Bukar: ​​​Zuma Sai Da Wuta
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
(Aunty Cute)
NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}
Allahu akbar kulu'nafsi za'ikatu mauti, Allah yaji kanki da rahma Maman besty Yar ficika. May jannatul Firdausi be ur final destination.
64
Kuka sosai Salma take yi, duk yadda taso fita gidan kasawa tayi kasancewar duk kofofin tamke suke da mukulli, ganin ba sarki sai Allah yasa ta lallashi kanta tadau abuncin daya kawo taci ta kwanta nan kasan dakin cike da tausayin kanta. Salim kuwa ganin yadda Mom bata zarge shi da komai ba yasashi samun karfin gwiwa, dakinsa ya nufa ya shirya kayansa tsaf cikin akwati cike da murnan gobe zai fece zuwa kasar Ghana da salma koda kuwa baa fasa daura mata aure da wanda yafi tsana a duniya ba, shine kawai ya gudu da Salma shine muradin sa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.