Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 41
"Bari ma dai na kalli useless girl dinnan"
ya fadi aransa, juyawa yayi ya kalle ta, yarinya ce da iyakacinta 18 to 19, kyakyawa black beauty, jikinta sanye da white pencil jean da red top, da rad hulan yemi alade daure bisa kanta, kai komo take tanai duban agogon hannuta.
Mugun tsaki yaja hade da dauke kansan, he cnt believe abunda ke faruwa, amma yarinyar ta gaba dashi da irin insult data mai.
Tana ganin Motar Salim ya iso ta sauke numfashi, fitowa yayi tayi sauri karasawa gareshi, hade da kaimai hug
"Thank God yaya ka iso on tym" ta fade cike da murna.
Janyeta yayi yace "keda waye, miya faru ?
Hannu tasa natai nuna mai motar tana tab'e baki.
Duban motan yayi, atake yasha jinin jikinsan ganin motan Ogan sane.
"La'ilah mai salma ta tsokano mai yanxu" ya fadi aranshi.
Shikam Mujahid ganinsu ta side mirrow yasa shi kara daure fuska hade da fitowa yana masu mugun kalloi, hararar sa Salma tahauyi sai sannan tagano Guy din cikin frame din ne, mijin tsohuwa Fa'iza atunanin ta, saidai dalilin dayasa yake binta shine bata sani ba, kallon Salim tayi da tuni yayi tsuru tsuru tace
"what are you waiting for, kayi arresting dinshi mana"
Karasa wa gurinsa Salim yayi, hade da risinawa yace
"Sir kayi hakuri, kanwa tace ay mata uxuri"
Girgiza kai Mujahid yayi yace,
"atunanin you are d useless person a family dinku ashe dai kana da kanwa data fita zama useless and shameless"
Shuru Salim yayi yasan hakan zata kasance.
Salma kam tagama fusata da abunda yace, tace "i tink you're d shamless person here, jibeka sanye da suit kaman mutum arziki,
Sauri rufe mata baki salim yayi
"Plz salma kiyi shuru
Cire hannusa tayi cikin masifa tace "haba yaya kanaji yana xagin mu, who the hell is he, dan kawai shida matarsa suna aiki saisu nemin raina mutane, or do they tink d world revolve around them"
Janye ta salim yayi sauri yi, yanai bawa mujahid hakuri, saidai kasan zuciyan shi yaji dadi yadda Salma ta mayar mai magana, suna cikin haka Fa'iza ta karaso
"Mjay make faruwane"
Nuni yay mata da hannu ta shiga motar sannan shima ya shiga, ran shi ya gaba bacci.
"Ban taba sani apart from student akwai dabbobi anan ba"
Kallon Salma tayi dake tsaye gefe Salim na bata baki,
tace "miya faru"
Yace "stupid gal din ta dauka sonta nake, dan kawai munyi crossing path daxu da yanxu"
Tsaki faiza taja tace "Salma Abbas maccido, ai sam yarinyar bata da kunya ga bin maza, ina zargin ma barauniya ce
Tayar da motar yayi yace "mita sace maki"
Shuru Fa'iza tayi dan kuwa bata da evidence tunda bata ganta ba, amma tana zargin itace.
Tace "haka naji wasu student na fadi.
Tsaki yaja ya figi motar hade da buda masu kura ya wuci, rikota Salim yayi yace "salma cool down mana, so kike yasaki a prison, babban police nefa".
Kaman xatayi kuka tace "and so, wana law ne yace yamin rashin Mutunci".
Masifa sosai salma tahau dakyar Salim ya lallbata ta shiga motar ta taja yanai biye da ita a tasa motar har suka isa gida hadaddan gidansu dake Asokoro.
Suna isa momy ta iske zaune a palo, da gudu ta karasa gurinta fuska ba walwala.
"Yau kuma wace tsokana kika iyo"
Gunguni tahau yi
Salim yay mata bayani.
Haushi ne ya kama Mom tahau ta da fada, "nikam nagaji da fitinar ku, yau salim kaine gobe kuma itace, bari dai Daddy yadawo".
Hankalin Salma ne ya tashi tana mugun tsoro fadan Daddy, shiyasa akodayaushe take kaffa kaffa, hakuri tahau ba Momy kamn xatayi kuka, dakyar mom tA hakuri tanai tsokanan ta maganinta Daddy.
