Complete Hausa Novels

Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Zuma Saida Wuta Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 24 of 41

Parking Jafar yayi a haraban asibitin bacin ya gano dakyar nan gurin ambulance din ya kawo Salma, duba girman asibitin yahau yi yana tunanin ta inda zai fara bi, juyawa yayi ya hangi Mujahid tafe daga can nesa dashi, da azama ya nufesa, Mujahid na ganinsa yakara shan kara shan mur.
Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya tsaya gabansa cike da tashin hankali yace "thanks Goodness you're here, kasan cewa Ummi ce yarinyar daka aika mutanan ka har gida dauko ta ?"
Cikin rashin nuna damuwa Mujahid yamai kallon banxmza yace "is dat y you're freaking out ?
Kallon rashin fahimta Jafar yamai yace "kana sane kenan ?
Tsaki Mujahid yaja, baice komai ba yayi gaba abunshi, mamaki ne ya kama jafar, ba tantama Mujahid yasan Ummi ce saidai bai san dalilin dayasa yake kokarin hunting dinta down ba, koma miye zaiso sani daga bakin Ummi, duk azuci yake magana Hanyar daya hangi yan sadan tsaye ya tabbatar nan Ummi take.
Karasawa gurin yayi suka ki bari ya shiga, haka ya hakura komawa gida saboda dare yayi.

General clinic inda aka mik'a gawar Baba nayaro nan Mujahid yanufa, police dayabar incharge din dauko gawar ya iske tare da wasu mutane zaune suna Kuka.
Yace "suwaye wannan ?
Police din yace "family din deceased dinne nayi contacting, kai suke jira tun dazu"
Kafin yayi magana daya daga masu kuka yace "dan Allah ka taimaka ka bamu Babanmu, mu mikashi gidan gaskia, bamu damu dasai an dauki mataki ga wanda ya kashe shi ba, wlh mun yafe" kuka sosai saurayin yake, daga gani ba masu hannu da shuni bane.
Tausayin su Mujahid yayi, yace yana zuwa, so yake ya amshi evidence mai karfi dazaiyi preventing Salma zuwa prison. Idan har ya karba ya boye sai randa yaga dama zai fito dashi ya ceceta.
Gurin Doctor ya shiga suka gaisa sannan yace.
"Ka gama autopsy (dissection da akeyi dan gano possible cause of sum1s death)
Doctor yace " komai anyi, zuwa gobe result will be ready.
Kwantar da Murya Mujahid yayi yace "make sure karka nunawa kowa, zan zo dakaina na karba"
Doctor bai kawo komai aranshi ba ya amsa bai da toh, fitowa mujahid yayi ya fadima mutanan cewa zasu iya tafiya da gawan, sukam kuka kawai suke.

Hankali tashe Daddy ya dawo Gidan, nan Mom ta labarta mai abunda ke faru, kuka sosai take babu labarin Salma, ran Daddy sosai yabaci ya kira Salim awaya, kaman wani majinyaci ya fado palon, duk ya fita hayyanci tsabar gulity conscious dake damu shi.
Cikin tsawa Daddy yace
" dan uwarka ina ka kaimin Salma?
Tsuru Salim yayi ji yake kaman asirin shi zai tono, yace "wlh Daddy nima neman ta nake.
"Karya kake, duk wani rashin jin Salma tare kuke yi ka dauka ban sani ba, dan haka gayamin gaskia awana dalilin ake tuhumarta da kisan mutum ?
Shuru Salim yayi baice koma ba, Daddy ya cigaba "asararrar banza tashi ka bani waje, kuma ka binciko min duk inda Salma take".
Jiki ba kwari ya mike ya fice.
Mom tace "wayarta na ringing baa dauka"
Bara na gwada atawa, Daddy ya fada hade da dailling no dinta.

Jafar na Isa gidan yayi parking, fitowa zaiyi yaji ringing din waya, dubawa yayi ya hango Pink Jakar Salma, dauka yayi ya bude yaci karo da frame mai dauke da Hoton Mujahid, kallon hoton yayi cike da mamaki, nanya tabbatar sunsa Juna, "toh make faruwa ? Ya tambayi kansa, wayarsa ya duba yaga miss call Mom hamsin saina Dad guda biyar, ajiye jakar yayi cikin motar sannan ya karasa gidan rike da wayan, dakin Hajiya ya shiga ya iske ta zaune tayi tagumi, fada mata yayi yadda sukayi da Mujahid hade da nuna mata wayan ummi da iyayanta kerlta kira, ranta sosai ya kara baci da kuma tsoro daya kamata da ganin Dad naciga da kiran Salma. Kallon namban jafar yayi kaman yaso yagane nambar, wayarsa ya danna yayi compare din nambar Dad dake kira, gabansa ne ya fadi, ya kalli Hajiya yace nasan Gidan da Ummi take, tace ai zuwa zamuyi bamuga ta zama ba, tashi tayi da sauri ta zuri hijab sukai waje.

