Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 41
Yana isa NPF (Nigeria police force Q), parking yayi ya fito k'arasawa dept dinsu ya hadu da abokin sa kuma abokin aikinsa Mubarak. Gaisawa sukayi har zai wuce ya tsaya yace.
"Mubarak nasan kasan manyan mutane agarin nan".
Dariya Mubarak yayi yace "ka shirya aure kenan, diyar wace ce yanzu nama hanya"..
Tsaki Mujahid yayi.
"Kaima kasan babu wanan a lissafina, kasan wani babban mutum Alhaji Abbas Maccido a agarin nan ? Ya fada, dukda baisan waye Alhajin ba yasan mai kudi ne ganin motar da shameless daughter dinsa ke driving.
K'ad'a kai Mubarak yayi yace
"nasan shi, babban dan canji ne (Burea de change) mai kudin gaske wanda anjima ana damawa dashi"
Numfashi Mujahid ya sauke.
"Good, inason details din komai game da family members dinsa, And plz make it Quick".
Cigaba yayi da tafiyan sa batare daya jira cewar Mubarak ba.
Dariya Mubarak yayi ya wuce, aranshi yana adduan ko abokinshi ya fara sanya So aranshi.
***
Yau lecture free day, ko wanka batayi ba ta fita palo yin breakfast, wanda k'idar gidan ne dole by 8am a hadu dining yin breakfast kafin nan kowa ya wuce zabgogin sa.
Kayan bacci ne jikinta riga da wando cotten, gashin kanta baje babu kallabi, Su biyu ta tarar zaune kan dinning taja kujera ta zauna hade da yin mik'a da salati sannan ta kalli iyayan hade da k'ok'arin fara had'a tea.
"Dad n mom good morning"
Kunnan ta Mom ta rik'o tace,
"Salma bana hanaki fitowa da Nyt wear ba, idan Salim ko wani ya ganki haka fah".
"Kai mom bacci fah xan koma idan na gama"
Katse su Daddy yayi da cewa, "yau baki da lectures ne ko wani bak'in halin kikayi aka koroki " fuska daure yayi maganan.
Shagwabe Fuska Salma tayi, aranta tanai fadi "Daddy dai zancen shi kullum makaranta, kuma ma babu wanda ya isa ya koreni, i can defend myself".
Afili tace "Daddy bamu da lec yau, sai gobe muke da Math 105"
Yace "Good, make sure kiyi revising kafin kiyi bacci".
"Yes, Daddy" ta fada tanai dariya kasa kasa.
Mik'ewa Daddy yayi sannan ya kalle ta yace "ki zauna a gida, banso na dawo daga office naji labarinki in some kind of trouble"
"Okay Dad, Allah ya dawo dakai lafiya"
Ta amsa.
Murmushi yayi sannan ya wuce, mik'ewa Mom tayi hade da kai mata duka tace "kin daiji abunda yace wlh Salma ki kiyaye ni"
Dariya tayi.
"Momy mi nayi kuma".
Harara mom takai mata sannan ta juya da azama tabi bayan Daddy rakashi bakin mota.
Kad'an ta iya cin abinci ta tashi ta koma Daki, jakarta ta jiya ta fiddo daukan handout dinta taga frame din hoton sa, Dogon tsaki taja, harga Allah ta manta da hotonsa a jarkarta, wani mugun haushin sa taji tunawa da yadda ya zage su jiya. Daukan Frame din tayi ta ajiye shi kan Console daidai inda hotonta dana Momy ke ajiye, harara hoton tahau yi taji an turo kofar dakin an shigo, da sauri ta kife frame din sannan ta juyo adan tsorace, ganin wanda ya shigo yasa ta daure fuska.
"Ya Salim miye haka, jifa yadda ka tsorata ni ko sallama babu ka fadomin daki"
Karasawa yayi ya tsaya gabanta hade da kai hannu bisa gashin kanta yanai shafawa.
Yace "ai nanma dakina na, yaushe kuma kika tsiro da sai nayi sallama zan shigo"
Hannu yakai kan habarta hade da dago fuskan ta sunai fuskanta juna, yacigaba "Miye kike boyewa bakya so nagani, kinsan dai no Secret tsakanin mu"
Janyota yayi jikinsa yanai kokarin hade bakinsa da nata, tayi sauri matsawa gefe hade da kara tamke fuska
"Oh yaya plz stop it, you're getting too close"
Hannu ta ya riko yace
"Just a kiss saina tafi, kinga babu wanda ya ganmu".