Banda Zagin salma ba abunda Fa'iza take a motar har suka isa gidansu dake Garki 2,
ya ajiyeta
Yace ki tabbata motar ki an gyara nagaji da zama driver dinki".
Murmushi tayi tace "ba damuwa sai munyi waya"
Bye tamai sannan yaja ya koma office shidai Gida nedai bazai jeba.,( ni xarah nace xaka hadu da Hajiya)
Tana shiga Gida, Umma ta fake ta da Ido alamun tuhuma, sanna tace
"Faiza idan yaron nan sonki yake ya turo ayi magana, nagaji da wannan dangantakar taku, kusan shekaru ashiri kuna tare kinyi aure harkin fito kuma still kuna tare idan sonki yake ya turo.
Shuru Fa"iza tayi, ita kanta tarasa meke cikin zuciyar Mujahid, tun suna secondary skul suke tare as friends har yau kuma banda wanan bataga alamu love ba, tace
"Umma bafa saurayina bane abokina ne, kuma ma shifa babu so aranshi"
Kwafa umma tayi
"Karyan banza, duba fah yadda yake ji dake, ko gidansu ansanku tare, wa zaku rainawa hankali"
Faiza kam bata iya cewa komai ba ta wuce ciki, Allah yaga zuciyanta tun kafin auranta na farko takeso mujahid ganin bashi da niyya yasa tayi auranta gashi ta fito ba abunda ya canxa.
***
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: *Zuma sai da wuta*
~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
Happy birthday *Billy Galadanci*, Wishing you more perfect years ahead, its you day Have fun 🎈
*Wannan shafin naku ne, Hauwa shehu, maman safara da Aisha ture nagode matika da soyayyar ku gareni*
Wishing you safe trip to Birnin shehu, Feedoh Deedoh (Aunty yar ficika 😜), kina isa kuma ki aikomin da Matata gimbiyata, Sannan ki biyo ta gida Muci Rengem 😋😋😋😋😋
11 - 14
**
Cikin kayan yan sanda yayi shirin sa tsaf sannan ya sauk'o k'asa, jin shuru a palon yasanya shi ficewa waje da azama gudun kar hajiya tasan da fitar sa dan kuwa wasan b'uya yake da ita, adaran jiya ma cikin tsadaf ya shigo gidan yaci sa'an Hajiya ta jima da bacci.
Duk akan Idon Junaina dake tsaye ta window kitchen tana kurban tea, jikin ta tsaye da uniform na makaranta. Ajiye mug din tayi tama mai aikin su Lami sallama sannan ta fito waje haraban gidan inda motar ta ke ajiye, shi kuma alokacin yake kokarin tayar da tasa.
Murmushi yayi ya dubeta.
"idan bazaki damu ba kizo nayi dropping dinki"
Kallon gefen ta tayi dan kuwa batai tunanin da ita yake ba, ganin ita dayace yasa ta gano da ita yake.
Farin cikine ya cikata.
"Da gaske yaya.."
Kai ya d'aga mata, da sauri ta zagaya ta shiga ta zauna fuskar ta dauke da murmushi.
"Yaya ina kwana"
Ta fad'i.
Bai amsa ba yace,
"Hajiya bata ce maki komai jiya ba"
Kallon rashin fahimta tamai.
"wana abu kenan"
Daure fuska yayi yace ba komai sannan yaja motar.
Tace,
"ya Mjay zaka dawo daukana kenan
"A'a"
Ya fad'i atakaice.
Kallon shi tayi kaman zatayi kuka, aranta tanai takaicin gwanintarsa na kaita skull alhalin ba dawowa daukar ta zaiyi ba, kodayake ta riga ta gano shi, bata da wani amfani agurin sa sai yana neman information gurinta yake bata fuska.
Basu kara magana ba har suka isa premier Academy babu wanda yace uffan.
Sauka tayi motan, kafin takai ga mai magana yaja motar yayi gaba.
Guntun tsaki taja.
"Baima damu da yadda zan koma gida ba" aranta tayi maganar.
Murya k'awayanta taji abaya sunai kiranta, sauri sakin fuska tayi hade da sakin murmushi ta juya kallon su, kawarta Hameeda tace
"wow badai shine sweetheart dinki ba, gaskia ya hadu acikin uniform".
Dariya Junanai tayi aranta tana tunanin yadda zaici ubanta idan yasan da sunan sweetheart dinta kawayanta ke mai nuni.
Share zancen tayi taja hannusu suka shiga ciki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.