Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 41
Hauka ne kadai yarage Mujahid baiba, kaman wani zaki ya hau huci a office din, yasan Salma is a bitch saidai bai taba tsammanin she can stoop so low tayi kidnapping Junaina ba much less tayi demanding makudan kudi haka ba, tsoronsa daya karta gano Gidansu tunda har ta iya sato Junaina, Allah kadai yasan a ina ta gano shi as yayan Junai.
Karar shigowan text msg na account no dinta ne ya katsemai tunani, da sauri yadau ipad dinsa ya shiga yi mata transfer din kudi, amma a zuciyan shi yayi alwashi karbo kudin sa dan kuwa bazai bari taci bulus ba.
Salma naji alert tasa Su Tk suka kunce Junai, dakyar ta iya takawa suka karasa mota ta shiga abun tausayi, kallon su Tk Salma tayi sannan ta zaro 20k ta basu tace "aikkn nan bashi da amfani ku kama sanaa koda wanki da guga ne".
Sukam godiya sukai sosai cike da murna, dama rashin nasha da ci ke sanya su yin wani abun.
Shiga motar Salma tayi taja, Junai na zaune tana sauke numfashi wahala, hawaye take zubarwa, kanta dauke gefe tanai kallon waje.
Kiran Mujahid tayi, da azama ya dauka tace "ka fito tsakiyar cikin gari" katse call din tayi, yakuma kira bata dauka ba, saida ta iso National stadium sannan tayi parking, ta turamai text din inda take, kallon Junai tayi tace "kina iya sauka"
Kaman jira take ta bude motar, zata sauka taji Salma tace "am sorry idan kinji haushi na"..
Da karfi Junai ta rufe kofar batare data tsaya sauraran taba, saidai kalmar idan kinji haushi da Salma tace ya mugun kara bata mata rai, "wana kare xaa ma cin kashi haka yak'i jin haushi, itama dai tasan abunda tayi can never be forgotten or forgive" azuci junai tayi maganar, can gefe ta zauna akasa jiran Mujahid.
Cikin rashin damuwa Salma taja motarta tayi gaba.
Baafi minti 20 ba Mujahid ya iso gurin hankali tashe, da sauri ya sauka ya riko ta suka shiga motan yaja, ba abunda bai tambayi Junai ba fir taki magana har suka iso gida, Nan suka iske Hajiya da Jaafar shima alokacin ya dawo aiki yaga hankalin hajiya tashe, fitowa neman junai zasuyi sukaga motar Mujahid ya shigo..
Kafin ya tsayar da motar Junaina ta bude kofar ta fito, da gudu ta karasa gurun jafar hade da fadawa cikin sa tanai kuka mai tsuma zuciya.
Tambayan miyasa meta jaafar yahau yi, bata iya bashi amsa ba sai kuka, yajata suka shiga ciki.
Mugun kallom Hajiya tama Mujahid dake tsaye bayan ya fito motar, kaman marar gaskia haka ya koma.
Fuskar hajiya ba annuri tace "ina ka kaita, mai kayi mata..".
Shuru yayi baice komai ba, tsoron sa daya kar Junaina tama hajiya Description din Salma, yasan Hajiya dason bin diddigi.
Wayar hannuta Hajiya ta danna hade da kiran Aunty Bilkisu, fitowan ta kenan daga NNPC clinic inda take aiki. Hajiya tace da ita ta biyo ta gida Junai ba lapia.
Hararan Mujahid tayi sannan ta kama hanyar komawa ciki.
Zaunar da ita Jafar yayi kan gadonta yanai kara tambayan ta, jikinta gaba daya rawa yake, cikin muryan tace "wata yar Mafia ce ta saceni, kuma da alamun tana da wani Dirty relationship da yaya kuma fah her face looks familair i just dont know ina na santa"
Riko hannuta yayi yana lallashinta yace "ko Faizan Umma ce.
Kada kai tayi "Aunty faiza is too naive, ba ita bace wannan fah so pretty gata black beauty saidai zuciyan ta ba imani, i was so scared, kiris yarage bata harbe ni da bindiga ba" duk cikin Kuka take maganar, fuskar ta gabadaya ta kumbure.