Takaici ne ya kamata
"Why cnt you understand, i don't have any feelings for you, tayama zan yadda kayi kissing dina cikin gidan iyayena adakina for dat matter"
Idon shine ya fara sauya launi, yace "karya kike salma, duk yadda kike hugging dina muke holding hands sannan kice baki da feelings, i know you love me kawai bakya son nuna wane".
Dafe kai tayi cike da takaicin abunda yace.
"I swear i dont love you kaman yadda kake tunani, d only people i love sune Daddy, mom n you, plz ka bini ahankali kar love din yan'uwantaka da nake ma ta koma Hatred"
Kaman zaiyi kuka yake kallan ta, yace "Salma ina sonki"
Dauke kai tayi gefe, yayi gaba zai wuce tayi saurin rikon hannu shi ya juyo suna fuskanta juna.
Tace "yaya am sorry, babu so araina dan Allah karka ji haushi na"
Murmushi dabai kai zuciya ba ya kirkiro yace "ba komai, i hope randa kikasa so aranki ni zaki so".
Dariya tayi, dan abune ne mai wuya, tace "yaya by 9pm idan ka dawo aiki, zamuje Officers club chiiling, zaman gida ba dadi"
Ware ido yayi, yace "ba ruwana, kinsan dai Daddy ya hanaki fitan dare"
Shagwabe fuska tayi tace "don't worry satar fita zanyi yadda bazai gane ba, ko kuma nazo part dinka na boye idan yayi bacci sai muje"
Dariya yayi yace "nice idea, nizan wuce office, am getting late"
Hannu shi ta saki tace okay bye"
Sannan ya fita sukayi kicibis da momy a palo, kallon tuhuma tamai dan tuni ya riga kowa breakfast yace ya tafi ashe yana nan.
"Mom agogona dana bata ajiye naje karb'a" ya fadi cikin muryan marasa gaskia.
K"wafa Mom tayi batace komai ma ya fice cikin sauri.
****
Bayan Magrib Mubarak yasamu daman harharda Details din, zaune yake a office din yana dannan laptop din gabansa saidai rabin hankalinsa yayi gida, sarai yasan yama Hajiya laifi amma taurin kai bazai barshi yaje ya fuskan ceta ba.
Knocking Mubarak yayi ya shigo bayan anmai izini, zama yayi kujeran bak'i yana murmushi ayayinda Mujahid ya daure fuska yanai mai kallon dami kazo.
"Kwantar da hankalin ka nasamo ma komai akan Family din Alhaji Abbas Maccido"
Gyara zama Mujahid yayi yanai duban sa.
Mubarak yace "Alhaji Abbas matar sa daya Hajiya Zaituna da kuma diyar su tilo Salma, da wani saurayi da suke rike dashi a gidan tun yana yaro Salim ne sunan shi"
Anzo gurin, k'ad'a kai Mujahid yayi, sai yanxu yagane ashe Salma da Salim ba siblings bane, saidai akwai wani abun dake tsakanin su ganin yadda sukai ta mannewa juna jiya.
Duban Mubarak yayi yace "baka da komai akan Salma".
Kashe mai ido Mubarak yayi yace "kodai kana ciki ne, kaga yar kyakyawa ka susuce"
Tsaki yaja, aranshi yanai mai zaiyi da Bak'ar karuwa.
Afili yace,
"baka amsamin tambaya taba"
Nisawa Mubarak yayi "Ba wani abu akanta, tayi secondary skull dinta a London, uban nata yaso tayi jamiar acan taki zama fir ta gudo Nigeria, uban nata sam baya wasa da karatun ta, yanxu dai nan gwagwalada take 100 level"
Jinjina kai Mujahid, yayi yanai zancan zuci.
"Tabbas biri yayi kama da mutum, sam yarinyar batta da tarbiyya amma yayi alkawari koya mata hankali da samun tarbiyyan da ubanta bai bata ba"
Sun jima suna magana daga bisani Mubarak ya fice daga office din.
Mikewa Mujahid yayi ya tattare komai gefe sannan ya fito, parking lot ya nufa ya hadu da Salim shima zai shiga motarsa, wani kallon suka aikawa juna dani kaina ban tantance kallon miye ba sannan kowanne su ya shiga motar sa yaja.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.