Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 41

Suna Gama 2 to 4 lecture Salma ta dawo gida, hankalinta kwance bata da damuwa, tana son ganin yadda fuskar Mujahid zata kasance saida ta rasa ya zatayi, "kila ma jiya yayi kuka" ta fada aranta, dariya tayi. Ta fiddo wayarta kiran Salim dan jin ya yagansa da safe a office, tana bugawa salim ya dauka, hayaniya sosai taji tahau tambayan yana ina, yace yana Sheraton an gayyace su wani programme nayan skull dinsu,"
Tace "harda ogan ka kenan"
Shuru yayi yasan wa take nufi, tace ka fito waje nanda 30 minti gani nan"
Katse wayan tayi.

Da gudu ta shiga gida, agurguce tagaida mom ta fada toilet, wanka tai ta fito ta shirya cikin wata short Golden Gown mai adon crystal stone, hannu shi dogo ne, sai kuma red 6 inches shoes data sanyawa karfa ta, dama ba wata doguwa bace sosai, hill din yayi dagwas da ita, gashin kanta ta tamke waje daya sanan ta dauko weavon cap mai kananun kitso ta sanya kanta hade da tufkewa one side, kwalliya tayi ta kyace raini, sannan tadau wayoyinta da clutch purse red ta lallaba a guje ta fice, motarta ta shiga taja at 360 zuwa Sheraton.

Babbab hall ne mai shegen kyau, kowa zaune a round table mai dauke da sit din mutum biyu. Wani law student ke bayani anai mai tafi.

Mikewa Mujahid yayi, faiza tayi saurin zaunar dashi "Mjay kayi hakuri, ankusa gamawa, wai miya faru ne naga duk ranka abace"
Kwafa yayi ya koma ya zauna ba tare dayace uffan ba, Salim nagani ya mike yayi waje (ni xarah nace oga ta iso).

Gyaran Muryan Mc yayi yace "muna son volunteers na face of Gwagwalada na 2017, ina kyawawan suke" duk yan gurin dariya sukayi, saboda yadda ya fadi cikin salon shakiyan ji.
Yacigaba "harkar nan fah no student no lecture, mutane da dama nema suke basu samu ba"
Dariya yan gurin suka karayi, Mujahid kam ya kosa ya bar gurin, Faiza kam so take ta tashi as volunteer amma tana jin kunya, tasan dai tana da kyau gata fara, muddin ta zama face of gwagwalada ba karamin respect zata samu ba.
Kaman an tsikarate ta mike tsaye, kallon Ta MC yayi yace "Are you in".
Ba kunya tace yes" ihu da tafi aka fara, dan kam tana da kyau ba karya..Mujahid kam inda akwai bindiga kusa ba abunda xai hana ya harbe ta dan haushi.
Takawa Stage din Faiza tayi, cikin jin dadin yadda aketa hailing dinta, MC yafara fasa mata kai da zuzuta kyan ta, can yace "she is damm beautiful, akwai wanda ke opposing beauty dinta?
"No" hall din ya dauka, Faiza kam she just dey feel her self.
Daga hanyar shigowa sukaji muryar Salma tace "i appose"
Mamaki kowa yayi, kallo ya koma kanta, wasu sun santa a skull wasu kuma yau suka fara ganinta, Takawa Salma tayi kan Stage din cikin yauki da kwarkwasa, Mujahid Kallon ta yayi yana rokon Allah kar zuciyarsa ta buga dan haushi dressing din da tayi, wani mugun tsanan tane ya sokesa a ziciya

MC yace "miyasa kikace haka yammata...
Harara takai mai tace "saboda na fita kyau, black is beauty...
Ihu yan Hall suka kwashe dashi, wata igbo gal dake zaune ta mike tahau stage wai bata yadda ba, itama tana da kyau ai, MC kam yaga ikon Allah, 3 people fighting for one thing, dabarace ta fado mai.
Yace "Ba karya duk kuna da kyau, but mutum daya akeso, saidai Ayi Bidding"
Faiza kam ji tayi kaman ta shake Salma, bata rai tayi tace ta siya 50k, Igbo gal dasan kudi ko sisi bata saba ta sauka da gudu, Salma tace tasa 150k, kwafa Faiza tayi yaukam saita kure yar iskan yarinyar nan, tace 200k, Salma tace 500k, shuru faiza tayi kaman tayi kuka, dan kudin ta da take maneji da rike gidansu baima kai 500k