Hankali tashe Daddy ya kira no din abokinsa head of police gabadaya, sun jima suna magana daga karshe ya yanke gobe zaiso office suyi magana.
Baa fi mintin uku ba maigadi ya kwankwaso wai sunyi baki, izini yamai dasu shigo, Su Hajiya na shiga Daddy yaga Jafar, Hajiya kam kallon Mom take wanda tasha kuka harta gaji.
Zama sukayi aka gaisa, Daddy yace "jaafar yanxu nake shirin kiran ka awaya"
Ajiya zuciya ya sauke ya mikawa Daddy wayan Salma, karba yayi, ya labarta masu haduwa su da Salma da kuma yanxu asibitin da take. Salati Mom tahau yi hade da fashewa da sabon kuka, Hajiya kam binta kawai tayi da ido, Daddy yace "amma officer in charge of this case sai yaci uwarsa, saiya fadamin yaushe yaga yata ta kashe wani dahar zaiyi babak'eran aresting one n only daughter na"
Katse shi Mom tayi da cewa, "Alhaji tashi zakayi muje mu dibo yarta."..
Jaafar yace "baa bari, saidai gobe.."
Sai sannan Mom ta dubi Hajiya dakyau sun danyi yanayi da Salma, sharewa tayi tace "mungode sosai da temakon yarmu da kukayi, Allah ya saka da alheri"
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "nice da gode maku, Allah kadai yasan dami xai saka maku"
Kallon rashin fahimta Mom tayi mata, hajiya taci gaba "basan ya akayi Salma ta dawo hannunku ba, saidai kun cancanci riketa yadda naga duk kun damu" k'walla hajiya ta share tacigaba "ni yayar mahaifiya salma ce, na jima ina neman ta banganta ba"
Ware ido Mom tayi, shikam Dad baiyi mamaki ba, koda ya hadu da Salma daman neman yan'uwanta taxoyi a garin Abuja, ganinta karama lokacin yasanya ya kawo ta gida yarike ta tamkar yar cikinsa, saidai yaji dadi ganin Jaafar amatsayin d'an Hajiya, hada aura salam da Jafar yazo asauki kenan.
Kuka Mom take sosai tana rokan Hajiya karta rabata da Salma, Hajiyan ma kuka take tace "karki damu Salma takuce halak malak bazan rabaku da ita ba"
Dddy yace "ikon Allah kenan, jaafar Allah yayi bazaku hadu da Salma ba tun shekarun baya dana ma zancen auran diyata, ashe kai dan'uwan ta nema, faduwa yazo daidai da zama".
Sosa keya jaafar yayi hade dayin murnushi..
Hajiya kam jikinta ne yayi sanyi jin Daddy zai ruguza mata plans, saidai ba yadda ta iya tunda shiya rike Salma, bata isa tace Mujahid ta kamawa Salma ba, balle yadda taga Daddy yadau zafi da officer dake kokarin aika salma gidan yari....
Sun dan jima suna magana, daga bisani su Hajiya suka bar gidan bayan sunyi zasu hadu gobe a asibiti.

****
Washe gari bayan Mujahid yayi Sallar asubah asibitin ya nufa gurin Salma danso yake ta farka agaban idonsa.
Salma kam Baccinta take, wata nurse ta shigo dakin tacire roban jini sannan ta sa mata na ruwa, fita nurse din tayi, baiyi awa daya ba Salma ta fara motsi, ahankali ta bude, ganinta cikin farin daki yasata mikewa azabure, wani kara tasaki jin ta karce hannuta, duban gurin tayi taga haunta da karfen gadon makale da handcuff, kokarin cixgewa tayi ta kasa, "na shigu uku" ta fada bayan ta tuna abunda ya faru"
kuka ta soma yi, jin motsin xaa shigo yasata tsayar da kukan hade da kafawa kofar ido.
Mujahid ne ya shigo, jikinsa sanye da dagon jallabiya, tana ganinshi ta hade hade rai, tuna neman kasheta da yasoyi tayi.
Murmushi yayi mai dauke da ma'ana iri iri sanna ya karasa daf da ita ya tsaya, murya ciki ciki yace "ya jikin ki ?
Banxa tayi dashi
Yace "hope you're ready to spend 30 years a gidan yari"
Dogon Tsaki taja, tace"am ready, then after 30 years kuma i'll come back to destroy you for good".
Dariyan rainin hankali yayi yace "kina da guts dayawa" gashin kanta ya damko, saida tayi kara, daure fuska yayi yace "dan uwarki ni kike yiwa tsaki.."
Dukda ciwon da jikinta yake mai hanata kokarin cizge hannusa daka kanta ba, kaman mai shirin yi kuka tace "idan banyi tsaki ba mai kakeso nayi, apologise or beg your pardon kake so nayi, toh kasani, that will never happen, badai so kake ka kaini prison ba, bismillah, kuma point of correction uwarka badai uwata ba..."
Iya k'ulewa Mujahid ya kai, wuyanta ya damko da karfin gaske, yace " uwata kike zagi.."
Tace "uwa batafi uwa ba, idan kana nonsense dinka dont ever include my Mom."
Sakinta yayi yana Huci, juyawa yayi zai fita tace "am hungry, get me sumtin to eat".
Bai iya tanka taba ya fice zuciyarsa na zafi, baiso reaction din Salma haka ba, yaso ace kuka zatayi ta rokoshi amma dan karfin hali irin nata ba ita tayi kisan ba but she is willing to serve 30 year a prison... Tsaki yaja yana tunanin yadda zaisa a azabtar da ita a prison. Motar sa ya shiga ya koma gida dan shiryawa zuwa office.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.