Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 29 of 41

Side drawer Mujahid ya bude yadauko wani magana a tube ya diga a idon, wani mugun azaba yaji, maida black shade yayi ya fice daga d'akin.

Ta bangaran Junai kuwa kitchen ta shiga ta zauna matsar kwalla, koda Hajiya ta fito ta isketa a hakan ba tambayar da batai mata ba taki fad'a mata komai sai cewa tayi cikinta ke ciwo, Palo hajiya ta riko ta suka dawo tanai mata sannu.

Banko kofar Palo Annah tayi batare da Sallama ba ta kutsa kai ciki ta fadin "ba kowa agidan ne ?
Adan tsorace su Hajiya suka juya kallanta jin yadda aka banko kofar, bata yi samma nin ganin taba ba dan kuwa sunyi waya jiya bata ce mata tana tafe ba.
Dakyar Hajiya ta iya hadiyan yawu tace "Annah sannu da zuwa, aibansan kina tafe ba"
Tabe baki tayi ta kalli yadda palon ke haskawa da kayan alatu, tace "yanzu kin ganni ai
Shuru Hajiya tayi, Junaina ta gaidata, nunata tayi da walking stick din tace "kece haka kika girma ?
Magana Junai zatayi Salma da Jaafar suka shigo palon adaidai lokacin da Mujahid ya sauko daga stairs.
Zubamai ido sukayi, ko kallonsu bayi ba, fuska daure ya kama hanyar ficewa, dakatar dashi Hajiya tayi da cewa "bakaga Annah ba zaka wuce ?
Tsaye yayi chak yanai ma wani Annah mugun kallo ta Black shade din fuskar sa, aranshi yace "uhnm sai yadda ta yuyu kenan, nakuda ad'aki mayya"
Afili yace "mai makauniyar nan tazoyi agidan nan ?
B'ata rai Annah tayi ta k'arasa kusa dashi, bai ankara ba yaji ta fara kaimai Duka da Sandar hannu ta tana fadin "uwar ka nazo, dan tselan uwa kawai" ta ko ina tahau kaimai bugu, ihu kadai yarage baiyi ba tsabar yadda sandar keda zafi, Salma kam dariya tahau babbaka wa, ayayinda saura kuma suke kallon Annah cike da takaicin abunda take, Mujahid kam ganin ba bari zatayi ba yasa yayi hanyar waje da sauri, baima lura ba yaji ya buge kai da bango, da azama ya fice waje.

"Ni zai nunawa duniyan ci kamar wace ya samu sa'ar sa" Annah ta fada Masifa sosai tahau yi, Salma kam kasa daina dariya tayi, da sauri tabi bayan sa waje, Mugun kallo Annah takai masu, tace da Hajiya ke kuma muje ciki ina da magana dake, haushi biu ne yakama hajiya ba yadda ta iya ta marawa Annah baya suka shiga daki.

Ajiyar Zuciya Junaina ta sauke ta kalli Jafar dake tsaye yana jin haushin fitar Salma, tace "yaya Alhakina ya kaima ya Mujahid, dazu bakaga dukan da yayi min ba
Da mamaki ya kalle ta, "duka kuma, mi kikayi ?
"Daga daukar wayarsa, wai bincike zan mar, yahau ni da zagi da duka"
Dariya zancenta yabashi, yace "yayi maganin ki kenan ?
Turo baki tayi "aini yanxu ba ruwana dashi, he is so mean".
Murmushi yayi, Baice komai ba ya wuce ya haura sama, turo baki tayi ta tahau gungunin baice mata sannu ba.