Ihu kowa yayi Salma ta burge su, Salim kam mamaki yayi yasan Daddy na tsakarwa Salma kudi, amm 500k yayi yawa tayi wasting abanza, Mc kam baki har kunne sun samu kudin banxa, atake ta masu transfer din kudin, crown ya dauko zaisa mata tace "no need, d title is okay for me" juyawa tayi tanai wani sexy cat walking ta fita agurin, wani ihu hauka aka farayi, jiki sanyaye Faiza ta sauka, gurin Mujahid ta nufa tace tashi mu tafi"
Baiko kalle taba ya raba gefenta ya wuce, da gudu ya karasa haraban waje inda Salma ke tafiya, gabanta ya tsaya yana murmushi sannan yace "congrat"
Daure fuska tayi
"I dont need your congrats saboda nasan your heart is burning right now, so gwara ma kar kayi pretending"
Rab'awa tayi gefe ta wuce, ya kuma shiga gabanta, hararar sa tayi tace "am done with you nonsense, am begging you ka fita rayuwata, kamin laifi na rama, kuma na hakura, stay away from me" wucewa tayi gefen sa.

Murmushi yayi ya tsaya kallonta harta shige motan ta, aranshi yace "kin shigo rayuwata kuma no way out..."
[9/7, 12:37 AM] Xarah Bukar: Zuma Sai Da Wuta

~na~
©ҳaɾaɧ bųkaɾ
®NWA

31 - 33

Tsaye Faiza tayi tanai kallon shi, saida yaga motar Salma ta bar gurin sannan ya taka zuwa tasa mota, shiga yayi ya zauna yana cigaba da murmusawa, jiki sanyaye Faiza ta shiga yaja, sunyi nisa babu mai magana da wani, kowa da abunda yake sak'awa a zuciya.
Dakyar dai faiza ta samu courage din yimai magana, duban shi tayi fuskar sa fayau ba damuwa tace.
"Mjay badai ka fara folawa yarinyan nan ba?"
Kallon ta yayi yace
"I dont tink so, amma koda ace na fola mata ai it isn't a crime ko ?
Marairace murya tayi
"Kawai naga she isnt d right person for you, kuma ma you deserve more.."
Katse ta yayi da cewa, "tnx for your concern, i decide what i want and what i don't want"
Shuru tayi, ta shak'a ba kadan ba, sun danyi nisa yace "When are you ready to settle down
Aranta tace kai nake jira, afili tace "very soon, kasan komai lokaci ne kuma sai Allah yayi"
Daure fuska yayi Yace "kafin lokacin learn to respect youself bawai kina embarrassing kanki kamar yadda kikayi dazu ba, you ain't a kid any more"
Kallan takaici tamai, ita bataga wani bad abu datai ba dazai ce haka alhalin ita waccan data siyar da mutuncin ta lallab'a ta yaje yayi.
Bata iya cewa komai ba har suka iso gidansu, sauka zatayi taji yace "yaushe kike da class ?
Abunka da cool headed person, murmushi tayi tace "jibi"
"Allah ya kaimu" ya fada yaja motar yayi gaba.

Salma na isa gida ta hadu da Mom, fada sosai tasha da irin dressing din datayi, haushi biu ne ya hade mata, daki ta shiga tacire kayan sannan ta zauna kan gado tunanin abunda ya faru tahau yi, ta jima zaune daga bisani ta mike, hoton sa dake gurin tadau ta wurga ciki karamin trash can dake dakin sannan ta koma ta zauna zuciyarta na zafi.

***
Yau kam jikin Junaina ya warware, bataje skull ba saboda intervel na kwana biyu da take dashi, duk babu dadi takeji barin Mujahid gidan, ganin su Hajiya ko ajikinsu yasa ta nuna ita ma bata damu ba, tana son kiran shi awaya amma tana tsoro, ganin take idan ta kuma mai magana yar Mafia zata iya cafko ta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.