Hankali jaafar ne yatashi, yau kam sai yayi confronting yayan shi, Hajiya ce ta shigo, ba tambayar da batai ma Junaina ba, taki gaya mata komai, sai cewa tayi b'ata tayi sunje gidan kawarta.
Aunty Bilki na karaso wa ta duba Junai hade da bata pain relief, sai sannan hankalin Hajiya ya kwanta atunanin ta ko wani abu mugun abu Mujahid, dakyar Junai ta iya tashi tayi wanka tayi alwala sannan ta fito tahau jera salloli.
Rai bace Jaafar ya haura sama, dakin Mujahid ya fada ba tare da Sallama ba, tsakiya dakin ya iske shi zaune akasa kan center carpet, hannusa rike da Sigari yana busa, daga ninsa cikin tsananin baccin rai yake.
Yana ganin Jaafar ya dauke kai,
Kansa jaafar ya karaso ya tsaye yace "wace yarinya ce keda guts din kidnapping junaina sannan kai kuma as a policeman you aint doing anything about it ?
Banza dashi Mujahid yayi, dan kuwa ayadda ranshi ke zafi sai iya haushi da duka.
Kafadar sa Jaafar ya riko yace " stand like a man and talk to me, ko nima tsoro na kakeji kaman yadda tsoron yar mafia ya hanaka arresting dinta..".
Azabure Mujahid ya mike yana huci, iya karfin sa yasa ya ture Jaafar wanda saida ya bugu da D mirror dake gurin, glass din ya face, da gudu Hajiya da Aunty b suka hauro sama.
Mugun naushi Mujahid ya kaimai a fuska, nan suka cakwade suka fara dambe, akideme su Hajiya suka fado dakin, Salati ta saki tahau kokarin rabasu, jaafar ta janye gefe wanda tuni bakinsa yafara zub da jini, fadi yake "matsoracin kawai, ai fitowa xakayi ka fadi abunda ya faru bawai kayi shuru"
Rufe mai baki Hajiya tayi tana jaafar yi shuru ya isa, mujahid kuwa huci kadai yake, ganin yadda attention din Hajiya da aunty b na gurin Jaafar yasa shi fara harhada kayan shi cikin akwati, atsorace Aunty B ta kalle shi Mujahid miye haka, ina zaka.
Baibi takan taba ya hade kayansa a kwati yaja ya raba gefen su ya wuce, Janyo Aunty B hajiya tayi tace "kyaleshi ya gama fushi, muje ki taimaka wa Jaafar" ba musu Aunty B ta riko jaafar suka sauka kasa, kallon dakin Hajiya tayi taga sigari dake baje agun, kai ta girgiza tace "Allah ya shirya min kai Mujahid"
Afusace Mujahid ya fada mota yaja, bai zarce ko ina ba sai Louis House nan inda gidajan mayan yan sanda Nigeria suke, babban Flat dinsa ya nufa, security dake gurin ya bude mai gate din gidan, hadaddan gida ne mai dauke da 3bd, 2palo ds kitch sai haraban gida da garden ta baya, ko dauka akkwati bai ba ya shiga gidan, ciki ma ya hadu ba karya..
Dirshan yayi kan kujera ya dafe kai kaman yayi kuka, shi kadai yasan abunda ke yawan mai azuciya.
Da nishadi Salma ta karasa gida, dakinta ta fada ta kwanta abunta kasancewar hutun sallah take, so take kadai taga Fuskan Mujahid, hotonsa ta dauka tana kalla hade da sakin lausassiyar murmushi.
"***
Washe gari kam Junai da zazzabi ta tashi, Neco sukiyi kuma aranar zasuyi Math, dole ta hakura ta zauna a gida ranta duk abace wani mugun tsanan Salma take ji aranta.
Mujahid baiyi niyyan fita ba tsananin yadda zuciyarcsa ke tafarfasa, haka ya daure ya fita dan zuwa wani programme da yan Gwagwalada University suka hada mai suna Nigeria law & constitution da zaayi a Sheraton Hotel, kwata kwata bashi da raayin zuwa, koda suka turo mai Gayyata bai amsa ba ya zabi wasu a office su wakilteshi, Faiza ce data kira shi awaya ta nace saiya je dan itama zataje, kasancewar lectures da dama zasu da kuma yan aji biyar masu karanta Law. Gidansu yaje ya dauke ta by 5pm sannan suka wuce gurin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.