Haraban Gidan Salma ta fito waigen inda Mujahid yake, daga can nesa ta ganshi gurin parking motaci zaune kan boot din motarsa, kansa daure bisa cinyar sa.
Karasawa tayi gurin tana mamakin miyake yi gurin. Yana jin tsayuwar ta gurin yaki d'ago wa, hannu tasa ta d'ago da fuskar sa tana fadin "yaya badai dukan nan yasaka kuka ba" cike da zolaya tayi maganar, saidai ganin shatin dukan da yadda fuskarsa ta kumbura yasata ta shan jinin jikinta.
Hawaye taga ya fara gangarowa bisa kunci sa, yace "hankalin ki ya kwanta koh tunda kinga karshe na?
Cike da kidima da tsoro take kallan sa, gabanta sai faduwa yake..
Murmushin takaici yayi yace
"Am sorry nasan nayi hurting dinki, plz forgive me".
Tausayin sane ya kamata saidai bazata bari ya raina mata wayo ba, tace "miyasa sai yanzu zaka nemi afuwata ?
Ahankali ya zamo daga kan motar, suna fuskan tar juna, cikin sanyi murya yace "Salma i love you alot, dou nasan ba lailai ne ki yadda ba but tun ranar dana fara ganinki nakasa samin nutsuwa, kawai karfin hali da ego irin nawa yasa ban taba fahimtar hakan ba sai yau"
Kur Salma tayi mai da idanu, danson tantance gaskiar maganar sa ko kadan bata yadda dashi ba, saidai taji dadi i love you daya ce mata, kalamar data jima take son ji garesa, koda ace karya yake itadai taji dadi.

Dariyar rainin wayo ta saki sannan kuma ta daure fuska tace "do you tink am stupid, if i could recall, kwanakin baya haka kazo kace you liked me, ka bukaci friendship dina nikuma i was dumb nayi accepting, at last miya biyo baya, you wanted killing me, tnkx to Allah nayi surviving but still saida kaso ka kaini prison, gayamin wannan so ne ko kiyyaya or is it part of your egotistical behaviour ?
Hannuta ya riko, yace "nasan baza ki yadda ba, kin tsane ni, but plz find a place in your heart ki yafemin"
Dogon Tsaki Salma taja.
"You're not serious" ta fada hade da kawar da kanta gefen, sam ta kasa fahimtar inda ya dosa.
Gani tayi yayi kneeling down, da sauri ta kalle shi hade da ware idano.
Black shade din fuskar sa yacire yace " ciwon ido zai zama ajalina, i dont tink zan iya kaiwa jibi da irin azabar da nakeji, bazaki bani tym ko kadan ba ?
Tsoro da firgice ne suka kamata ganin yadda idonsa yayi jajir suna zubo ruwa, runtse ido yayi da sauri dan bazai iya barin su bude ba.
Tsugunna wa tayi gabansa,
Cikin rawar Murya tace "yaya miyasa me ka haka?
Kuka ya fashe dashi "i dont know, mayb kuma shower gel dina yayi expire nikuma nayi using yayi affecting dina, koma. dai miye ne ya illatani dayawa coz i cnt see clearly".
Na shiga uku na kasheshi, Salma ta fada aranta, sai yanxu tagane dalilin buguwarsa a bango daxu. Kaman zatayi kuka tace "plz yaya tashi muje asibiti, i cnt see you liked this"
Kai ya girgiza.
"karki damu nariga nayi using wani magani na, kuma banaso Hajiya tasan ina cikin matsala zata iya shiga tashin hankali"
Hannuta ya riko gabaya, "just tell me kin yafemin ko zanji dadi araina"
Sosai yabata Tausayi, wani irin haushin kanta take ji da muguntar da tamai, tace "yaya na yafe maka dukdai ban rikeka araina ba, but plz kadaina cewa xaka mutu, you cnt leave me"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya zauna akasa had'e da zaunar da ita yace "kinga no secret between us, nafada mike zuciyata, do you have something to confess ?.
Shuru tayi, gabanta na faduwa, tanason gayamai itace silan komai tana tsoro.
Ji tayi yace taimaka min mu shiga ciki, kinsan yanxu na zama makaho.
Mikewa tayi jiki sanyaye suka fara takawa ciki, sun kusa shiga Palo Salma ta tsaya tace "yaya karsu Hajiya su ganmu tare, miza muce masu ?
Yace "hakane ga wayata ki kira Faiza tazo, tunda na makance bakya so aganmu tare, nasan ita komin rintsi she wil stand by me"
Cire wayar yayi aljihu ya mike mata, kin karba tayi tace "wasa nake fah"
Aranta kuwa tace "wana hauka ya kaini kirama wannan bazawarar"
Ciki suka shiga suka ci saa ba kowa a palon sai junai da hankalinta gabadaya yana kan Tv, ahankali ta taimaka mai suka haura sama.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.